*SAUYIN ZUCIYA.*
*Littafin kuɗi ne!**'Yar mutan zazzau Naanah M Shaaban*
*Whatsapp number https://wa.me/+2348122188717*
_FREE PAGE_
*_EPISODE 1-2_**#Ego*
Sauri sauri! gudu gudu yake tafiya duk irin saurin da yake yi kamar zai tashi sama amman gani yake sam baya saurin! bashi da wani buri a yanzu irin ya ga ya isa masarautar sarki Muhammad Bello, wacce take cikin garin Kano kasancewar ya ji labarin za'a debi 'yan aiki a masarautar yau da misalin ƙarfe 7:00am na safe shiyasa ya buga sammako ya fito yanzu ƙarfe 6:00am, Kyakkyawan ne ajin farko fari ne amman ba irin farin nan sosai ba, dogon hancinsa yayi dai-dai da ɗan ƙaramin bakinsa lebensa kuwa pink ne wanda turawa suke kiranshi da pink lips, manyan idanuwansa sun yi matuƙar dacewa da doguwar fuskarsa! gashin kanshi kuwa baki ne wulik ya kwanta a kansa sai sheƙi yake yi, ga sagensa ya kwanta luf a fuskarta sa! yadda kasan shi yayi kansa ya gama haɗuwa! indai ta ɓangaren kyau ne! wata koɗaɗɗiyar shadda ce a jikinsa wacce duk ta yayyage ta gama shan jiki! blue ce amman gaba ɗaya kalar shaddar ma ta koɗe ba za ka tab'a yin tunanin blue ba ce, takalmin ƙafarsa kuwa duk ya tsits-tsinke da leda ya saka ya kulle takalmin! Bassim kenan duk da kasancewarsa talaka bashi da cin yau bare na gobe amman yana da wadatar zuci.
Wajen ƙarfe 6:45am dai-dai ya isa masarautar tunda daman ba nisa sosai daga masarautar zuwa inda yake kwana, da yake masu gadin masarautar sun san yau za'a ɗibi sababbin 'yan aiki yana zuwa yayi musu bayanin ya zo neman aikin ne! suka barshi ya shiga, bai yi mamakin irin tarin mutanan da ya gani sun bi layi kusan mutane fiye da ashirin, ko bai tambaya ba ya san su ma aikin suka zo nema, dan haka shima ya bi layin, a haka mutane sukai ta zuwa suna bin layi, har wajen ƙarfe 9 sannan aka rufe shiga masarautar domin umarnin mai martaba ne, idan tara tayi a rufe ɗaukar mutane.
Suna nan tsaye Amman Mai martaba bai fito ba, k'arfe biyu tayi akai kiran sallar Azahar, ruwa aka basu suka yi alwala, sannan aka umarce su da su shiga cikin masallacin masarautar dan suyi sallah, suna idar da sallar suka dawo gurin da suke suka tsats-tsaya, har akai sallar la'asar babu sarki Kuma Babu alamar fitowarsa haka wasu daga cikin masu neman aikin sukai ta tafiya domin kuwa ba za su iya jiran gawar shanu ba, Amman Bassim bai tafi ba domin ko ya tafi bashi da gurin zuwa shiyasa ya gwammace gwanda ya zauna idan Allah ya taimaka mishi sai a ɗaukeshi a aiki, duk yawan da suke dashi Amman kwata-kwata su goma ne basu tafi ba, suka tsaya.
*GIMBIYA AFSHEEN POV.*
Tsaye take a gaban madubi tana k'arewa kanta kallo a jikin mudubi, sanye take cikin wata tsadaddiyar atamfa ta dora alkebba irin ta sarauta akan atamfar, kyakkyawa ce ajin farko ta gama haɗuwa ta ko ina, tsayawa inyi muku bayanin irin yadda take b'ata Baki ne, domin duk kwatancen mai iya kwatance ba zai iya yin bayanin irin yadda gimbiyar nan take ba, izza,mulki,kuɗi ga kuma uwa uba tsantsar kyau da take dashi, Gimbiya Afshin kenan.Jakadiya ce ta shigo ta tsugunna har k'asa tana cewa "Allah ya ƙarawa Gimbiya Lafiya, masu neman aiki, sun zo tun da safe har wasu sun fara tafiya, kuma Mai martaba ya ce ke zaki d'aukesu aiki" Wani irin murmushi tayi Wanda yake kunshe da tsantsar izza ta ce "Wato su da za'a taimakawa, su ne kuma saboda gajen haƙuri zasu fara tafiya, to ai shikenan, ki je ki cewa sauran da sukai yi ragowa lokacin hutawata yayi su tafi gobe sai su dawo, idan Kuma sun ga ba za su iya dawowa ba, babu Wanda aka yi wa dole" Tayi maganar tana mai zama a kan wata kujerar alfarma wacce duk an zagayeta da wani abin ado na gwal.
Jakadiya ta ƙara sunkuyawa kamar zata yi mata sujjada ta ce "To shikenan ranki ya dad'e na barki lafiya" Tayi maganar tana mik'ewa ta fita daga turakar Gimbiya Afshin! Kai tsaye gurin da su Bassim suke tsaye ta nufa ta fad'a musu sak'on da Gimbiya Afshin d'in ta ce ta fad'a musu.
Ransu ya ɓaci matuƙa haka suka fita daga masarautar kowa ya kama hanyar gabanshi, Bassim zama yayi a wani dakali da ke nesa da masarautar! Amman daga gurin da yake ana iya hango gate ɗin masarautar, wata iriyar azababbiyar yunwa yake ji kamar zata kasheshi rabonsa da ya ci abinci tun jiya da rana da Larai mai abinci ta basa shima ba wani mai yawa ba ne! a zuciyarsa ya shiga tunanin, wa zai taimaka masa ya basa ko da kwanzo ne ya ci? A haka dai ya tashi da kyar jiri na ɗibansa ya fara tafiya yayi nisa sosai dan ya kusan isa rumfar Larai mai abinci, ji yayi ana kiran sunansa da ƙarfi "Bassim! Bassim!! Bassim!!!" Da sauri ya juya duk da yadda ya ke ganin mutane dishi-dishi hakan bai sa ya kasa gane waye yake kiransa ba! Khalil ne yana d'inki shagonsa yana kusa da rumfar Larai mai abinci.
YOU ARE READING
SAUYIN ZUCIYA.
Romanceta tsaneshi sosai duk da yadda yake bawanta, amman alƙalamin ƙaddararta yasa ya auri ƴar uwarta.