*SAUYIN ZUCIYA.*
*LITTAFIN KUƊI NE.**ƳAR MUTAN ZAZZAU NAANAH M SHA'ABAN✍🏽*
_FREE PAGE_
*EPISODE 5-6**Whatsapp number https://wa.me/+2348122188717*
*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽
*500MB* 200
*1GB* 300
*2GB* 600
*3GB* 900
*6GB* 1800
(CHECKING BALANCE * 461*4# )
VALIDITY : 1 MONTH
For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*
*#Compassion & Painful*
Ifteehal zama tayi a tsakiyar tafkeken falon tana kuka tare da kiran sunan Bassim, wata kyakkyawar budurwa ce ta fito daga wani ɗaki, fara ce sosai kamar su ɗaya da Gimbiya Afsheen zata iya yin shekara goma sha tara zuwa ashirin, kanta babu ɗankwali gashin kanta duk ta hargitsashi ya sauka a gadon bayanta, tana tafe tana dariya tare da cisgar gashin kannata, tsayawa tayi turus ganin yarinya a falonta tana kuka, da sauri ta ƙarasa gurinta ta zauna tana dariya tace "yarinya" sai kuma ta tuntsire da wata iriyar mahaukaciyar dariya, Ifteehal tace "Dariya kike yi min ko?" Gimbiya Abeela tace "dariya kike min ko" sai ta ƙara fashewa da dariya, Ifteehal tace "meyasa kike dariya, ni ina so naje gurin Yayana ki kai ni kinji auntyna" Gimbiya Abeela ta ƙara fashe da dariya tare da maimaita abin da Ifteehal ɗin tace "meyasa kike dariya ni ina so naje gurin Yayana ki kai ni kinji auntyna" wannan karan Ifteehal ita ma dariya tayi tace "Auntyna kina bani dariya sosai, kin san menene yayana yana yawan ce min idan mutum yana cikin farin ciki ya kamata ya dinga samun wanda zai dinga sakashi nishaɗi, na ji daɗi sosai dan kin sakani nishaɗi auntyna ina sonki sosai" Ifteehal tayi maganar tare da rumgume Gimbiya Abeela, murmushi kawai Gimbiya Abeela takeyi haka kawai ta ji yarinyar ta kwanta mata a rai, kamar an tsikareta ta ɗago Ifteehal tana dariya tace "zo muyi wasan ƴar ɓuya" Iftehal tace "to Auntyna kin ga ɗankwalina sai na rufe miki fuska, idan kin kama sai nima nayi" Ifteehal tayi maganar tare da rufewa Gimbiya Abeela idanuwanta da ɗankwalinta, Gimbiya Abeela tace "ki daina ce min wannan sunan, wannan mutumin yace sunana A...Ab..Abee..." Sai kuma ta dafe goshinta tace "na manta meyace min" Ifteehal tace "kin manta sunanki kenan??Ko ke baki da suna??" Gimbiya Abeela ta taɓe fuska tace "eh ban da suna" Ifteehal tace "to na saka miki sunan ƙawata ta gidan Mama mai raino" Gimbiya Abeela da sauri ta gyaɗa kai tare da cewa "eh ina so" Ifteehal tace "to sunanki Basma daga yau" Gimbiya Abeela tace "Bas...Ba.. Ya ma sunan na manta" Ifteehal tace "Basma, zan dinga tuna miki idan kin manta" Gimbiya Abeela tayi murmushin jin daɗi tare da miƙewa tana tsalle idanuwanta a rufe tana cewa "yeeeee ina da suna yanzu" Ai ba ta yi aune ba santsin tiles ya kwasheta ta faɗi ƙasa kanta ya bugu da tiles ɗin falon kanta ya fashe, ta fasa wata iriyar jijitatciyar ƙara, jini ya fara zuba, a dai-dai lokacin Gimbiya Afsheen da Falmata suka shigo falon, da gudu Gimbiya Afsheen ta ƙarasa kusa da Gimbiya Abeela ta kunce mata ɗankwalin Ifteehal daga idonta, Ifteehal sai a lokacin ta tuna abin da yasa aka kawota turakar Gimbiya Abeela da sauri ta miƙe tana ƙoƙarin fara aikin gyaran turakar jikinta sai rawa yake yi, Gimbiya Afsheen ta ɗago tana yi wa Ifteehal wani irin wulaƙantatcen kallo mai tattare da tsantsar tsanarta, "Falmata janyo min yarinyar nan" Falmata ta maka hannun Ifteehal ta janyota kusa da Gimbiya Afsheen hankalinta a tashe dan bata san me za ta yi wa Ifteehal ɗin ba, cikin zafin nama Gimbiya Afsheen ta kama kan Ifteehal ta dinga bugashi a jikin wani glass har sai da glass ɗin ya fashe duk da irin yadda glass ɗin yake da ƙarfi, Ifteehal tuntana ihu har sai da ta daina motsi amman Gimbiya Afsheen bata kyaleta ba, Falmata ta fashe da wani irin azababben kuka na tausayin Ifteehal, Gimbiya Abeela ganin yadda Gimbiya Afsheen take buga kan Ifteehal a cikin fasassun glass, tayi saurin fisge Ifteehal ɗina tana cewa "ke ki bari ƙawata ce, zamuyi wasan ɓuya da ita me ruwanki da mu" Gimbiya Afsheen ta buɗe baki zatayi magana, Mamy ta shigo tare da Sultana Maimuna da Jakadiya suna bin bayanta, ta zo ne dan ta duba lafiyar Gimbiya Abeela, da sauri Mamy ta ƙaraso kusa da Ifteehal ganin kanta sai fitar da jini yake kuma ga fasassun kwalbaye a fuskartata wasu sun shige cikin tsokar fuskartata "meya faru da ita??wane mara imanin ne yay mata haka??" Mamy tayi maganar muryarta na rawa, Sultana Maimuna jikinta na rawa ta ɗauki Ifteehal ta ɗorata a jikinta hawaye na zuba daga cikin idanuwanta, Falmata ta kalla tace "meyafaru da ita Falmata" Gimbiya Afsheen cikin fushi, taƙama da kuma gadara tace "nice nan na hukuntata akan laifin da tayi kuma yanzu zan saka a kai ta ɗakin duhu dan sai na tabbatar jinin ƴar uwata bai tafi a banza ba, ba ku ga halin da Gimbiya Abeela take ciki ba ne, ta ɗaure mata fuska ta faɗi ta fasa kai amman ku gaba ɗaya hankalinku yana kan wannan ƙasƙantatciyar yarinyar mara galihu, kuma uwa uba na sakata ta gyara turakar nan, amman ba maimakon tayi abin da na sa ce tayi sai ta shiga shiryawa ƴar uwata mugunta irin nasu na ƴaƴan talakawa maƙasƙanta" Gimbiya Afsheen tayi maganar tare da miƙewa tsaye ranta gaba ɗaya a ɓace yake wani irin mugun haushin su Mamy take ji ganin sun damu da Ifteehal sai wani rawar jikin suke akanta, Gimbiya Abeela ta taɓa Mamy hawaye na zuba daga idonta tace "ƙawata bata tashi ba, nace mata ta zo muyi wasan ɓuya ta rufe min ido ta ba ni suna mai daɗi shine na tashi ina tsalle na faɗi ban sani ba, dan Allah ki tasheta ina sonta sosai ƙawata ce ita" Sultana Maimuna da ta gama sauraron abin da Gimbiya Abeela tace ta miƙe hannunta riƙe da Ifteehal idanuwanta akan Gimbiya Afsheen tana yi mata wani irin kallo "ban taɓa tunanin ke ɗin tabbatatciyar mahaukaciya ce ba sai yau! iliminki bai amfana miki komai ba, kwata-kwata baki da tausayi barantana imani, wannan ƙaramar yarinyar zakiyi wa irin wannan tsantsar rashin imanin kuma bayan haka ki ce zaki sakata a ɗakin duhu, to Gimbiya Afsheen ni Sultana Maimuna wallahi ba zan taɓa barinki ki ƙara taɓa koda ƴan yatsan yarinyar nan ba barantana kuma ki sakata a ɗakin duhu, karki ga kina yin duk abin da kike so ana kyaleki ki dinga ganin ana jin tsoronki kaf cikinmu babu mai jin tsoronki babu wallahi,dan ke ba komai bace idan ban da baiwar Ubangiji, ki gyara halinki kafin ki dawo daga ƙarshe ki fara yin nadama mara amfani" Tana gama faɗar haka ta huce dan ta kai Ifteehal ɗin asibiti, Mamy ta miƙe riƙe da hannun Gimbiya Abeela takaicin abin da ƴarta ta tayi wa Ifteehal ya sa ta kasa yin magana sai sauke wata ajiyar zuciya take mai bayyanar da tsantsar baƙin cikin da take ciki, bin bayan Sultana Maimuna tayi ba tare da ta kalli wajen da Gimbiya Afsheen take ba, Jakadiya na biye da ita a baya, Gimbiya Afsheen kuma ranta ya magana ɓaci da maganganun da Sultana Maimuna tayi mata "Tabbas wannan karan sai na saka Sultana Maimuna ta biya abin da tayi min karta ga ita ɗin ƴar uwata ce, ba'a taɓa ɓatawa Gimbiya Afsheen rai a zauna lafiya wallahi na rantse da girman Allah sai na hukunta Sultana Maimuna da hannuna" Tayi maganar tare da fita ta nufi turakarta, Falmata kuwa haushi da tsanar halayyar Gimbiya Afsheen ne suka mamaye zuciyarta, wannan karan kam ba za ta taɓa barin Gimbiya Afsheen ta hukunta Sultana Maimuna ba duk yadda za ta yi ta dakatar da ita za ta yi, dan ta san ko sarki ya ji cewar Gimbiya Afsheen za ta hukunta ƴar uwarta babu abun da zai yi akai dan yana tsananin son Gimbiya Afsheen ɗin kamar ransa duk da cewar yana da ƴaƴa, miƙewa tayi ta bi bayan uwar gijiyar ta ta jikinta duk a sanyaye tana tafe tana share hawayen fuskarta.
***** ***** *****
Bassim ne tsugunne a bakin kofar da aka shigar da Ifteehal dan a bata taimakon gaggawa, ita da Gimbiya Abeela, basu haɗu da Ifteehal da Gimbiya Abeela ba dan ana shiga dasu! shi kuma yana shigowa asibitin dan labarin da ya iskeshi na abin da Gimbiya Afsheen ta yi wa ƙanwarsa, kuka yake kamar ransa zai fita tare da dafe kansa, gaba ɗaya ya ji aiki a masarautar ya fita daga ransa tunda har ana neman a kashe masa ƙanwarsa "dan Allah Ifteehal karki mutu wallahi ina sonki ba zan ƙara yadda a turaki kiyi aiki ba, dan Allah na roƙeki karki mutu ki barni ki tsaya mu mutu tare" Sultana Maimuna ta kalleshi cike da jin tausayinsa tace "insha Allah Iftee ba za ta mutu ba, kayi haƙuri ka daina kukan nan dan bashi da amfani" Mamy da tausayin Bassim ya gama kamata daƙyar ta iya buɗe baki dan tun da suka zo bata iya cewa komai ba, sai kukan zuci takeyi "kayi haƙuri, dole a baka haƙuri dan nasan an cutar da ƙanwarka sosai kuma"..... Fitowar Doctor Abiddin ne yasa Mamy yin shuru, Bassim da sauri ya miƙe tare da cewa "likita ya Ifteehal take bata mutu ba dai ko, dan Allah karka ce min ta mutu dan wallahi ba zan iya jure rashinta a tare da ni ba" Doctor Abddin ya goge hawayen da yake ƙoƙarin fara zubo masa saboda yasan abin da zai faɗa dole ya gigita Bassim, Sultana Maimuna da kuma Sarauniya Mamy, "Bayan irin taimakon gaggawar da muka basu Gimbiya Abeela mun samu mun tsayar da jinin da yake zuba daga kanta anyi mata allurar bacci dan ta samu nutsuwa sosai sai nan da awa ɗaya zata farka" Mamy tace "Alhamdulillah ita kuma Ifteehal fa, da fatan babu abin da ya sameta?" Doctor Abiddin yay shiru yana tunanin ta ina zai fara faɗa musu Ifteehal ta mutu, Bassim ganin Doctor Abiddin yayi shuru yasa jikinsa duk yay sanyi, wasu zafafan hawaye ne ya fara zuba daga cikin idanuwansa zuwa kan kuncinsa cikin rawar murya yace "Likita naji ka yi shuru, Ifteehal ta mutu ne?" Yay maganar zuciyarsa kamar zata tarwatse, Doctor Abiddin ya kalli Bassim tare da dafasa yana cewa "Ka kwantar da hankalinka ɗan uwa, karka manta fa da rayuwa da mutu duka a hannun ubangijinmu suke, kuma idan har ubangijinmu ya kira bawa to dole sai ya amsa kiransa, Ifteehal a halin yanzu addu'armu kawai take buƙata ba kuka da tashin hankali ba" Mamy jin abin da Doctor Abiddin yake faɗa tace "Doctor ka faɗa mana Ifteehal ta mutu ne?" Doctor Abiddin ya gyaɗa kai alamar eh tare da cewa "eh sarauniya munyi iya bakin ƙoƙarinmu dan mu ceto rayuwarta, amman sakamakon yadda kanta yay mummunan bugawa tare da fasassun kwalbayen da suka shige cikin fuskarta yasa"........ Ai yadda Bassim yay kukan kura ya riƙe wuyan rigar Doctor Abiddin ne yasa yay shuru bai iya ƙarasa maganar da yake son faɗa ba "meyasa ka bari ƙanwata ta mutu, ba ka san ita kaɗai ce dani ba, ita kaɗai nake kalla naji daɗi a zuciyata amman gashi yau kun haɗu kun kashe min ita, kun kasheta" Yay maganar tare da zubewa a ƙasa tare da fashewa da wani irin kuka mai cin rai.*WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE, MATAKI UKI NE GASU NAN ZAN JEROSU A ƘASA*
*NORMAL GROUP #300*
*VIP #600*
*SPECIAL GROUP #1K**KU TURO KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER ƊIN 0017770369 UNITY BANK, AISHA YUSUF MUHAMMAD, SAI KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08122188717.*
*SHARE IT FISABILILLAH👏🏼*
YOU ARE READING
SAUYIN ZUCIYA.
Romanceta tsaneshi sosai duk da yadda yake bawanta, amman alƙalamin ƙaddararta yasa ya auri ƴar uwarta.