7-8

14 0 0
                                    

*SAUYIN ZUCIYA*
*Littafin kuɗi ne*

*Ƴar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏽*

_FREE PAGE_
*EPISODE 7-8*

*Whatsapp number https://wa.me/+2348122188717*

*#Angry & Tears*

Mamy cikin sanyin jiki ta samu guri ta zauna a ƙasa, Sultana Maimuna ta tsugunna kusa da Bassim hawaye na zuba daga cikin idanuwanta, cikin shsh-sheƙar kuka tace "kayi haƙuri Bassim, dan Allah kayi haƙuri ni ban san da wane irin kalmomi zan yi amfani dasu wajen baki haƙuri ba, na san Gimbiya Afsheen bata kyauta ba, bata kyauta ba sam ita ɗin tana da wasu irin halayya na wulaƙanci, girman kai, iko, taƙama, izza tana ganin cewar komai tayi dai-dai ne, amman"..... Da sauri Bassim ya ɗaga mata hannu cikin fushi ya fara magana muryarta na sarƙewa "Ya isa! ya isheni haka, ba na so ki ƙara ba ni haƙuri saboda ina jin wani irin zafi a cikin zuciyata, ƴar uwarki ta kashe min ƙanwata baku iya yin komai a kai ba, saboda baku ɗauki talaka a bakin komai ba, saboda Gimbiya Abeela ta faɗi ta fasa kai, shin ita Abeela mahaukaciya ce da zata bari ƴar ƙaramar yarinya ta faɗar da ita, ina da tabbacin haɗa baki sukayi dan su kashe min ƙanwata, kuma har abada ba zan taɓa yafe musu ba, sai sunyi mummunan ƙarshe" Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da wani irin wahalallen kuka, Sultana Maimuna jin Bassim yana ƙoƙarin ganin laifin Gimbiya Abeela bayan ita bata ma cikin hayyacinta tace "karka ga laifin Gimbiya Abeela da mu, dan mu ba mu san Gimbiya Afsheen tayi wa Ifteehal haka ba, zuwa mukayi dan mu duba lafiyar Gimbiya Abeela muka tarar da abin da ya faru, ita kuma Gimbiya Abeel"......Bassim ya ɗagawa Sultana Maimuna hannu tare da cewa "karki yi ƙoƙarin kareta, dan hat da saka hannunta a kashe ƴar uwata na tsanesu fiye da komai a duniyar nan" Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya shige ɗakin da Ifteehal take zuciyarsa kamar zata buga, Doctor Abiddin da yake tsaye tausayin Bassim ya hanashi iya cewa komai yace "Allah sarki Bassim baka san cewar Gimbiya Abeela bata cikin hayyacinta ba ne shiyasa kace haka, kuma ko da Gimbiya Abeela tana cikin hayyacinta wallahi ba za ta taɓa yarda a yi wa Ifteehal irin wannan kisan gillan ba" Sultana Maimuna tace "tabbas Bassim bai san Gimbiya Abeela ta rasa tunaninta ba, bata ma iya tuna komai hatta sunanta bata iya tuna shi, mu da muke ƴan uwanta kallon wasu bare take yi mana" Mamy ta miƙe daƙyar tare da kallon Jakadiya tace "kije ki kira min Gimbiya Afsheen ta sameni a turakata, minti ɗaya na bata idan ta huce sai ranta yayi mummunan ɓaci" Jakadiya ta ɗan risina alamar girmamawa tace "angama sarauniya" Daga nan ta huce turakar Gimbiya Afsheen dan ta sanar da ita saƙon Sarauniya, Mamy ta kalli Sultana Maimuna wacce har lokacin tana turƙushe a ƙasa hawaye na cigaba da zuba daga idanuwanta tace "Sultana ta zo mu tafi, ki daina kukan nan ya isa haka" Sultana Maimuna tace "Mamy ban taɓa neman wani abu a wajenki baki yi min ba, a yau ina son na roƙeki dan girman Allah ki hukunta Gimbiya Ashfeen akan kisan da tayiwa ƙaramar yarinya ba tare da tayi mata komai ba, Mamy karki manta fa a addini ma cewa akayi duk wanda ya kashe wani ɗan adam to shima a kasheshi" Mamy zuciyarta nayi mata zafi tace "ki taso mu tafi Sultana Maimuna" miƙewa Sultana Maimuna tayi tana tafiya tana haɗe hanya har suka fita daga asibitin suka nufi turakar Mamy, Doctor Abiddin bin su yay da ido yana tunanin irin hukuncin da Mamy zata yankewa Gimbiya Ashfeen dan ya fuskanci yau ranta ya ɓaci sosai kuma tana cikin zafin raɗaɗin abin da ƴarta ta aikata, office ɗinsa ya shiga ya xauna a kujerar office ɗin ya cigaba da yin aikinsa, a ɓangaren Bassim kuwa yana shiga ɗakin Ifteehal ya zauna akan gadon tare da kallota, an nannaɗe fuskarta gaba ɗaya da bandeji shi kanshi bandejin ya jiƙe da jini, wani irin sabon kuka ya rushe dashi tare da kama Ifteehal ɗin yana jijjigata "rabin raina duk na san wannan duk laifina ne, ni na bari aka kai ki turakar waccen muguwar, amman na roƙeki ki tashi wallahi bazan ƙara barin kowa ya taɓa ki ba, ina sonki sosai ƴar uwata" Magana yake yana jijjigata da ƙarfin tsiya yana yin kuka mai sosa zuciya, komai ya tuna da sauri ya ɗauki Ifteehal ya fita daga ɗakin, fita yay daga asibitin masarautar gaba ɗaya, ya nufi ɗakin da aka basa, ya shiga ya kwantar da Ifteehal akan katifar dake ɗakin, ya nufi gate ɗakin masarautar komai ya faɗawa fadawan sai gani nayi sun wangale masa gate ɗin ya fita daga masarautar gaba ɗaya.
            *****  ***   *****
Gimbiya Afsheen ce tayi sallama Jakadiya na biye da ita a baya, a tsaye ta tarar da Sultana Maimuna da Mamy suna jiran isowarta, babu wanda ya amsa sallamar saboda dukkansu haushinta suke ji, Gimbiya Afsheen bata damu da irin yadda ta ga mahaifiyarta da ƴar uwarta sukayi mata ba dan ita da su amsa mata sallamar da karsu amsa duk uwarsu ɗaya kuma idan zasu shekara suna ɗaure mata fuska ko a jikinta wai an tsikari kakkausa da ita bata ma san suna yi ba, cikin izza tace "Sarauniya ina Gimbiya Abeela??","tana gidan ubanki shegiya dabba, jahila kawai" Mamy tayi maganar cikin zafin rai tare da wanketa da wani mahaukacin mari hagu da dama sai da ta gera mata sau shida sannan ta kyaleta, Gimbiya Afsheen ta ɗago tare da dafe kuncinta, mamaki ya bayyana akan fuskarta dan tunda suke da Mamy bata taɓa saka hannu ta mareta ba, "Mamy!" Gimbiya Afsheen ta kira sunanta zuciyarta kamar zata fashe hawaye na zuba daga cikin idanuwanta, wani marin Mamy ta ƙara yi mata tare da rufeta da duka ba ji ba gani, Jakadiya ganin haka yasa ta fita ita ma tana zubar da hawayen tausayin Bassim dan kuma ta san Gimbiya Afsheen ta chanchanci fiye da haka, "Haihuwarki bata da wani amfani a gurina gwanda na kasheki na hutu, ke kin zame min bala'i da masifa a rayuwata, ke jahila ce mara imani daƙiƙiyar banza daƙiƙiyar wofi" Mamy duk tana dukanta take wannan maganganun, Sultana Maimuna ce ta samu ta janye Mamy tare da cewa "Mamy ki kyaleta! dukan da kike mata ba zai saka ta shiga hankalinta ba dole ki hukuntata" Mamy tace "ba sai kin faɗa ba Sultana, idan har ban hukuntata ba zuciyata zata iya bugawa kuma ba zan taɓa yafewa kai na ba kuma" Gimbiya Afsheen wacce take a durƙushe a ƙasa tana kukan baƙin ciki, ta ɗago tace "menayi Mamy kikayi min wannan wulaƙancin har da yi min maganganu marasa daɗi" Mamy ta nufeta da niyyar zata cigaba da dukanta, Sultana Maimuna ta tare da tace "A'a Mamy! barta ni zan bata amsar tambayarta, ba sai kin daketa ba" Mamy tace "kafin ki faɗa mata bari na yanke mata hukunci" Sai kuma ta juya musu baya ta cigaba da cewa "sakamakon abin da kika aikata, ni Ɗahiratu bintu Auwal na yanke miki hukuncin yawo a masarautar nan babu takalmi, kuma"......"Mamy!" Gimbiya Afsheen ta kira sunanta da ƙarfi, juyowa Mamy tayi tana yi mata wani maƙasƙancin kallo, miƙewa Gimbiya Afsheen tayi tace "ai komai zaki min ni ba zan taɓa yarda da wannan hukuncinnaki ba, kin manta ni wacece ne, ni ce Gimbiyar masarautar nan kuma mai martaba yana tsananin sona" Sultana Maimuna ta ƙarasa kusa da ita cikin tsananin fushi tace "Afsheen ke baki san darajar mutane ba, kin ɗorawa kanki wulaƙanci da tozarta mutane, kuma dole kiyi abin da Mamy tace dan ita ce sarauniyar masarautar nan ke bakomai ba ce a masarautar nan idan banda ƴarta dan ni yanzu ba zan ƙara ɗaukarki a matsayin Gimbiya ba, dan ke sam baki chanchanta da wannan sunan ba, ke muguwa ce kuma azzaluma, kin kashe Ifteehal dan haka dole ki fuskanci hukunci mai tsanani" Tana kai wa nan ta juyo tana kallon Mamy tace "Mamy ki cigaba" Mamy ta buɗe baki zata cigaba da magana, Gimbiya Afsheen tayi saurin dakatar da ita da cewa "ohhh saboda na kashe wannan ƙasƙantatciyar yarinyar da take ƙoƙarin kashe Gimbiya Abeela shine za'a hu"...Cikin tsawa Sultana Maimuna tace "a ina take ƙoƙarin kashe Gimbiya Abeela, to idan kin manta mu ba mu manta ba Gimbiya Abeela da kanta take faɗa mana saboda Iftee ta bata suna shine ta tashi tana tsalle Iftee ta rufe mata ido zasuyi wasan ɓuya shine ta faɗi ta fasa kai, ni ina so nayi miki wata tambaya shin mekika ɗauki mulki ne??kin ɗauka mulki shine ayi ta wulaƙanta mutane, to karki manta kuma ki saka wannan a zuciyarki duk abin da ka yi to dole kai ma sai anyi maka, kuma idan zaka gina ramin mugunta ta ginashi dai-dai da idan tsautsayi yasa ka faɗa zaka iya fitowa, idan kuwa kika yarda kika gina shi da zurfi abin ba zai miki da kyau ba, Afsheen ke bakomai ba ce idan banda baiwa a duniyar nan, kuma"........"Ya isa Maimuna, ke har kin isa ki dinga faɗa min maganganun da kika ga dama, karki ga cewar ke ɗin ƴar uwata ce wallahi zan iya sakawa ayi miki hukunci mai tsanani dan ina da ƙarfin iko a masarautar nan" Mamy tace "bashi dashi, baki da ikon komai a masarautar nan Afsheen ki tsaya a matsayinki na Gimbiya" Gimbiya Afsheen cikin zafin rai ta fita daga turakar Mamy zuciyarta na tafasa hawaye na ƙoƙarin zubo mata amman bata bari sun zubo ba ta mayar dasu, kamar ance ta kalli bakin gate ɗin masarautar sai ganin Bassim tayi ya shigo hannunsa riƙe da baƙar leda, cikin takunta na isa da izza ta nufi gurinshi zuciyarta cike take dam da tsanarshi "shi maƙasƙancin mutum har abada a haka yake dauwama cikin ƙasƙanci, yau ka saka mahaifiyata ta min abin da bata taɓa yi min ba, akan wai na kashe wannan wulaƙantatciyar, ƙazamar yarinya, to sai me dan na kasheta ko akwai uban da ya isa ya ɗaureni ne idan da akwai ina so a yanzun nan ba sai gobe ba na ganshi yazo" Duk maganar nan tana yinta ne lokacin da ta ƙarasa kusa da Bassim shi kuma ya juya bayansa yana ƙoƙarin nufar ɗakinsa ya ji maganganun Gimbiya Afsheen, nan take ya ji zuciyarsa ta cika da tsanarta da kuma baƙin cikin kashe masa ƴar uwa da tayi amman tunda har ta zo wajensa sai ya tabbatar ya wulaƙantata a bayynar jama'ar masarautar nan sai ya nuna mata ita ɗin ba komai bace,ba ce jahila mara tunani, juyowa yay fuskarsa kunshe da murmushi "Gimbiya Afsheen kike kowa?? ni shawara nake so na baki akan ki koma makarantar islamiyya dan ki samu tarbiyya da kuma ilimin zama da mutane da kuma fiskantar yadda rayuwa take, dan na fuskanci kwata-kwata baki da tarbiyya babu abin da kika saka a gaba sai wulaƙanci, izza, jiji da kai, girman kai, taƙama da kuma mulki, kuma kin san masu irin waɗannan halayyar ya suke komawa?? idan baki sani ba yau zan sanar da ke, suna komawa ne kamar mabarata, ƙarshensu baya taɓa yin da kyau, kuma duk masu irin haka tabbas zaka samesu da ƙarancin ilimin addini, Ubangiji sai da ya karrama ɗan adam a cikin alkur'ani mai girma, anan kaɗai ma zaki san irin yadda ɗan adam yake da daraja da ƙima, ko da yake ba lallai ki san haka ba kin san idan aka ce mutum jahili ne, to sai ana yi masa uzuri, kuma idan mulki kike ji dashi fir'auna ya fiki, idan kuma kuɗi kike ji dashi ƙaruna ya fiki, idan girman kai kike ji dashi shaiɗan ya fiki, idan kuma izza kike ji dashi to a cikin sahabbai akwai waɗanda suka fiki, amman basa yin izza irin taki ki je ki tambayi malamai su faɗa miki irin yadda suke yi domin ki dinga yin irin ta su, ko da yake na manta fa shi daƙiƙi da jahili duk tafiyarsu ɗaya, kuma komai zaka faɗa musu ba za su taɓa fahimta ba" Yana gama faɗar haka ya nufi ɗakinsa ya barta tsaye zuciyarta sai harbawa take, kallon bayin da ke gurin tayi idonta yana ƙoƙarin zubowa da hawaye dan ta san sun ji irin yadda Bassim ya gaya mata maganar da babu wani bawa da ya taɓa tararta gaba da gaba ya faɗa mata, turakarta ta nufa da sauri zuciyarta nayi mata zafi yau babu wanda ya isa ya hanata kashe Bassim zata fille masa kai a gaban kowa, ko ta samu sauƙi zugin da zuciyarta take yi mata.

*WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE, MATAKI UKU NE GASU NAN ZAN JEROSU A ƘASA*

*NORMAL GROUP #300*
*VIP #600*
*SPEACIAL GROUP #1K*

*KU TURO KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER ƊIN 0017770369 UNITY BANK, AISHA YUSUF MUHAMMAD, SAI TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08122188717, KO KUMA HOTON KATI TA NUMBER, BAN DA VTU PLSS*

        *SHARE IT FISABILILLAH👏🏼*

SAUYIN ZUCIYA.Where stories live. Discover now