LOVE AND ROMANTIC STORY

29 1 0
                                    

*SAUYIN ZUCIYA.*
*Littafin kuɗi ne!*

*Ƴar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏽*

*EPISODE 11-12*

*WANNAN SHAFIN NAKI NE DJAMILA COMMENTS ƊINKI YANA KASHENI😂💔KEEP IT UP HABIBIYA💚GASHI NAN NA ƘARA MUKU WANI SHAFIN DAGA WANNAN BA ZAN SAKE POSTING BA, KOWA YA ƘOƘARTA YA SIYI HALALINSA! KU TUNTUBENI TA NUMBER TA WHATSAPP OR CALLS 08122188717, NRML GRP 300, VIP GRP 600, SPEACIAL GRP 1K, LABARI NE MAI DOGON ZANGO*

*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*
HAMMAD SANAA

By Pharty BB
Free Book

*Labarin cin amanar yarda, yayinda ƙaddarar su tasa su yin nesa da juna.*
*Ko ya haɗuwar su zai kasance?*
*Wace irin ƙaddara ce tasa su yin nesa da juna.*
*Wa ya ci amanar wani?*

Wannan amsoshin suna cikin labarin matasa biyun wato HAMMAD SANAA.
It's about limitless and intensely love, romance and destiny.

Domin samu tare da sauran littafanta ku duba handle ɗinta na wattpad @PhartyBB
Ko ku mata magana ta lambar WhatsApp 07037487278

#share fisabilillah👌🏼

*#Saboteurs,Humiliate & Celebration*

Toilet ya shiga, ya kwashi kusan awa ɗaya a ciki bai fito ba, sai chan gashi ya fito, yana ɗaure da wani ɗan ƙaramin towel a kugunshi da alama wanka yay, sai da ya tsane ruwan da ke ɗiga daga jikinshi, da wani towel ɗin daban, sannan ya shafa wani mai tsananin daɗin kamshi, drower ya ƙarasa tare da ɗauko kayan da zai saka, gejeren wando ya saka wanda ko gwiwarsa bai kai ba, sai wata rigar kalar wandon pink colour ya saka, gurin mudubi ya ƙarasa ya ɗauki wani turare ya shiga fesawa a jikinsa, wayarsa ce ta hau ruri, kallon wayar yay wacce take kan bedsite drower tare da yatsine fuska, kiran ya katse aka sake kira, wani dogon tsaki yaja sannan cikin takunsa na isa ya ƙara gurin da wayar take ya ɗauki wayar tare da kallon screen ɗin wayar  *MOMMAH* ya gani yana yawo akan screen ɗin, zama yay akan tafkeken gadon ɗakinsa wanda kana kallonsa kasan an zubar da miliyoyin kuɗi wajen mallakarsa, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana girgizawa sannan ya ɗaga kiran ba tare da yace komai ba, daga chan ɓangaren Mummy tace "Yareema Ɗalhat, har yanxu ban ji kace komai ba game da abinda muke son tsara, ka san fa ban da wani buri a duniyar nan irin na ga bayan wannan shashashar yarinyar, kuma yau na ji wani labari wanda ya daɗe yana ban mamaki" Yareemah Ɗalhat yace "wani labari ne Mummy?"Mamaki ne ya kamani na dinga tunanin daman yana jin hausa ne, dan yana yinsa bai nuna alama ko kaɗan ba na yana jin hausa, Mummy tace "wani maƙasƙancin bawanta ne ya wulaƙantata a gaban jama'ar masarautar, amman bata iya ce masa komai ba, kuma mai martaba ya tara jama'a za'a hukuntashi, ta fito ta hana, ta fara kawo wani soki burutsunta" Wata iriyar mahaukaciyar dariya Yareemah Ɗalhat ya saki, zuciyarsa cike da farin ciki ya fara cewa "gaskiya zan so ganin wannan jarumin bawan, yanzu duk izzarta ta da taƙamarta amman ace yau wani bawa ya".... da sauri Mummy ta dakatar dashi da cewa "ni ba wannan nake son ji daga wajenka ba, kasan dai irin burin da muke son mu cimma akan Gimbiya Afsheen da mai martaba, yanzu wane shiri ka ke yi dan tarwatsa su, ba ka ji irin yadda nake ji ba ne Yareemah Ɗalhat shiyasa baka mai da hankalinka ba akan mun ga bayansu" Yareemah Ɗalhat yay wani irin mugun murmishi ya ɗauki kusan mintina biyar ba tare da yace komai ba sai chan ya fara magana kamar wanda aka yi masa dole "Mummy baki san irin shirin da nake yi ba ne, shiyasa kike ganin kamar ban damu da cikar muradinmu ba, Mummy ni na fiki son ganin mai martaba ya zama sheƙaƙƙe ita kuma wannan shashashar yarinyartasa mai shegen ji da kanta sai mun wulaƙantata, mun nuna mata ita ɗin ba komai bace, sannan ita ma mu tura garin da ba'a dawowa, wannan uwartata kuma da take ji wani ɗaɗɗaga kai ita bata yarda ba wai ita sarauniya sai mun mayar da ita baiwarmu da waɗannan ƴaƴan nata Sultana Maimuna da kuma mahaukaciyar nan, ki bari na dawo gida ki ga yadda mulkinsu zai dawo gurinmu karki yi aikin banza nake yi anan, wata maƙarƙashiyar nake shirya musu" Mummy tace "Dakyau yarona sai yanzu na san cewar ina da ɗa mai tsananin son abin da nake so, amman ban gane abin da ka ke nufi da mahaukaciya ba??wacece mahaukaciyar?? daman a cikin ƴaƴan Ɗahiratu akwai mahaukaciya ne??" Dariya sosai Yarima Ɗalhat yay tare da cewa "akwai mana, Mummy wai kina nufin kin manta Abeela ne, mutumin da ya rasa hankalinsa ai ya zama mahaukaci na gaske ma kuwa" Dariya ita ma Mummy tayi sosai tace "ai kai na baka faɗa min yadda zan gane ba, da sai ka ce min Abeela mentel ka ke nufi" Yareema Ɗalhat yace "ai ina matuƙar jin daɗi ganinta a haka, zan so ta dauwama dan sai yafi bada nishaɗi" Mummy tace "ai insha Allahu a haka zaka zauna har lokacin mutuwarta yay ta ƙara gaba" Yareemah Ɗalhat yace "Mummy sai anjima dan akwai inda zan je ne yanzu" Mummy tace "to shikenan" sannan ta kashe wayar zuciyarta cike da farin ciki burinta ya kusan cika, shi kuma Yareema Ɗalhat suna gama waya da Mummy yay wurgi da wayar ta faɗa kan kujara, fuskarsa kunshe da wannan murmishi kana ganin yanayin yadda yake yin murmushi kasan na mugunta ne, "Sarki Muhammad Bello da kuma Afsheen Muhammad Bello da ace zan iya baku shawara da zan baku shawarar kuyi duk yadda zakuyi dan kar na dawo gida, domin dawowata tana tattare da hatsari, bala'i, masifu iri-iri da zarar na dawowa zan tarwatse ku zan kasheku ɗaya bayan ɗaya" yay maganar tare da tintsirewa da dariya, tashi yay tare da fita daga ɗakin, gurin da yake ajiye motocinsa ya nufa ya shiga ɗaya daga ciki ya ja ya nufi *Oberoi Wilflower hall* babban swimming pool a ƙasar indian, yana zuwa yay parking ɗin motarsa, ya fito daga cikin motar irin yadda ya fito daga cikin motar ma kaɗai zaka fahimci wannan matashin saurayin yana da tsananin izza, jin kansa da kuma mulki, Ɗalhat irin mazan nan ne basu ɗauki mace a bakin komai, suna ganin mata kawai amfanin su jiyar dasu daɗin zumarsu bayan haka basu da wani amfani a garesu, sun ɗauki mace kamar riga ce, kullum da irin wacce zasu chanza, Ɗalhat mutum ne da yake tsananin son mata yadda kasan bunsuru haka yake, kai zan iya cewa yafi ma bunsuru dan shi ko da jaririyar yarinya ya kyalla idonsa akanta ya ga tayi masa to insha Allahu sai ya rabata da budurcinta ko da kuwa ƴar gidan wacece, aiki ne ya kawosa ƙasar indian kusan shekara ɗaya kenan, ba tare da ya taɓa zuwa ya ga gida ba, tun da ya je indian, gurin cike yake da mata da maza duk yawancinsu tsirara suke wasu kuma daga su sai bra da pant suna cikin swimming pool suna wanka su da samarinsu, wata budurwa ce  ta zo da gudu tare da rumgumeshi daga ita sai wani kyalle a jikinta zan iya cewa dashi da babu duk ɗaya dan ana iya hango nonuwanta waɗanda basu da wani girma da sauran surorin jikinta, lumshe idonsa yay tare da danna kansa a cikin ƙirginta ƙyallen da ta rufe jikinnata ya kunce ya faɗi ƙasa, nan ya fara tsotsan nonuwanta kamar wani mayunwacin zaki, ɗurƙushewa sukayi a ƙasa, saboda ƙafafuwansu sun gaza ɗaukarsu, gaba ɗaya idanuwansu sun rufe kowannansu yana ƙoƙarin ganin ya ba wa ɗan uwansa daɗin zumarsa, nishi kawai suke yi, Ɗalhat ganin baya jin daɗin tsotsarta a ɗurƙushe ya kwantar da ita a gurin, yana ƙoƙarin ƙara hawa kanta ta jawosa jikinta tare da birgimi shi ya koma ƙasa ita ta hau kansa, kafin yay wani yunƙuri ta kama lips ɗinsa tana tsotsa tare da fara cire masa kayan jikinsa, sai da ta tabbatar tayi masa tsirara sannan ta cigaba da tsotsar ko ina na jikinsa gaba ɗayansu sun gama gigita basu da wani buri irin sukunsanci junansu, na ƙarƙare muku zance sai da su ka gama aikata baɗalarsu a gurin, duk da tarin mutanan da suke gurin suna kallonsu ko da yake su a gurinsu wannan ai ba komai ba ne, sai da sukayi wanka a cikin swimming pool ɗin tare sannan suka fito Ɗalhat daga shi sai gejeren wando rigarsa a hannunsa, ita kuma budurwarta sa ta ɗaura ƙyallennata, wani guri suka shiga ba su yi wani tafiya ba sai ga su a wani babban bedroom mai ɗan iskan kyau wanda ya sha ƙyalƙyalin kayan ɗaki, kan gado suka faɗa suka ɗora daga inda suka tsaya, ni kuma nace amman Ɗalhat ka ci ka babban bunsuru.
*BABBAR MASARAUTAR GARIN KANO.*
Bayin gidan sun gyara masarautar sosai, ko ina yay fas sai ado su ke yi wa bangon jikin ginin masarautar dan al'adar masarautar ce indai za'ayi wani taro na farin ciki dole sai an yi wannan adon, cikin takunta na izza ta fito daga cikin turakarta tayi kyau sosai dan kullum idan tayi kwalliya ƙara kyau ta ke yi, farar atamfa ce a jikinta an yi wa atamfar kwalliya da wata flower babba da wata pupple ɗin colour, ta dora wata tsadaddiyar alƙyabba wacce take jan ƙasa akan atamfar, tana tafiya ana zuba mata wasu furanni masu kamshi a ƙasan da aka share tana takawa tana tafiya, idanuwanta ne suka sauka akan Bassim wanda ya dage yana yin aikinsa cikin kwanciyar hankali, nan take yanayin fuskarta ya chanza farin ciki da annurin da suke kan fuskarta duk suka gushe, ta tsani ganin Bassim da ba dan akwai mugun ƙudurinta akansa ba da tuni ta ƙawar dashi daga doran duniya, tuno irin shawarar da Falmata ta bata tayi anan take wani farin ciki ya cika mata zuciya dan har sai da ta saki wani lallausan murmushi "nan gaba kaɗan za ka fahimci irin shu'umancina, kai da kanka zaka roƙi mutuwarka dan sai na tabbatarka biya abin da ka yi min" duk a zuciyarta ta ke yin maganar, chan kuma ta tuno da Ifteehal dan ta ji labarin yarinyar bata mutu ba "Falmata!" ta kira sunan Falmata cikin wani irin salo na mulki, Falmata wacce take bayanta ta matso tare da sunkuyawa tace "na'am ranki shidaɗe","ina wannan ƙasƙantatciyar yarinyar take?" Falmata ta fahimci Ifteehal take nufi dan ita kaɗai take kira da ƙasƙantatciya "Am ranki shidaɗe tana gurin sarauniya" Gimbiya Afsheen cike da takaici tace "sarauniya kuma?? me take yi a gurin Mamyna??" Falmata tace "ranki shidaɗe wallahi nima ban sani ba, amman ɗazu na ga Jakadiya ta ɗauketa ta shiga da ita turakar sarauniya","meyasa Sarauniya zatayi min haka, meyasa take son ta dinga jan yarinyar nan ƙasƙantatciya ƴar talakawa mara galihu, to wallahi ba zan yarda ba dole sai na ɗauki mataki akan haka" Tayi maganar cikin fushi tare da nufar turakar Sarauniya, suna isa suka tsartsaya a kofa ita kuma Gimbiya Afsheen ta shiga cikin turakar ba tare da tayi sallama ba, abin idanuwanta suka gane mata ne yasa tayi saurin zaro ido zuciyarta ta shiga harbawa da ƙarfi, Ifteehal ta gani a jikin Mamy an shiryata cikin wasu ƴan kanti waɗanda aka yi musu kwalliya da ruwan gwal, tayi kyau sosai gashin kanta  an tifkeshi a tsakiyar kanta, gefe guda kuma Sultana Maimuna ce take yi wa Gimbiya Abeela kwalliya, dukkansu ka kalli fuskokinsu zaka tabbatar suna cikin farin ciki matsananci "keeeeee!"Gimbiya Afsheen tayi maganar cikin tsawa da ƙunar zuciya, gaba ɗayansu suka juyo suna kallonta, Ifteehal tana juyowa ta ga ita ce da sauri ta ƙanƙame Mamy jikinta na rawa, ƙarasawa kusa da inda Mamy take tayi tana shirin fisgota daga jikin Mamy "Afsheen!" Mamy ta kira sunanta cikin kakkausar murya, Gimbiya Afsheen ta dakata daga ƙoƙarin fisgo Ifteehal tana kallon Mamy ba tare da ta amsa ba, Mamy ta cigaba da cewa "idan kina buƙatar ganin ɓacin raina to ki kama ko da rigar yarinyar nan ki ga yadda zan yi da ke, idan kin san kin zo ne dan ki tayar min da fitina ko kuma kiyi wulaƙancin da kika gada a gurin ubanki to ki gaggauta fitar min daga turaka" Gimbiya Afsheen tayi murmushi mai ciwo "hmmm! Mamy ina so na tambayeki wani abu, shi wannan ƙasƙantatciyar yarinyar mabaraciya asiri tayi miki ne, wallahi ina mai tabbatar miki da cewa idan ita da wannan mahaukacin yayannata ne sukayi muku asiri ku ke ta wani rawar jikin akansu to sai na karyashi kuma daga nan na wulaƙantasu su bar masarautar nan dan ba ta ubansu ba ce" Tana gama maganar ta fita waje fuuuuu! kamar wacce ake buga mata iska, Sultana Maimuna ta ja tsaki tare da cewa "Allah ya shiryeki, Allah ina roƙonka ka kawo kasa na ga lokacin da Gimbiya Afsheen zata samu *SAUYIN ZUCIYA* " Mamy tace "Amin" Gimbiya Abeela ta matso kusa da Mamy tana cewa "Mamynmu kin ga muguwa ta tafi" Mamy ta shafa kanta tace "A'a Gimbiya Abeela ki daina ce mata muguwa ƴar uwarki ce" Turo baki Gimbiya Abeela tayi tare da cewa "ni sunana Basma ba,wannan sunan ba, kuma ai ita muguwa ce ko ƙawata" Ta ƙarasa maganar tana kallon Ifteehal wacce har lokacin tana ƙanƙame da Mamy, kai ta gyaɗa mata alamar eh dan har lokacin gaba ɗaya jikinta rawa yake ta kasa magana, Mamy tace "to shikenan ku cigaba da shiryawa kafin a fara taron" Tayi maganar tare da miƙewa tana rumgume da Ifteehal a jikinta bedroom ɗinta ta shiga, Sultana Maimuna ta kama Gimbiya Abeela ta cigaba da yi mata kwalliya, a ɓangaren Gimbiya tana fita daga turakar Mamy ta ci karo da wani bawa tsoho ne sosai dan daƙyar yake iya tafi, yana share fulawowin da aka zuba mata a ƙasa, wata muguwar tsawa ta daka masa tare da ƙarasawa gurin ta ɗaukeshi da mari, tsohon nan ya faɗi ƙasa wanwar tare da dafe kan kuncinsa "kiyi haƙuri Gimbiya tuba nake ranki shi daɗe" Gimbiya Afsheen cikin fushi tace "matsiyaci kawai, kazo kana share gurin da zan taka na wuce, yanzu uwarka ka ke so ka na taka na huce","ita mahaifiya da kike gani tana da matuƙar girma da daraja, duk wanda yasan darajar mahaifiyarsa ba zai taɓa yin ƙoƙarin zagi ko cin mutuncin mahaifiyar wani ba, kuma ina so ki sani karki ga shi ɗin bawanki ne wannan zai yi sa'an mahaifinki ko ma ya girmeshi amman haka ki ka ɗaga hannu kika zabga masa mari, ina so ki saka wannan a ranki duk abin da ki ka yi wa mahaifin wani ko mahaifinyar wani to kema sai an yi wa naki iyayen wannan faɗar ubangiji ne kama tudini tu dan" Bassim ne yay maganar yana kallon Gimbiya Afsheen fuskarsa babu alamar tsoro ko kaɗan, sunkuyawa yay ya ɗago bawan tare da kakkaɓe masa jikinsa sai da ya gama tsaf ya ɗago cike da tausaya masa yace "sannu Baba" Bawan yace "yauwa nagode" Bassim ya juya yana yi wa Gimbiya Afsheen wani irin wulaƙantatcen kallo, Gimbiya Afsheen ranta ya gaba ɓaci sau biyu kenan yana wulaƙantata a gaban bayin gidan, amman yau ta ƙudurci anniyar sai ta yi masa abin da ba zai taɓa mantawa ba, kallonsa take ido cikin ido tace "yau ina so na san waye ubanka a garin nan" Falmata ta ɗan saki murmushi tare da cewa "ranki shi daɗe ai wannan bashi da iyaye dan kaf unguwarsu idan ki ka je ki ka tambaya su waye iyayen Bassim cewa miki za'ayi basu san su ba" Gimbiya Afsheen ta ɗan saki murmishin jin daɗi yanzu ta samu abin da zata tozartashi a gaban kowa "Shege ne kenan" Falmata tace "tabbas haka yake dan kaf unguwarsu haka suke kiranshi da Bassim shege ko kuma su ce Ifteehal shegiya" Gimbiya Afsheen ta saki murmushi har lokacin idanuwanta akan Bassim suke wanda ransa ya gama ɓaci wani irin bugu ƙirginsa yake yi da ƙarfi, wata sabuwar tsanar Falmata ce ta fara cika zuciyarsa tunda yake ba'a taɓa ci masa mutunci irin na yau ba "kai kana shege amman kazo ka na sakawa masu iyaye baki a cikin al'amuransu to"...... Falmata ta katseta da cewa "ranshi daɗe ai shi kansa ma bai san iyayennasa ba, dan ko gidan kansu basu da shi haka suke yawo shi da ƙanwarsa su bi wannan inuwar su bi waccen inuwar, ni a labarin da na ji ma cewa aka yi a bola aka tsicesu lokacin shi bai huce shekara takwas ba ita kuma ƙanwartasa tana jaririya sai wata mabaraciya ta ɗaukesu ta kai su gidanta ko kwana shekararsu biyar a gurinta ta mutu ƴaƴanta suka koresu daga gidan, suke yawon bara akan titi" wata iriyar dariya Gimbiya Afsheen tayi tace "ashe kai a cikin matsiyatan ma kai faƙiri ne, to bara ka ji in faɗa maka ni Afsheen ina da iyayena ina da mulki, kuɗi, izza, taƙama da kuma iko zai iya sawa a ɗaureka babu abin da ka isa ka yi, banza shege matsiyaci kawai, ya kamata ka fara jin kunyar kanka kazo kana wani fiffisga kamar wani mai iko ashe shege ne shegen ma wulaƙantatce" Tana gama faɗar haka ta sa kai ta wuce xuciyarta cike da farin ciki, Falmata kuwa bata iya ɗagowa ta kalli Bassim ba, ta san tabbas zai tsaneta sosai amman dole tayi haka dan ta tseratar dashi daga tarkon da Gimbiya Afsheen take ƙoƙarin ɗana masa ta samu ta ruguzashi, bin bayan Gimbiya Afsheen tayi da sauri suke shige turakarta, wannan tsohon bawan ya kalli Bassim dan su kaɗai suka rage a gurin sauran bayin duk sun bi bayan Gimbiya Afsheen, dafashi yay tare da cewa "Ka yi haƙuri na san zaka ji zafi sosai a cikin zuciyarka, amman ka ɗaure wata rana sai labari" Bassim ya ɗan ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali baya tunanin zai iya yin magana a halin da yake ciki dan bakinsa ya riƙe ba zai iya motsashi ba, wucewa yay ya koma ɗakin da aka bashi ya kwanta akan katifar ɗakin idanuwansa na kallon saman ɗakin ya riƙe ƙirginsa da yake yi masa wani irin mugun bugu da hannunsa yana yin duk addu'ar da ta zo bakinsa, a hankali ya samu nutsuwa bacci ɓarawo ya sace sa dan haka Bassim yake indai yana cikin ɓacin rai bai yi bacci ba baya taɓa samun nutsuwa.
masarautar ta cika da al'umma babu abin da ka ke ji sai busar sarewa da fadawa suke yi, anyi shagali sosai na taya sarki murnar samun kwangila, sai da daddare sannan aka watse kowa zuciyarsa cike da farin ciki, Gimbiya Afsheen ce zaune akan kujerar alfarmarta gefe guda Falmata ce a ɗurƙushe a ƙasa, kallon Falmata tayi tace "tun da nake da ke Falmata baki taɓa faranta min rai irin na yau ba, na san wannan shegen yana chan zuciyarsa cike da ɓacin ciki" Falmata ta ɗan yi murmushin yaƙe tace "ai ranki shi daɗe wannan shi ake kira wasa farin girki, tunda nace zan taimaka miki wajen ganin kin wulaƙantashi to kawai ki zuba ido ki gani, shi da kansa zai ɗauki shegiyar ƙanwarsa su gudu daga masarautar nan su koma yawan barace-baracen da sukeyi akan titi" Gimbiya Afsheen "shiyasa duk shawarar da za ki bani ba na taɓa watsar da ita" Falmata dai tayi shuru a zuciyarta tace "tabbas yau kin sa na aikata abin da ya tsaye min a raina, ya Allah ka yafe min ka sa wannan bawan naka shima ya yafe min, ke kuma Gimbiya Afsheen na san tabbas watan sai kin samu *SAUYIN ZUCIYA*" Haka dai Falmata ta dinga yi mata hirar duniya, Gimbiya Afsheen tana sauraronta fuskarta kunshe da murmushi.
*YARIMA ƊALHAT*
Zaune yake akan kujera shi kaɗai yana zane, kusan mintina talatin ya kwashe yana yin zanen sannan ya ɗago yana murmushi tare da nuna wani ɓangare daga cikin zanannasa da yay zanan wata budurwa daga ƙasa ya rubuta sunan Gimbiya Afsheen yace "ta kanki zan fara Afsheen sai na shiyasa miki gadar zaran da ba za ki iya tsallakewa ba, da zarar na gama da ke kuma zan koma kan mai martaba na san kece rauninsa da zarar na sheƙaki lahira zai rage bashi da wata walwala zai rasa farin cikinsa na har abada daga nan shima idan na gama shiyasa masa makirci zan sheƙashi gurin da na kai ki daga nan kuma na dawo kan ƴan uwanki Sultana Maimuna da wannan mahaukaciyar yarinyar Abeela  su ba zan sheƙasu lahira ba su da uwarki zasu zama bayina zan wulaƙantasu fiye da yadda kike wulaƙanta bayinki sai sun kwanta a ƙasa na takasu na huce" Yay maganar tare da fashewa da dariya, shin ya kika ga wannan wasan Afsheen yay maganar yana nuna hoton Gimbiya Afsheen da ya zana😫✍🏽.

*_Ƴar gidan Sha'aban ce._*
08122188717

SAUYIN ZUCIYA.Where stories live. Discover now