*SAUYIN ZUCIYA.*
*PAID BOOK**'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban💗*
_FREE PAGE_
*EPISODE 3-4**Whatsapp number https://wa.me/+2348122188717*
*#Dislike*
*BAYAN AWA D'AYA.*
Bassim ya saka Ifteehal a gaba yana yi mata nasiha, irin yadda ya tattara hankalinsa gaba d'aya wajen yi mata nasiha, zakayi tunanin wata babbar yake yi wa nasihar, "Ifteena kin ga yanzu ke kad'ai ce nake kallo na ji dad'i a zuciyata, ina son ki zama mai hak'uri a duk inda kika tsinci kanki, ina tsananin tausaya miki Ifteena saboda ke d'in macece kuma yarinya k'arama, ban da wani buri irin na ganki cikin matsanancin farin ciki wannan shine BURIN RAINA" Ifteehal wacce ta nutsu tana sauraron Yayanta idan ka ga yadda ta zauna take jin abubuwan da yake fad'a mata zaka sha mamaki dan ko motsi batayi cikin gwaranci ta fara magana "Yayana zan yi hak'uri kamar kai ka ji, ba na son ka na shiga cikin damuwa Yayana so nake kullum ka dinga dariya ka na murmushi kamar ni! hakan zai saka na ji dad'i sosai" Duk da irin yadda yake cikin bak'in ciki sai da yay murmushi, ita ma murmushin ta sakar masa, haka dai Ifteehal ta dinga yi masa gwarancinta wani ya gane wani kuma baya gane abin da tace.*GIMBIYA AFSHEEN POV.*
Gimbiya Afsheen cike da ɓacin rai take kallon Falmata duk da kasancewar Falmata baiwar Gimbiya Afsheen ce! amman jininsu ya zo d'aya da ita sosai, dan har tana zama ta fad'a mata abin da yake damunta, idan Falmata tana da shawarar da zata bata ta fad'a mata, kuma aka yi sa'a duk irin shawarar da Falmata zata fad'awa Gimbiya Afsheen tana d'auka sosai! kuma idan tayi amfani da ita tana yin nasara! ta ga komai yayi mata yadda take so! wannan dalilin ne yasa ta nad'a Falmata a mai bata shawara, cikin izza,isa,tak'ama da kuma mulki take magana "Ban san dalilin da yasa na d'aukeshi a aiki ba, tun farkon kallon da nayi masa na ji na tsaneshi matuk'a, ko ganinsa ba na son nayi, ban san meyasa ba tun lokacin da na d'auki shi aiki! zuciyata gaba d'aya a dagule take, wani irin haushin kaina nake ji fiye da tunaninki, so nake na ga baya cikin duniyar nan, bayan na gama wulak'antashi hakan ne burin raina" Falmata ta sauk'e wata iriyar gauruwar ajiyar zuciya tace "Allah ya huci zuciyarki ranki ya dad'e 'yar sarki! jikar sarki! ki daina b'ata ranki akan wannan bawan, karki manta fa shi d'in bawanki ne dan haka ki kwantar da hankalinki dan daga shi har k'anwarsa a hannunki suke sai yadda kikayi dasu!" Mik'ewa tsaye tayi tana kallon Falmata cike da bak'in ciki tace "Me kike nufi?? Har da k'anwarsa ya zo masarautar nan??" Falmata ta d'an sunkuyar da kanta alamar girmamawa tace "Ba da ita ya zo ba ranki ya dad'e, bayan kin amince kin d'aukesa aiki ne shine ya fita bayan ya nemi izini a gurin Jakadiya yaje ya d'aukota, amman k'anwarta sa yarinya ce dan"..... Cikin tsawa Gimbiya Afsheen tace "Dakata! Bana son kiyi min wani bayani, wato ita jakadiya har tana da matsayin da zata amince wani ya d'auko wata ya shigo masarautar nan da ita ba tare da ta faɗa min na amince ba, har tana da wannan matsayin" Tayi magana tana tafiya ɗay-ɗay cikin izzah "Falmata ki je ki kira min Jakadiya" Tayi maganar cikin muryar ɓacin rai, Falmata jikinta a sanyaye ta miƙe dan bata yi tunanin gimbiyar bata san Bassim ya ɗauko ƙanwarsa ba, ta san yau Jakadiya zata sha wulaƙanci da ƙasƙanci "To ranki ya daɗe yadda kike so haka za'ayi" Falmata tayi maganar tare da fita daga ɗakin, mintina uku kawai Falmata tayi sai gata ta dawo tare da Jakadiyya gaba ɗayansu suka zube a gabanta, Jakadiyya tace "Gani ranki ya daɗe" Gimbiya Afsheen tace "Uban waye ya baki damar saka wanchan maƙasƙancin mutumin ya d'auko wata ƙazama wai da sunan ita ma ta zauna a masarautar nan" Jakadiya tace "ranki ya daɗe Allah ya huci zuciyarki, ayi min aikin gafara, wallahi ban yi tunanin ranki zai ɓaci ba, dana ji yace ƙanwarsa ce kuma ƙara"..........."Yi min shuru tsohuwar banza! shashasha, ƴar talakawa ke kina ƴar matsiyata har kin isa ki yanke hukuncin abin da ya dace da wanda bai dace ba, ni kaɗai nake da wannan ikon a masarautar nan, ko mai martaba ba ya taɓa shiga abin da ya shafeni, ni yake bari na gudanar da komai" Jakadiya ta sunkuyar da kanta tana cewa "Ki gafarceni ranki ya daɗe in sha Allah! hakan ba za ta sake faruwa ba" Gimbiya Afsheen ta shiga yin taku kamar tana jin tsoron ƙasa "Jakadiya dole sai na hukuntaki domin babu wanda yake min shsh-shigi a cikin al-amarina" Shigowa Sultana Maimuna tayi ba tare da tayi sallama ba tana kallon gimbiya Afsheen cike da baƙin ciki tace "Ai Mamy ta san Bassim zai ɗauko ƙanwarsa, dan lokacin da Jakadiya ta basa umarni ya ɗaukota! taje ta faɗawa Mamy, dan haka sai dai ki haɗa da Mamy ki hukunta har da ita" Gimbiya Afsheen ta yi wa Sultana Maimuna wani irin kallo tare da cewa "Ke har kin isa, in yanke hukunci ki zo kina faɗa min maganar banza, ki iya bakinki Sultana Maimuna idan ba haka ba zaki ɗebi haƙoranki a hannunki" Sultana Maimuna tace "Gimbiya Afsheen kenan! ai daman ita gaskiya ɗaci gareta, karki dinga yin tutiya da mulkin da kike dashi, ki ce kin samu damar wulaƙanta mutane, izza,mulki, taƙama da kuma iko duk ba komai ba ne a duniyar nan dan".....Wani irin azababben mari Gimbiya Afsheen ta wanke Sultana Maimuna dashi har sai da ta sunkuya, ɗagowa tayi tana kallonta ta saki murmushin yaƙe tace "Ban yi mamakin marin da kika yi min ba gimbiya, amman ni ba zan dena faɗa miki gaskiya ba, dan na san wata rana dole sai kin samu *SAUYIN ZUCIYA!* kuma wannan muguwar zuciyarta ki da bata son a faɗa miki gaskiya kuma kina nuna tsantsar tsana ga mutane! ina baki shawarar da ki dai-dai ta! ta dan ki samu damar da zaki dinga tanƙwarata" Sultana Maimuna ta kalli Jakadiya tace "Mama Jakadiya tashi mu tafi" Jakadiya ta miƙe daƙyar ta huce gaba Sultana Maimuna na bin ta a baya har suka fita daga turakar Gimbiya Afsheen.
YOU ARE READING
SAUYIN ZUCIYA.
Romanceta tsaneshi sosai duk da yadda yake bawanta, amman alƙalamin ƙaddararta yasa ya auri ƴar uwarta.