TSAKURE

333 6 0
                                    

ALMAJIRA
NOBLE WRITERS

Bismillahi Rahmanir Rahim
_TSAKURE_

Tagumi ta yi da hannayen ta duka biyu yayin da hawaye ne ke kwaranyo wa daga cikin kwarmin idanuwan ta, ta hanga gabas da yamma, kudu da arewa mabarata ne makil suke ta cincirindon karɓar sadakar waina.

'Oh ni Hadiza, duniya ina zaki kai mu babu uwa babu uba, babu wani namu da muka sani cikin ayarin mabaratan nan, azanci na hausawa su kan ce komai nisan duhun daji akwai karshen sa, to ko yaushe karshen zai zo?'
Ba na ce bani da ƴan uwa ba domin mabarata sune komai nawa bani da kamar su don sune ahali na gaba da baya....a hankali ta kalli cikin da ke jikina  wanda ya fito a ɗan shatin bakar boubou rigar abayar da na sanya, na runtse idanuwa don har cikin kwakwalwa ta ina jiyo yadda yake motsi yana daɗa kwalfe duk wata cimar da tayi saura cikin cikina , Yayin da idanuwana suka sauka akan kanwa ta Sofia mai shekara uku cur a duniya sam yarinyar bata da hayaniya don ba ma ta iya magana ba uwa uba hakuri.......na janyo ta jikina na rungume ta, Lokaci ya yi da ya kamata na jajirce akan nema mana abin da zamu ci na kuma yi namijin kokari wajan kare kanwata daga shafar fentin bakin tabo kamar yadda ya auku da ni.

Tafiya ce mai tsayi cikin ayarin mabarata kallo ɗaya za ka yi ma dubbannin al'umman ka hango Tsoffi daddatawa, Ƴan mata, ƴan samari, yara sa'annin ta da kuma na ƙasa da ita, da kuma jarirai, duk kan su basu da matsugunin tsugunnawa.

Cikin wannan lokacin muka yaɗa zango a garin charanci cikin jihar katsina wacce muka taso tun daga Bakura cikin jihar zamfara.....A galabaice na zauna daɓas yayin da na sauke Sofia wacce take goye a bayana, na buɗe wani jarkar ruwa na kwalkwala tsabar yunwa da kishi da suka haɗu sai suka sanya ni kakarin amai bayan na ajiye jarkar ruwan take yanke na fara kwararo amai babu kakkautawa domin yunwar ta riga da ta ta cinye cikin, nan na kwanta a kasa ina mai da numfashi a hankali, lokaci guda ƙwanya ta ta tariyo min maƙasudin wannan tafiya da muke ta yi ba dare babu rana kuma babu mai taimakon ka saboda kowa ta kansa yake yi.

MAFARI

Kauyen Bakura, wani kauye ne ko ince wata "ƙaramar Alƙarya"da ke tsakanin Zamfara da Sokoto, kauyen ya na karkashin jihar Zamfara state.

Mutanen Garin mafi a kasarin su Hausawa ne sai Fulani kalilan, Babbar sana'ar mutanen garin shine Noman rani duk dama karamin gari ne ba kasafai suka cika yin kasuwanci ba.

Bakura local government suna da makarantun allo ta almajirai, wanda mafiya a kasarin yaran garin, samari da ƴan mata, yara yara duk shi suka fi zuwa. Tsiraru ne ke zuwa makarantar bokoko wanda sukai mishi lakabi da "karatun nasara"

Dubannin mabarata sun yi cincirindo a bakin kofar masallacin garin kowa yana jiran kiris ya amshi rabon shi Yayin da wasu bara su keyi daga wannan kusurwa kusurwa, kwararo kwararo,Lungu lungu, saƙo saƙo.


Mabaratan a kalla ba'a kasari ba sun kai mutane ashirin ko fiye da haka ma kowa da irin larurar da yake ɗauke da ita, wasu larurar gaskiya wasu kuma lalurar karya, Shiyasa suke bara don samun kuɗi da kuma abin da zasu ɗan ci su da iyalansu, duk dama da muryoyi ɗaya ko ince a tare suke jero wakar barar sai dai wata zazzakar murya wacce ta fi kowacce murya daɗin sauraro, kana iya jiyo muryar amma yawan al'ummar dake zazzaune wasu suna tsaye ba lallai ka gane wacece mai ɗauke da wannan muryar ba.

A bamu na Allah "babiya Allah"
A bamu na Allah "babiya Allah"
Muna bara a bamu don Allah
"babiya Allah"
A bamu don Ma'aikin Allah
"babiya Allah"
A bamu don Mahaliccin mu
"babiya Allah"

Ita ce kalmar wakar da mu mabarata muka yi amanna da ita kuma muke iya rairata a ko wani lokaci ko mun koshi ko bamu koshi ba, ko an bamu ko ba a bamu ba, bamu kasance masu godiyan Allah ba a wannan sana'a ta bara, shiyasa bama taɓa ganin cigaba a ko da yaushe muna sanye cikin tsummokara, cike da talauci, cike da kazanta shiyasa jama'a da dama suke kyamatar mu.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now