15

59 4 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
14

______________________________________
KADUNA

Ina nan zaune a gefen wani dakali daga bakin kofar makarantar idanuwa na suna ta kalle kalle hankali na duk ya karkata zuwa cikin makarantar ina tunanin yadda zan samu na shiga.

Masu tsaron kofar makarantar wanda suke sanye da kayan ma'aikata ma'ana ma'aikatan da suke tsare kofar mashigar makarantar...duk sun du ku fa suna binchika bayan motoci suna tantance motocin da zasu shiga makarantar a dai dai lokacin na lallaɓa nayi shigiwata tafiya kawai na keyi ba kakkautawa kamar dai na san makarantar, ajijuwan ɗalibai suna ta farko gini ne mai bin ɗan uwan sa wato bene, manya manyan gina ginan su suka burge ni, na cigaba da tafiya kasancewar ɗalibai sun yi yawa ga kuma jama'a kowa ya sanya kayan gida, ba za ayi tunanin wacece ni ba hakan ya bani damar zuwa filin da mafi yawan ɗaliban anan suke zama don samun cikakken lokacin hira da ƴan uwan su da yawan su suna ta shagalin cin abinci, ana ta ɗaukan hotuna, idanuwa na suka sauka kan wani ahali kyawawan gaske sun shimfiɗa katuwar dadduma sun jera cololi na abinci akalla ba a kasari ba sun kai goma ban da abin sha da kwandon kayan marmari da kuma kayan makulashe, gefe ɗaya mai musu hoto ne yana ta musu vedio da wayar sa...yarinya ce wacce ba zata wuce sa'a ta ba sai iyayen ta su biyu da kuma kanin ta da kanwar ta da alama gaba ɗaya sun zo mata visiting ne, sai ahalin suka burge ni wanda hakan ya sani zubar da kwalla.

Ina zaune a wajan na cire nikab ɗina saboda ya ishe ni, ga kuma zafi yayi yawa,
nayi zaman tankwashe kafa sai na hangi wasu bayin Allah maza biyu da wani ɗan yaro sanye cikin kayan makaranta suma suna zaune kamar yadda waɗan cen suke zaune dalilin daya sa na nufi wajan shine naga wani yana musu laɓe a bayan mota kasancewar murfin bayan motar a buɗe yake, dana isa wajan sai naga ya ɗauki waya ta cikin tagar motan yana niyan guduwa nayi saurin tare sa na kama hannun sa ina ihun barawo! barawo!!! barawo!!!! na kama sa wallahi.

Ahmad na tsaye yana kokarin kulle murfin bayan mota ya ɗauki abu sai yaki rufuwa, ya zagaya ya ɗauki wayar sa ba tare da ya buɗe kofar motar ba kawai sai yaji an capke hannayen sa zazzakar muryar da ba zai taɓa mantawa da ita ba yaji ta na ihun barawo barawoo na kama shi wallahi ya ɗauki waya kuzo kar ya gudu!!!!!!!!!

Josiah, Nurain da driver su kayi saurin zuwa wajan sai suka ga Ahmad da yarinya sanye cikin kayan makarantar islamiyya, suka wai ga gabas da yamma, kudu da arewa amma babu wani barawo sai ma daɗa furta kalmar take yi har sai da hankulan jama'a ya fara dawowa kan su.

Ahmad ran sa ya baci amma ya daure ya ce,"Idan kin gama ihun barawon ki sake min hannu na"

Cikin sanyin hali irin nawa, na kafe shi da idanu shin kaman na taɓa ganin wannan fuskar amma na kasa tuna ko a ina ne, na kalli mutanen dake kewaye dani suna ta bashi hakuri akan abin da nayi duk dama Allah yasa jama'a ba su taru ba, sai na sake hannun na ɗan yi baya kaɗan da kyar da rawan jiki na furta kalma uku
"Ka yi hakuri" cikin siririyar murya ta mai daɗin sauraro.

Ahmad tun da yarinyar ta soma magana yake ji kamar dai Hadiza ce, ya sani ba zai taɓa mantawa da zazzakar muryar taɓa, kuma ya sani fuskar ta nanan a kwanyar kwakwalwar sa sai dai wannan yarinyar sanye cikin kayan makaranta ta rufe jikin ta ruf bazai iya ganin wata she da ba, duk dama ita ma Hadiza wancen lokacin jikin ta rufe yake ruf kawai mayafin da ta rufe fuskar ta ne ya nuna alamar gashin kan ta, sannan kyakkyawar surar fuskar ta ya bayyana a waje sosai ba kamar na wannan yarinyar ba.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now