ALMAJIRA
EP_16AHMAD POV
Sallamar su Josiah yayi, ya ce su koma ɗayan motar, shi kuma zai biyo su daga baya, da kyar Josiah ya yadda suka tafi suka bar Ahmad ba don sun so hakan ba.Suka raka Nurain har bakin hostel suka ajiye masa kayayyakin sa, shi kuma ya kira abokanan sa suka taya shi shigar da kayan da komai ma....daga bisani ya dawo wajan Yaya Ahmad.
Ahmad yayi shaking hannun sa yana cewa Nurain ka mai da hankali kaga exam zaku fara gobe, 1st position nake so na gani kamar yadda ka saba kana jina.
Nurain ya gyaɗa kai yana murmushi, ya kalle ni yana cewa,"Yaya wannan ma ƴar uwan mu ce? naga kuna ta magana da ita"
Ahmad ya shafa masa kumatu yana cewa,"Yes she is your aunt" oyaaa say Hi to her"
"Ina wuni" Nurain ya gaishe ni sai naji wani abu kamar banbara kwai wai ana gaishe ni, ni ALMAJIRA HADIZA ban an sa ba amma na mayar masa da kwatan kwacin murmushin da ya min sannan nai masa fatan alkhairi daga bisani nayi shiru ina kallon su gwanin ban sha'awa.
Ahmad ya sallami Nurain ya ba shi kuɗin da Daddy yace a bashi, sannan ya raba ma abokanan sa kuɗi suma suna ta murna suna godiya.
Ina nan tsaye naga ya yi parking, Nurain na tsaye yana mun murmushi wanda na rasa shin murmushin miye yake mun daga bisani ya buɗe mun kofa wai na shiga.
Na girgiza kai ina cewa, "Ban taɓa shiga irin wannan motar ba, babu ruwana, kuma ma meyasa ka sallami sauran mutanen?...kila ma ɗan yankan kai ne kaje ka yanka ni"na faɗa ina kara matsawa da baya.
Ranshi bai wani baci ba saboda shi yasan ba manufar sa ba kenan, amma haka ya sake ya ce min "Gidan ku fa zaki kai mu khadija kuma ni ba ɗan yankan kai bane, Ko ina yankan kai zan yanka wanda tamun sata ne ba tare da na sace mata wani abu ba ita ma"
Ya ilahiii!!!!!! ya sake kulle min kai na, hakan ya sa na ce ,"Ni wallahi bana fahimtar maganar ka, ni kam ka tafiyan ka, ka bar ni kawai"
Ya gumtse dariyar sa sai dabara ta faɗo masa Ya ce,"Kin san makarantar nan akwai sojoji masu yi ma mutum bulala"
"Na gyaɗa kai ina cewa "Eh na gan su a bakin kofar shiga makarantar"
"Yawwa to kin tambaye su izini da zaki shigo"
"Aa na girgiza kai, tsoro karara ya bayyana a fuskata, na daure na ce,"Ban tambaya ba" yayi kwafa Ya ce to idan suka kama ki zasu kulle ki a wani ɗakin duhu babu haske kuma za suyi ta jibgar ki so ba a dadi Ina gaya miki, gwara kawai kizo na fitar dake babu wanda zai gane ki"
Ashe Nurain na gefe basu wuce ba, sautin dariyan su kawai muka ji, Yana cewa,"Kai Yaya Ahmad babu kyau fa tsorata mutane"
Ahmad ya galla masa harara ya dafe kan sa Ya ce,"Au baza ku tafi hostel ɗin ku ba sai kun yi laifi ko"
Da gudu Nurain ya kwashe ragowar kayan shi da abokanan sa suka kama hanya suna ta dariyar Hadiza.
Ahmad da Hadiza dai basu jika da dramar da suke yi ba, ni dai Diela ina gefe ina ta kyalkyatan dariya saboda Hadiza dai matsoraciya ce ga sanyin hali irin su ne idan su kayi wani abun sai kaji kamar ka sharara musu mari hahhhhhhhhhh, Amma fa mace ce mai kamar maza saboda tana da kokari sosai wajan ganin ta kwatan ma kanta ƴan ci, Dramar su bata kare ba ni dai ban san ya a kayi ba ganin su nayi sun fito daga cikin mota a daidai kofar gidan su Anna.
Na fito daga cikin motar ina tafiya kamar wacce kwai ya fashe wa a ciki sai naci karo da Baffah yana ta kokarin faskara manya manyan itace guda uku har ya gama ma yana na karshe, na ce mishi,
YOU ARE READING
ALMAJIRA ✔
Ficción GeneralOnce, a young girl wandered the desolate streets, her eyes sunken from the weight of her own misery. Orphaned, with her three year old sister, No family to turn to and no roof to call her own, she was forced to beg for scraps, her dignity slowly wit...