02

197 9 3
                                    

ALMAJIRA
NOBLE WRITERS
©Diela_Writer
Ep_02

_GODIYA_
Ina godiya ga Allah maɗaukakin sarki, Mai kowa da komai, Sarkin da babu kaman sa duk faɗin duniyar nan, Ina kara godewa Allah da ya ara min lokaci kuma ya bani ikon rubuta wannan littafi don faɗakar da al'umma baki ɗaya.

Free page
LABARI DA RUBUTAWA FADILA IBRAHIM

HADIZA'S POV
Wayewar gari da sanyin safiya Hadiza da Sofia suka tashi, sai dai kuma jikin su na ta kyarma, alamar ruwan saman da a kayi ya saukar da sanyi sannan sanyin ya ratsa jikin su yana niyar yi musu illa, gata da karamar yarinya, bugu da kari tana ɗauke da ciki.

Da kyar nike iya ɗaga kai ina kallon masu wuce wa a kan hanya yayin da nike zaune daɓas a kasa Sofia na kwance saman kafata yau bana da kuzarin da zan iya ɗaukar ta har mu tafi filin da mabarata ƴan uwan mu suke bara,....bama iya wannan kaɗai ba zafin da jikin Sofia ya ɗauka tamkar dai kwan dake kunshe cikin makwancin kaza shine babbar matsalar da ta sanya ni tunani haɗe da zubar da kwalla saboda halin da muke ciki.
          
Bara nike yi cikin zazzakar murya ta, Yayin da mun fi awa ɗaya duk muna tsaye gaban ƴan mata masu robobin kosai, awara taliya da wake da manja...amma ko asi bamu samu ba a galabai ce na samu jikin bango na tsugunna haɗe da kunce goyon da nayi ina share wani zufa da yake keto min babu kakkautawa....tagumi na zuba ina takaicin rayuwar da muka tsinci kan mu babu gata ko kaɗan in ban da kaddarar rayuwa kuma dole mu karɓe ta hannu biyu don samun salama a wajan ubangiji domin kuwa shi daya bamu wannan rayuwar shi yafi kowa sanin halin da muke ciki,shiyasa kullin babu abin da nike ambato sai sunan sa don samun sassauci.

Ina kallon kyakkyawar kanwata Sofia wanda a ka bar ni da jagorancin rayuwar ta, hakika wahala ya sa ta dafe hasken fatan mu dama ba ɗaya bane ita ainihin fara ce mai yellow, yanzu kam babu shi ta dafe tsabagen wahala, sai yala yalan gashin kanta dogo wanda nayi mata kitson kalaba sune suka sassauko gadon bayan ta don Allah ya bamu gashi kasancewar mu asalin mu Buzaye ne.
A ka miko ma HADIZA take away na abinci, kamshin shinkafa da jar miya ne ke fitowa daga cikin take away ɗin.

Duk da muna cikin matsanancin yunwa amma hakan bai sa na karɓa da wuri ba, sai ma ɗagowa na yi ina kallon mai miko min abincin wanda tuni ya ajiye min a kasa ya juya ya tafi ganin zan ɓata masa lokaci, suit ne a jikin shi bana iya hango fuskar ta shi sa'annan har ya shiga wata zukekiyar mota, ban hakura ba na bisu da kallo cen naga sun kuma tsayawa wajan mabarata suna raba take away, wanda na gansu makil a bayan wata toyota da alama wanda ya saba raba abinci ne duk ranar juma'a... Na ɗan yi murmushi ina cewa Allah ya saka da alkairi.

Hankali na ya kwanta hakan yasa na buɗe ina hamdala na fara ba ma Sofia taci rabi ta sha ruwa sai da na tabbatar ta koshi kafin na soma ci.....ina gamawa na kunce gefen zani na, na ɗauki naira ɗari biyar daga cikin kuɗin da muka samu jiya, muka tafi da Sofia chemist na siyo mata magani na bata nima na sha na zazzabi muka tafi inuwa muka zauna.

KADUNA STATE
Garin kaduna kamar yadda wasu suka sani gari ne mai yalwan mutane, bariki ana yi masa kirari da garin kazo nazo, Kaduna garin gwamna a turance kuma *Center of learning* Kar kuga laifi na because anan marubuciyar ku tayi wayo....back to business.

Karkashin Gadar kawo kowa yasan akwai mabarata da yawa wanda wasu  daga ciki anan suke matashi su kwanta idan dare yayi...dayawa mafi akasarin mabaratan basu da matsuguni wato dai basu da gidaje na kansu da zasu koma su rintsa, da yawansu sun zo ne daga garuruwa daban daban wasu kuma anan garin kaduna suke, wasu suna da gidajen amma basa komawa saboda suna ganin kamar idan suka bar wajan za a raba kuɗi basanan shiyasa sai su kwana abin har ya zame musu jiki suna yawo da tsummokaran su ba wanka, da yawan su ba alwala bare sallah, kuma babu ilimin addini bare na boko....da wannan rayuwan wasu suke samun ciki kuma su haife shi a wannan wahalar shima ya girma da son kuɗi ya girma yana bara.....wallahi wasu daga cikin su zaku ga babu abin da suka rasa na rayuwa dai dai gwargwardo amma sai kaga sun fito bara, dole dai sai anyi almajiran ci, wasu kuma ba laifin su bane halin rayuwa ne ta jefa su suke yin almajiran ci kamar yadda idan kuka biyo ni zakuji dalilin rubuta ALMAJIRA SABON SALO.

Cikin Kawo akwai wata unguwa mai suna Rafin guza idan ka shiga cen asalin rafin guza akwai tsofin gidaje na ginin laka wanda akalla an jima da gina su a wannan wajen a haka kuma na hango wani matsakaicin gida daga gefe wanda kofar shiga ma babu anyi amfani da kara aka kewaye gidan, tamkar dai muna kauye amma baza a kira wajan da kauye ba tun da suna cikin gari ne, kawai dai gidajen su ne suka tsufa.

Gidan ginin laka ne sosai, Na kutsa kai na shiga ina mai kwaɗa sallama anan na ci karo da ɗakuna guda biyu sai barandar ɗakunan wanda suke kallon yamma, sai ban ɗaki dake gefe an kewaye shi da kara, sannan sai randa na kasa wacce aka binne su manya manya guda uku ko wanne da moɗar ɗiban ruwan...daga gefe kuma ta hanyar ɗakunan anan naga wata karamar bishiyar gwanda wacce kasanta wata randa ce sai tulu, da alama wannan keɓantaccen ruwan shan su ne...tsafta a gidan ba a magana saboda komai kal kal babu alamar yaro a gidan.

Na zuba idanuwa ina son ganin mamallaka gidan, Idanuwa na ne suka min tozali da dattawa guda biyu Mace da Namiji su biyu sun fito reras suna rike da sanda hannu ɗaya Namijin yana musu jagora, ita kuma tana rike da tabarmar kaba a ɗayan hannun nata.

Dattijon mutumin yana sanye cikin shiga ta farin kaya, Dogo ne kuma fari tas kamar balarabe ga wani kwantaccen saje duk da tsufan da yayi , kana iya hango kyau mai sunan kyau a tare da mutumin.
Kayan dake jikin sa sun canja launi daga launin fari zuwa wani kala daban, duk sun tsufa sun sha jiki ga shi sun yayyage...yana rike da wata sanda doguwa wannan sandar ita ce dai ganin sa domin kuwa shi ɗin makaho ne baya gani, ya na ta tafiya yana dogara sandar sa har yazo wajan da langar ruwan su yake hannu yasa yana lalube har ya samu moɗar ɗiban ruwan da karfin sa ya damke ta sannan ya laluba kasa ko zai samu ƴar butan su, da ikon Allah ya ci karo da wata fatattakiyar buta duk ta fashe ta huje a haka ya kama ruwa sannan ya ɗauro alwala ya nufi kofa don zuwa masallaci.

Dattijuwar macen ita ma makauniya ce ba ta gani, fara ce sol kamar dai mijin nata sai dai ita tafi shi haske nesa ba kusa ba, tana da ga shi mai laushi wanda ya sauka har gadon baya.
Tana sanye cikin shiga riga daban zani daban sai wani chukurkuɗaɗɗen hijabi wanda ya yamutse ya tsufa sosai, ba laifi ya rufe mata jiki don ya sauka har kafafuwanta, itama dai sallar magriba ta gabatar...ta zauna tana lazimi.

Ko da ya dawo nan ya iske ta ya zauna shi ma,
Ta ce"*Baffah* sannu da dawowa"

"Yawwa sannunki *Anna* Fatan kin mana addu'a? ya tambaya yana ɗan lankwasa kai alamar yana jiran amsar ta.

"Tayi murmushi wanda ya kara fito da asalin kyawun fuskar ta, lallai ita ɗin kyakkyawa ce ajin farko, Muryar ta mai daɗin sauraro tana cewa,"Kullin ai bana manta wa da burin mu kamar yadda kai ma na san kake daurewa kana yi mana addu'a haka zalika nima na jajirce wajan ganin na koka wa Allah bukatar mu, uhmmm ta ɗan numfasa sannan ta cigaba da cewa,"*Baffah* na san mun ɗau tsahon shekaru a haka kullin muna rokon Allah da ya biya mana bukatar mu, Amma har yanzu shiru, Ina da yakinin wata rana burin mu zai cika,ko rayuwa zata canja mana.

Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce,"Anna kwarin gwiwar ki ita ce take kara kwantar min da hankali, In Sha Allah, Allah bai manta da mu ba kuma muma zamu cigaba da mika masa bukatun mun"

"Allah yayi jagora" Cewar Anna sannan ta buɗe musu samira tuwo ne miyar kuka ta ce,"Muci abinci *Baffah*"

Suka dulmiya hannayen su, bayan sun gabatar da bismillah, suka ɗaura da cin tuwo suna yi suna hira abin su gwanin ban sha'awa dai.

©FADILA IBRAHIM

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now