ALMAJIRA
NOBLE WRITERSFree page
02LABARI DA RUBUTAWA FADILA IBRAHIM
_____________________________________
RAFIN GUZA
KADUNA STATEYau tun safe *Anna* ke faman kwalfe ruwan saman da yake zubo musu ta cikin kuryar ɗaki, tsabagen roof ɗin da a kayi ya tsufa kuma ya ɓuɓɓule ta nan ruwan yake zubowa sosai, duk da bata gani amma tana amfani da basirar ta wajan kwalfe ruwan, yayin da Mijin ta *Baffah* yana taya ta fitar da bokitin da take cikawa, don ma sun matsar da kayayyakin su ta yadda ruwa bazai jika su ba, babu komai a wajan sai fili.
Ruwa sai da suka cika bokiti ɗaya da rabi watarana ma suna kwashe bucket uku....ana ruwa yana zuba su kuma suna aikin kwashewa.
Anna ta ce wash Allah *Baffah* na gaji, *Baffah*ya taimaka mata suka fita daga ɗakin suka zauna a barandar kofar ɗakin nasu, tana cewa "Baffah anya ba zamu koma sana'ar mu ta da ba kuwa, *Baffah ya ɗan kalle ta ya juya bai ce komai ba*, Anna ta cigaba da cewa, "Sana'ar gugar ma yanzu taki ɗaure wa kullin cikin wahala ko ciniki ba'ayi"
*Baffah yayi shiru yana nazari, Yayi gyaran murya kafin ya ce,"Wato Anna bawai bana bukatar shawarar ki bace amma mubi a sannu komai mai wuce wa ne, da ai ba haka muke ba, shekaru ashirin da biyar muka ɗauka a cikin wannan rayuwar kuma babu yanda muka iya, yau idan kai ne gobe ba kai bane....ya ja numfashi sannan ya cigaba da cewa gobe ki shirya mana kayan baran mu sai mu fara fita.
*Anna*
Da kyar ta runtse idanuwan ta zafafan hawaye suka sauko izuwa kuncin ta, ta furta kalmomi uku tana cewa "Allah ya kai mu"
Cikin zuciyar ta kuma sake sake babu wanda ba tayi.Washe gari da sassafe misalin karfe shida na safe sun gama shiryawa, Baffah ya sanya farin kaya chukurkuɗaɗɗen yaɗi ya tsufa ya shamule, yayin da Anna ta zumbula wata doguwar riga a material shima baya da maraba da na Baffah, ta yafa wani shamulallan mayafi tsoho kayan wankakkaku ne kuma an tsaftace su amma a idanun jama'a baza su taɓa lura da wannan tsaftar ba.
Sannan suka rike sandar su tana gaba yana baya da kafa suka taka sunayi suna hira suna kuma bara kafin su isa bakin titin kawo sun samu naira ɗari biyu.Karkashin gaɗar kawo anan suka yaɗa zango minti biyar da zaman su ƴan uwan su mabarata wanda suka gane su, suna ta kawo gaisuwa, abin mamaki suna ta sanar da sauran cewa ga Baffah da Anna sun dawo abin ma su farin ciki sukeyi.
Mabarata da yawa maza da mata babba da yaro, yara yara duk suna ta kawo gaisuwa wa Baffah da Anna a take a wajan wasu masu kuɗi suka tsaya suna son rabar da kuɗi.
Mutumin ya sauko yana cewa waye shugaban ku anan mu bashi sai ya raba muku buɗar bakin wata tsohuwa tace" *Baffah da Anna*"
Sauran ma suka rinka ihu suna cewa a baiwa Baffah don Allah.Wasu daga cikin mabaratan suka ɓata rai mutsamman wani baba tsoho wanda ya haɗa kungiyar sa suna kewaye da shi suna ji suna kallo aka bai wa Baffah kuɗin ya kirga kuɗin dubu ɗari ne sannan sukayi godiya, bayan tafiyar mutanen baffah ya kirga iya mutanen wajan cikin kwarewa da jajircewa akan gaskiyar sa yayi calculating kowa abin da zai samu, sannan ya sanar da su har da wannan baba tsohon da kungiyar sa, Baffah ya fara raba kuɗin kowa na karɓa yana murmushi har yazo kan Baba tsoho ya basu nasu amma suka ki amsa karshe ɗaya daga ciki ya karɓa ya wurga masa a jikin sa sannan yayi masa kashedi da kar ya kara shiga sabgar su idan kuma yaki ji to zai yi dana sani. Duk da baya gani ya tsugunna zai kwashe kuɗin.
Anna ta janyo mijin ta bayan an sanar da shi shi kwashe kuɗin ta zaunar dashi tana bashi hakuri ita dama tasan za'a rina babban dalilin da yasa suka dena fitowa bara kenan, kuma gashi an fara daga yau...taja numfashi.

YOU ARE READING
ALMAJIRA ✔
General FictionOnce, a young girl wandered the desolate streets, her eyes sunken from the weight of her own misery. Orphaned, with her three year old sister, No family to turn to and no roof to call her own, she was forced to beg for scraps, her dignity slowly wit...