ALMAJIRA Sabon Salo
PAID BOOK*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
FREE PAGES
05HADIZA'S POV
Bayan sati huɗu
Tun bayan samun kuɗin nan na dena yawan zuwa bara saboda halin da nake ciki,cikin dake jikina ya kara girma da kyar nake iya goya Sofia, komai ma da kyar nake yi, Wani mai chemist yaga halin da nake ciki ya bani shawaran na siya maganin da masu ciki suke sha idan sunje awo, ya ɗirga min magani kusan kala uku yellow guda biyu da ja guda ɗaya wai na karin jini, kowanne guda talatin ya saka, kullin in sha ɗaya ɗaya har ya kare.Gani nan ɗai ba lafiya gareni ba, yau baya na yamin ciwo, gobe kafata, jibi kai na, gata mara na tayi ta murɗamin kamar yadda maran yake mun lokacin da nake period, kullin addu'a ta Allah ya raba ni da bawan sa ko baiwar sa lafiya ma'ana abin dake cikin ciki na.
Ni dai ina ta fama da zumbula zumbulan kaya, haka nayi amfani da kaɗan daga cikin kuɗin na siya mana suturu dogayen abaya guda bibbiyu irin gumaman nan, sai hijabai har kasa na ɗinka kuda biyu Sofia ma biyu, sai na siya mana atampha biyu na bai wa wani mai shago akan hanya ya ɗinka mana, komai dai na tafiya daidai misali duk dama jiya iyau ne tun da bamu da gidan kwana kullin a waje muke kwana.Na share kwallar da ta zubo min daga cikin kwarmin idanuwa na, ina zaune ni da Sofia kanwa ta wacce ban san lalurar meke damun ta na kafa ba, Tana iya mikewa tsaye amma bata tafiya kuma shekaranta uku har da rabi, Allah ya bata lafiyan kafa.
Yau ma kamar kullin wajan masu abinci na nufa na siyo mana abin karyawa muka koma gefe muka ci muka sha ruwa...muna zaune muna tunanin yadda Allah zaiyi damu...Kawai ihu muka ji hayaniya yayi yawa, mutane daga bayan gari suna haurowa suna guje guje kowa yana neman hanyar ɓuya, Shin meke faruwa ne?
Ɗaga kan da zanyi sai na hangi motocin ƴan kidnappers wanda suke yawan shiga kauyukan dake makota da bakura yau kuma Allah ya basu ikon shigowa gari, harbe harbe kawai suke yi, idan kuma sukayi gamo da mace yarinya shakaf to dama sace ta zasuyi hakan yasa kowacce uwa take ɓoye ɗiyar ta, ayarin mabarata na kutsa kai na shiga muna ta guje guje, cen mun laɓe gefen wani shago muna hutawa.
Da kyar na saɓa Sofia a baya nima zan yi ta kai na, Ji nayi an janyo ni an shigar dani wani shago sannan aka rufe rufff...bana iya ganin komi sai duhu, tsahon awa ɗaya muka ɗauka a wannan shago batare da na san dawa dawaye a ciki ba.
Bamu iya buɗe shagon ba har dare ya farayi haka muna tsoro ko motsin kirki bama yi balle magana chab, to mutuwa muraran, yanzu suna jin motsin mu ko su kona shagon ko su buɗe da karfi su harbe mu, ni dai salati kawai nake yi jikina rawa zuciya ta dukan uku uku, na rasa yanda zan yi, Sofia kuka rarrashin ta nayi tayi muka natsu waje guda.
Haka muka kwana a zaune muna ji ana ta harbe harbe munyi sa'a basu kona shagon da muke ciki ba, da asubahi tsit na ji alamar sun tafi, tsananin duhun shagon karo kawai muke da juna, bamu buɗe ba sai da muka fara jin hanayaniyar mutanen garin suna ta koke koke wannan ne ya bamu damar buɗewa,
Ana buɗewa rana ta hasko idanuwana har dishi dishi nake gani tsabar mun kwana a duhu muka fara fita ɗaya bayan ɗaya, ashe duk mabarata ne suka cika shagon, mutane ne tsiraru sai hayaki daya turbuɗe ko ina garin anyi kone kone, kana tafiya kana cin tuntuɓe da gawar mutum ɗan uwan ka, Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, karancin shekaru na ya kamata ace ina gaban iyaye na ina zuwa makaranta boko da islamiyya amma yau gani a titi ina terere ni da kanwa ta, ba uwa ba uba babu wani mai jagorancin rayuwar mu sai Allah mai kowa da komai.
YOU ARE READING
ALMAJIRA ✔
Narrativa generaleOnce, a young girl wandered the desolate streets, her eyes sunken from the weight of her own misery. Orphaned, with her three year old sister, No family to turn to and no roof to call her own, she was forced to beg for scraps, her dignity slowly wit...