Chapter Three

1.2K 75 1
                                    

____** *GIDAN GANDU* **____
               ❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

*wannan shafin sadaukarwane kwacokam ga,@sumayya yarima,@Aisha dakuma @hajiya,allah yabar kauna ga duk masoyana,hakika ina godiyah sosai*
Bari muga nagaba kuma😀😀😀😀

❤03❤

"Baba kayi hakuri fah dan yayan gidankune suka jawo,lokacin da mukaje kamo manjo dan gidan malam IDI a gidan ya saci mashin din wani saurayi kuma yayi masa duka,naga wannan shegiyar yar takace ta aiko mana arnan yaranta sukayi mana faca faca da ofishinmu,waima dan bata gari ba da kanta tazo ba,dan haka babu inda zamuje,in labiru kuke zance ma,dazu wasu samari suka kawomana kara wai sun nemeshi sun rasa a baking rafi lolacin da suke shan rake dazu,dan haka ku tattara naku ya naku kubar nan wajen tun wuri"
Cikin sanyin jiki na rashin sa'a suka bar wajen,wanda dama shi bashari baiyi magana ba,inda wajen tsara yan matane da bleaching toh ya rufe kofah,amma harkar yan sanda kam,matsoraci ne shi sosai na bugawa a taro.
Fitowa sukayi daga police station suka tari acaba wanda zai kaisu asibitin da aka kwantar da hanifan,nan ma saida akayi ja inja da mai adaidaita sahu kafin ya daukesu,suna cikin tafiyane bashari yagyara zama yafara magana wacce baiyi ba tun sanda aka shiga police station din,
"AI baba umaru in fada maka,mutanennen basuda imani,cewa muka cemusu anyiwa fah yarinya fyade amma ji yanda suke wani nuna halin ko inkula,hmmm abin duka babu sanda"
"Dallah can yimin shiru da fuska kaman ta sabuwar fatalwa,waiku adole yan gayu,duk kun shafa mai kun mele fuska kaman wanda aka bi da dutsin guga,zaka ce wani abin duka babu sanda in anbaka sandan uban me zaka iya idan an baka sandan,akwai abinda ka iya ne banda shegen zuwa wajen yan mata,duk wani dan kudinku anan yake karewa da kuma sayen tsukakkun wanduna"
"Kai baba umaru ku bakwa gane zamani,idan ta ganka baki babu wanka ai babu rabin zance,ai idan ta ga fuskarka fara tas ga kuma wandonka irin sabin gwanjonnan yanzu zakaga ana love wallhi in ba kaiba sai rijiya"
"Kai bashari zaman mu lafiya kayimin shiru anan wajen tammmm"
Shiru kuwa yayi da bakinsa bai sake cewa komaiba har suka iso asibitin da aka basu gadon.
A wajen cashier suka hadu dasu inna larai a tsaye suna jiran layinsu ya iso saboda ganin likata(kasar tamu kenan allah yah ya fiddamu cikin wannan hali).
Kudin wajennasu bai isa ba ,saida baba umaru yaciro guntun sanjinsa kafin aka bawa mai karbar kudin.
Bayan sun samu an basu gadone,baba umaru yah kalli kawu shehu yana mayar masa yanda sukayi da yan sanda a police station dazu,tun bai karisa jin mai ya faruba ya fara masifa saboda tsabar ransa ya baci,
"Hmm dama nasan za'a rina,wai an saci zanin mahaukaciya,duk sun bata yayannan basuda aiki sai jawo magana acikin gari,kowa acikin su bayason laifin dansa toh yanzu wa gari ya waya ,gatanan ina tatura yarinya kwadayi anyi mata aika aika tabar mutane da wahala"
Inna larai ce ta goge idanunta da yacika da hawaye ta dubi kawu shehu cike da masifa tafara magana,
"Kai shehu ya isheka haka,kawai zaka samu mutane da shegiyar masifa,zaka ce wani mun b'ata y'ay'a ,aikai suka iyo kaidin na allah ko kanace bamusan mai kake aikatawa,dama wanda yayi ai sai anyi masa,kuma dama kyan d'a yagaji ubansa,kai suka iyo,dan haka kadaina wani jingina laifin akaina eheee"
Kunyace takama kawu shehu ganin yanda inna larai tafere baki ta masa wankin babban bargo da masifa kaman d'anta gashi dakin Da'aka kwantar dasu da mutane.
Sallama baba umaru yayi musu ganin yanda abin yafara zama na tone tone maimakon zaman jinya,fatan samun lafiya yayi musu yai hanyar gida na fatan allah ya kyauta aransa.
Yana shiga gida inna RAMATU(matar baban SAMEEMAH ,uwar su sameerah )ta tari baba umaru da barka kaman ba itaba,da Mamakin sa yah kalleta saidai ya boye baice komaiba,ruwan sanyi ta kawo masa da shinkafa fara da mai da yaji da akayi da ranar.
Saida yah wanke hannun sa kafin yafara garwaya shinkafar dan dama da yunwa yadawo gidan ,kuma yayi arba da tsautsayin daya faru,dawowa tayi ta samu waje ta zauna tana gyara zaman dan kwalinta,
"Ah dama nace baban su ATIKA,(haka take cemasa),kaman dakai aka tafi da hanifa asibiti koh?"
"Eh dani ne ya akayi?"
"Meyafaru ne acandin?"
"Shiyasa kika tareni da fara'a harda ruwan sanyi da kawo abinci a kwano mai murfi dan kiji labarin abinda yafaru koh?"
"Haba baban atika ya zaka ce haka kuma naga dan ka fadamin ba laifi bane koh"
"A gunki kenan ba,toh bazan fada ba,waiku mai yake damunku ne bakuda aiki sai kowa buri yake yaga wani abu yasamu dan uwansa yadora agaba koh,haka kuke daga ku har y'ay'anku kamar an garwaya an raba"
"Kaga baban atika nifah ba cewa nayi kafara min wani zance na banza da wofi ba,kawai tunda bazaka fada ba shikenan,dadinta ma da su sule kaje,zan tambayesu su fadamin,kuma dama dazu na kara kudi an dad'o maggi na ashirin saika bani kudina na fasa yafewa"
Kade zaninta tayi tana cika kaamar kububuwa ta bar wajen,dan tsabar takaici daya shak'i baba umaru jijjiga kai kawai yayi yana rufe kwanon abincin,dan ji yayi duk abincin ma ya fita a ransa.
(Allah ya shirya matan mu a yanzu,musamman ma kauye koh babban gida wannan matsalar tafi yawa a irin wannan muhallen).
A kofar su larai kuwa kowa yah watse yakama harkar sa sai matan dasuke karkashin inna karima su kadaine a kofar ana maida abinda yafaru ana yada shewa,Hansai ceh matar dan baba umaru na farko manjo wanda yatafi cirani bayan ya saci kudin sarkin noman anguwar tasu ana nemansa,wanda yanzu y'ay'anta biyar  kenan,duk suna gidan suma ana fama dasu.
"Hmm ke kiji sai mukaji abu yafaru kuma?"
Itama wata a gefensu ce ta cafe tareda cewa,
"Naga dama ita ke likawa labirun,yanzu gashinan ai yayi mata aika aika,maganinta"
Wata a can gefece tana bawa danta nono ta kalli MAIRO wanda ita ta gama magsna yanzu,
"Ke mairo yanzu kece mai cewa wani wai allah yakara dan anyiwa Y'arsa fyade?,ai gwara ita dole akayimata naga ke yar ki HAFSA,amai muka ga tanayi akaje aka dawo kuwa ashe cikine da ita,kuka shirya ke da ita da asuba kikaje aka zubar mata ,harda cewa wai shawara ce take damunta"
Kunya ce ta ishi wanda aka kira da mairon wanda tafara masifa cikin borin kunya itama ta fara maidawa wanda tayi maganar da nata laifin,
"Naji dai ina Y'a tace kawai tayi,kuma hakan bazata sake faruwa ba,amma ba'a kama uwata da makocinsu ba a daki ina"
"Ke dan kutumar ubanki mairo mutsaya iyah kan gidannan banda sako gidan kowa,dan wallhi inta hakane kowa bazai ji dadi ba in toza'afara'za'afara"
"Hehe dama in baki yasan mai zaice bai san mai za'a mayar masaba,kan me uwa da wabi duk uban abinda za'a fada a fada ba tsoro nakeba,abin kunyane kowa gaba yabashi anan wajen ba baya ba,dan babu wanda abin kunya bai lullubeshi ba anan wajen,dan haka kawai ayi sha'ani wai na birni ya cuci na kauye".
Ganin abin zai bacine yasa inna karima korar kowa daga dakinnata ,kowa yayi hanyar kofarsa yana maida nasa zancen.
A wajen su sameemah kuwa lokacin da suka dawo daga gidan alhaji Sama'ila har sunyi hanyar gidan kungiyar tasu,ta bada umarnin a nufi hanyar gidan karagiya inda aka kai labiru dazu da safe,mashin din suka k'uza suna sakin hayaki a duk layin dasuka wuce kafin suka yanka cikin gari inda zai kaisu inda yake.
A zaune suka sameshi yana rarraba ido fuskarsa ta kumbura suntum saboda dukan dayasha,mamakine kwance akan fuskarsa daya ga sameemah a wajen,
"Yayah labiru kayi Mamakin ganina ne,nice dai y'ar kanwar taka"
"Amma mai kike a wajennan,ko dagskene da ake cewa kece shugabar yan dabar garinnan?"
"Kwarai kuwa gashi ka tabbatar da kanka,kafin mukai ga nan,ajiye wannan wasan a gefe muyi abinda yatara mu,miyasa ka aikata abinda nake zarginka dashi"
"Makike zargina dashi iyee,kaika jimin yarinyar nan"
Murtuke fuska sameemah tayi kaman ba itace take dariya yanzu ba,wani irin wawan mari ta sauke masa akan fuskar sa saida dungura jini yana fita ta hancinsa,komawa yayi ya gyara zamansa da Mamakin irin naushin daya fito daga hannun nata kamar wani babban majiyin karfine ya dakeshi,
"Yanzu zaka bani amsa koh kuwa,mai ka aikatawa karamar yarinya dazu da safe?"
Karkarwa jikinsa yafara yana rarraba ido ganin abun dagaske ne ba wasaba,
"Iyyeee na'am wai nnnni .........din"
"Oh tambaya kake,kai burgu ku dan taba lafiyarsa na dan minti talatin da alama bayason lafiyar tasa"
"Ahah su tsaya,kiyi hakuri wayyo,dama kullum tana wajena,ina yin hakuri shine har jiya nakasa toh yau dana ganta shine,na saya mata shayi da biredi bayan ta shanye najata shagon ilu dama bai bude ba,na biya bukata ta,shine kawai"
"Mesunan abinda ka aikata kenan?"
Saida yayi dan shiru ganin zata sake zabga masa wani marin yasashi saurin cewa,
"Fyade,fyade sunansa"
"Kowa yaji laifinsa ko baijiba?"
"Eh munji shugaba"
Suka amsa dukkansu a tare,
"Kai arnen dawa dakkomun abinda nasaka kamin dazu nasan yanzu yayi yanda nakeso,cikin sauri kuwa yabar wajen ,bai dade ba sai gashi da wani kwano abinda yake cikinsa yana turiri,
"Kai burgu kucire masa wando yanzunnan"
Aikuwa kaman jira suke cikin kankanin lokaci suka sutale masa wando,tun baisan mai zai faru ba yafara ihu yana rokonta,
"Shshshsshdh,katsaya da ihun tukunna bari nayi maka wani gargadi,idan ka kuskura nayi maka hukunci kaje gida aka tambayeka mai ya faru ka kira sunana.......,hmmm,saina rabaka gabadaya da abinda kayi amfani ka aikata laifin"
Tun bata gama masa gargadin ba,ta juye soyayyan mangyadan da aka dauko daga wuta akan gaban labirun,cikin kankanin lokaci kuwa fatar wajen tafara sutalewa tun daga kasan cibiyarsa har zuwa rabin cinyoyinsa.
Su kansu yarannata saida suka girgiza da hukuncin da sameemah tah aikata,
"Kuje kujefashi a bayan layin unguwarsu inda yan gidan zasu ganshi,uwarsa saitayi jinyarsa tunda ita ke daure masa kan macijin yake wasa da wutsiyar"
        Tabbbnnnnnnn,lallai sameemah!!
Mucigaba dai mutane Nah🤣🤣😂🤣

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
  Kasuwar  Rimi  Kano
Tel:📞 *07038339244*

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

GIDAN GANDUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora