Chapter two

1.6K 81 3
                                    

___** *GIDAN GANDU* **____
               ❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤02❤

Labirune a zaune shida abokansa suna shan rake a baki rafi,kai kace ba abinda ya aikata hankalinsa kwance kaman tsumma a cikin randa,yana cikin zance sai waigawa kawai yayi yaga bakowa a gefensa kamar dama ba zaune suke shida mutane ba,tun kafin yayi magana yaji an toshe masa baki,yayinda wani duka ya jiyarci keyar sa ta baya,daga nan bai sake jin komai ba sai duhi daya lullube ganin sa.
Sun gumarsa sukayi suka sabashi a bayan mashin din daya daga cikinsu sai gidan karangiya.
Zefashi sukayi a kasa kaman kayan wanki yayinda daya daga cikinsu yace,
"Kai baaaba yanzun zamu dabashi kaman yanda shugaba reza tace kokuma kawai mubarshi ta ji dashi"
"Haha nayi dakon kawoshi a banza wallahi saina dan tabashi,dama inajin haushinsa sani ne bakayi ba,shine fah wanda yayi shunemu a wajen yan sanda lokacin da muka sato akuyar hajiya delu zamu babbake mu maida maiko,kasani ai dakyar muka sha,badan shugaba jar wuyah tananan ba da tuni sun tara mana jini da majina"
"Gaskiyarka arnan mazaje,dole mudan mauleshi koh kadanne,dan babu abinda na tsana kaman masu bakaken kayannan(yan sanda) yan banza saikaace cinnaku"
Dariyar yan daba suka sa baki dayansu kafin daya daga cikinsu yasamu daidai duwawun labiru ya narka masa sandar hannunsa,wani wawiyar zabura yayi ya mike yana rarraba ido akan kowane dayansu.
Daya daga cikonsu ne wanda shine ya daki labirun da alama shine shugaba idon sa ya dau kwalli kaman tsohon dan farauta,
"Heeege gama karemu da kallo yau uwarka zaka ci a wajennan dan ma bamusan mai kayi ba,amma tunda ka tabo shugaba yau kataryarka sai tayi jawur a wajen mu"
Yana gama magana ya hau tabkar labiru kaman an aikoshi wajensa.
Saida sukayi masa lilis kafin suka barshi yashe a wajen tareda rufo kofar suka bar wajen.
Basu wane dade su sameemah suna tafiya a hanyaba suka iso gidan alhaji Sama'ila,gidane sannane kowa yasanshi saboda siyasarshi,a bakin kofar get din gidan suka yi parking din mashinansu kafin suka tunkari mai gadin wanda yake zaune akan benci yana jin radio,burgune yafara masa magana cikin gadara,
"Kai dattijo maza shiga gidan ka sanar da mai gidan isowar mu"
Bai ce komai ba sai tashi da yayi ya shiga gidan dan aiwatar da abinda suka sakashi saboda tsira da mutuncinsa,bai dade da shiga kuwa ba saigashi yafito,
"Eh na Shaida masa isowarku yace kushiga daga ciki"
"Shikenan dattijo godiya muke"
A parlorn baki suka sameshi ya baje akan kujera tareda ware cinyoyi yana shan iska,saboda kibar da yayi irin ta yan siyasa,washe bakin nan yayi yana musu barka da zuwa.
Sameemah ceh ta kalleshi tana yatsine fuska bayan ta zauna akan kujerar daya daga cin parlorn,dora kafa daya kan daya tayi kafin tace,
"Kafin a fara komai alhaji hada wannan cinyoyinnaka waje daya tukunna,dan banji dadin zama ba da ganin yanda ka wani ware kafafu kaman mai jiran kaciya ta biyu"
Cikin kunya da kuma dariya irin ta yan duniya ya hade kafafunsa waje daya amma da gani baiji dadin yanda sameemah ta disga shiba a gaban yaranta,saidai babu yanda zaiyi tunda shiyake nema a wajensu.
Maganar abinda yatarasu suka farayi gameda campaign daya ke so suyi masa na mutane,Musamman matasa na birni da kauye,sameemah ceh tayi saurin katseshi tareda cewa,
"Dakata harda kauye kakeson muyi maka ko iya cikin gari,sannan kanason mukula da ta bangaren yan sanda ko kuma ba ruwanmu dasu?"
"Eh kowanne nakeso ayi nidai kawai na samu na hau zabennan shikenan burina yacika"
"Toh sharadinka shine;zaka bada rabin kudi yanzu sauran rabi kuma saika hau zabe,amma idan ka hau zabe ka manta da mu,toh kasani sanda ka sauka a mulki saidai kanemi wani garin ba dai nan ba,dan bana barin bashi ko ranka zaka sayar saika biyani kudina bai dameni ba,sannan idan wani yarona ya shiga hannun hukuma kai ke da alhakin fito dashi ,idan ka yarda da sharruda na,kayiwa burgu magana zai kawo maka takardar saka hannu"
Gilas ta fitar daga jin jakarta ta toshe fuskarta kana ta mike tsaye har ta juya zata fita can kuma ta dawo,
"Am karka manta,inada lawyer wanda ba'a siyansa da kudi,karkayi kokarin wani kuskure,dan ni ba irin sauran yan dabar bane,ku tashi mutafi yara"
Kowa mikewa yayi kaman dama umarninta suke jira,sun zo dadai kofar fitane suka hadu da wani gogygyen dan siyasa da alama yafi alhaji Sama'ila ma matsayi a siyasar.
Tsayawa yayi kaman wani gunki ya tsare sameemah da ido wanda ta bashi hanya tun dazu ya wuce,ganin shiru kaman bashida alamar wucewa ne yasata dagowa dan ganin mai yake kallo haka,wani dan isakan kashe mata ido yayi tareda lashe baki irin na yan duniyar nan,dayake itama shugaba ce a wajen cikin sakanni ta gano mai yake nufi,take kuwa ta mayar masa da martani ta hanyar daga masa girarta ta hagun,
"Kibani numberki idan bazaki damu ba mana"
Ba wani bata lokaci tafara karanto masa yaronsa yana copy akan wayar datake hannunsa,saida suka gama yace,
"Banjin sunan zazzakar kazar ba?"
"In min hadu zakaji abinda yafi suna ma"
"Shikenan idan kinshirya zamuyi waya "
Bata sake cemasa komai ba tafice daga cikin parlorn.
Bayan sun gaisane shida alhaji Sama'ila,sai yayi shiru kaman mai tunani yana ta murmushi shikadai,alhaji Sama'ila ne yakatseshi ta hanyar cewa,
"Amma alhaji BALA naji dadai kuwa harkar da kuka kulla kaida seemah jar wuyah"
"Au Ashe kajimu,gaskiya na samu dami a akala dan dagani zatayi dadin harka sosai"
"Hmm alhaji bala kenan,anya kuwa kadauki dami mai kyau kuwa,karfah ka dauki dan maciji ina........,.."
"Kai kai alhaji Sama'ila menene kuma na wannan maganar,babu abinda yafaru kabar ma wannan zancen muyi abinda yakawo mu kawai".
A wajen fita waje kuwa bayan sun zo hawa mashin,burgune yakalli sameemah da Mamaki abinda yafaru,
"Amma shugaba maganar da kukayi keda wannan alhajin anya ba matsala kuwa"
"Me nake Tunani,ka fara mantani ne,gaskiya yakamata ma na fara  sabon aiki dan ina ganin nayi laushi dayawa tunda har kuke min wannan kallon kaman kuna gaban kannenku mata na gida"
Basu sake cewa komai ba sai burka mashinansu dasukayi kowa ya dale,dan da alamar sun jiyo gargadi da kuma fushi a cikin muryar tata.
Acikin gidan gandu kuwa tun safe ake abu daya har rana ta fara zafi lokacin  daura abinci amma babu alamar zasu daina hayaniyar dasukeyi.
Inna larai kuwa tun ana jiyo muryarta da karfi harta fara dushewa saboda masifah,kawu shehu ne yayi sallama ya dawo daga gona,tun daga wajen kofar gida yakejin masifar da akeyi wanda inda sabo yariga ya saba,saidai daya shigo gidanne yakula da kofar tasa cike take da mutane kaman ana rabon kudi,karo sukayi da baba umaru (baban su sameemah)wanda shikuma gadin makarantar primary anguwar yake wanda antashi kenan ya dawo gidan,
"Ahah shehu yadai kana kallon gaban ka kuwa?"
"Ina kuwa yaya umaru,shigowata kenan amma naga kaman duk matan gidan sun taru a kofar tawa inaga wani abune yafaru"
"Toh ai yakamata a je aji mai yake faruwa ba a tsaya daga baya ba"
Hanyar shiga kofar suka nufa wanda duk matar data kula da tahowarsu sai ta matsa tana kama baki saboda tsabar gulma.
Har suka isa sukayi magana inna larai bakinta bai mutuba sai masifa take idonta yayi fici fici,
"Keeh ba magana ake bane bazakiyi managa ba,ko kukane maganin abinda yafaru,kiyi bayanin menene "
Shiru tayi tana jan majina bayan tsawar da kawu shehu ya daka mata,
"Ina..innnnna dai hanifa ce aka kawomin ita wani tsinannen yayi mata fyade,shine sukuma waennan tanbadaddun matan suke tamini dariya suna yada min magana"
Salati suka farayi tsakanin kawu shehu da baba umaru,
"Toh ina ita yar take?"
"Tana daki a kwance"
"Me kika mata?"
"Bbbbbbabu komai"
"Ba komai kuma,haka kika barta a daki kika fito kina ta masifa kenan,masifarce zata warkar da ita kokuma maganin abinda yafaru?,ai kin fi kowa dabbanci da irin wannan kwakwalwar taki,baku da aiki sai shege kishi da fada,shi kadai kuka iya kawai"
Baba umarune ya rike kawu shehu wanda yake ta zazzagawa larai masifa saboda tsabar ransa yabaci,daki ya wuce yadauko yarinyar wanda jikinta yayi zafi rau saboda Zazzabin daya hau Jikinta.
A hanyar fita suka hadu da mazan gidan guda biyu,da Sule dakuma Bashari wanda dukkansu yayan baba umaru ne,
"Yawwa kai sule bi bayan kawunka shehu ku tafi asibiti ,kai kuma bashari zo mu tafi wajen yan sanda"
Hakan kuwa akayi kawu shehu suka tafi asibiti,wanda ganin zasu tafi yasa inna larai dauko gyalenta tabiyo su har waje,saida baba umaru yasaka baki kafin kawu shehu yabar ta bisu asibitin,saida tayi ta rusa musu ihu tukunna aka barta ta tari mashin tabi bayansu.
A wajen su baba umaru kuwa,saida suka bi layi tukunna suka samu layin yazo kansu,dan sandanne yakalli su baba umaru amma idon sa yafi tsayawa akan bashari da alama yaganeshi,
"Malam muna tsaye amma bakace mana komai ba"
"Eh ina jinka menene yake tafe daku"
Saida suka tsara masa, abinda yake faruwa tas kafin ya yamutsa guska yace,
"Hakikanin gaskiya babu inda zamuje kamo wani dan ya taba wani mutum a gidan gandu,saboda kuma da wani a cikin gidanne ya aikata mukaje kamoshi da kyar zaku bari dan sandan yafito da ransa in ya fito ma to saikun sanja masa kamanni kuwa.
     Toh fah yadai gidan gandu??

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
  Kasuwar  Rimi  Kano
Tel:📞 *07038339244*

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#vote
#like

GIDAN GANDUTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang