HANAN 01.........Free page... By Basmah Er Lele (Oum Azlan)

120 5 2
                                    

Bayan hutun tsawon lokaci, gani na dawo Gare ku dauke da hanan.....hanan kirkirerren labari ne....kuma nae muku alkwarin baza kuyi nadamar kasancewa dani ba @ cikinsa.....

HANAN zamani..........
Page 01....Free page.....

@ fusace ta fincike nikabin fiskan ta ta watsar a gefe, hade da kwaye katon hijab maroon wanda @ kalla ya kay yadi hudu da rabi ta wurga shi kan gadon katakon su da befi wata biyu ba da shigowar shi dakin. Umma, mahaifiyar suce da ta dauki adashe ta ta roki mala audi kafinta dake kofar gdansu ya dauki gadon tan da akay mata jeran daki dashi shekaru ashirin da biyu da suka wuce dashi ta kara masa koda dubu talatin ne yae mata sabon gado...Umman Hanan wannnan gadon nakin kona dauka ba abinda zanyi dashi dan dakyer @ siyeshi dubu goma, kibari kawai ki kara kadan kan dubu talatin din in miki sabon gado ay ba abinda zai gagara ko don mutun cin malam....caraf hamida kanwar HANAN tae yauwa umma to sai kibamu naki musa @ dakin mu ay katifar mu daidae take da taki dik da dae katifar tamu ta cinye amma ay dakin mu zaiyi kyau wlhy....Hanan dake zaune agun dan siririn tsaki kawai taja wanda babu wanda ya jita kuma dama bata isa tae wanda za @ jitan ba hade da meda kanta kan littafin umdatul ahkam din datake karantawa...ajiyar zuciya tae bayan tadawo daga tunanin yanda akay suka mallaki gadon dake dakin, yayin data zauna bakin gadon tana cire safan kafanta dawowar ta kenan daga islamiya...Wannan wace erin rayuwa ce haba...Jarrabawan haihuwan mutum @ erin gdan nan wallahi in kay me karamin kwakwalwa ne sai kayi hauka...ace dan'adam bayida lokacin kanshi, ba abinda ya isa yae na ra'ayinshi. Kana gdan ku gdan ubanka wae saidae ka zauna daga safe har dare ko ina na jikinka @ rufe...in zaka fita ka kawo uban hijab da nikabi harda safa kasa...in kawo gidan ma baka hutaba haka zaka wuni yawo ko @ tsakar gdah da hijab...dinki baka isa kayi na ZAMANI ba, babu dae abu guda daya da mutanen gdannan keyi wanda ke tafiya da zamani....Allah Allah ka rabani da kaddarerren rayuwannan....kome ta tina oho edonta ya ciko da hawaye, @ fili tace toma ina zaka je ka hutan ko aure kayi shima mijin haka zaka taras dashi da nashi wasu sabbin dokoki da kalolin takuran....Sannu da dawowa aunty hanan, muryan hamida kanwar tane yadawo da ita daga tunanin da take tae saurin share hawayen ta, hade da amsa yauwa hamidah ya ciwon cikin nakin??????


KB dake zaune cikin jerin abokan ango dake kewaye da tebur din da aka cike shi dam da kalolin abinchi @ hall din da ake gudunar da dinner din auren abokin su salis ne ya kwashe da dariya.. Bash dake gefensa ya watsa masa harara ganin haka yasa yae saurin cire hulan dake kanshi hade da rufe fiskar shi yana chgba da dariyansa...amma dae kai dan wulakanci nee kb, yanzu meye laifin wannan amaryar da kake dariyan iskancin naka daka saba daka ganta?. Hhhhh bash dan girman Allah wannan mace ce? Salis baya ganine fisabilillahi ya kwaso wannar? Dan Allah @ wani kauyen ya kwasota? Dubi yanda take tfyah ya karisa fada yana chgba da tuntsurewa da wani sabon dariya...ganin dariyan kb yae yawa yasani daga kaina ina kallon amarya da angon da suka shigo rike da hannun juna an saya musu kida slow motion, yayinda DJ nashi aikin na koda su...babu wani abun kushewa a jikin amaryan da kb keta tuntsura ma dariya hasali ma me kyau ce sosai iyanata kyawun gashi tasha adon amare sai murmushi take fiskar nan nata kyallin amarci....harara na dannama kb ina mamakin shi kuma wannan in har yana zagin wannan amaryar yaya mace me kyau take a wurinsa? Daga kaina nae naga bani kadai nake hararan shiba harda kusan abokanensu guda hudu....daya daga cikinsu me sanye da bakar geznar ya danna tsaki hade da fadin dan iska xamu ga taka kalar matan ay insha Allahu yanda kake zagin emmata da matan mutane inka gansu....bash yae caraf ya amsa eh wallahi kam kasan kuma erinsu kb wallahi sai kaga sun auri matan da inka gansu saika tofar da yawu sbdah tsabar muni. Sauran abokanen dik suka amsa da sauri wallahi kuwa bash gskyn ka....murmushi kb yae yana binsu da kallo hade da fadin samari ku kwantar da hankalin ku, indae nine kabir me zamanii billahi macen da zan dauko da niyyan aure sai macen da take da kyau ta cika mace take kuma da matukar kyan da ko kasar lebanon taje billahi sai an daga edo an kalleta, matar da en uwanta mata in sungan ta sai sunji tsananin kishin ta sun ji tamkar sukam @ maza aka halicce su....matan da dik wani namiji ko yau uwarsa ta haifeshi in ta rankwafo kansa sai ya girgiza edo...ran bikina kuwa kaf fadin kasar nan sai sun sani kuma sun shaida yau bikina ake. Ku rubuta ku ajiye na fada muku.....Hmnnn lallay kb ka debo da zafi...

Asalin su........

HANAN.....Where stories live. Discover now