HANAN zamani page 02, free page.......by Basmah Er lele....✍
Asalinsu......
MALAM muhammadu dattijon arziki kuma malamine babba @ karamar hukumar dukku dake garin gombe, yanada matan aure guda biyu...uwargdansa goggo ladi auren dangi sukay, shekaran su kusan goma da aure amma Allah bai basu haihuwa, @ lokacin abokin sa malam rabe yamar tayin auren kanwarsa fatsime da mijinta ya rasu bayan ta haifa mar tagwaye maza, tsohon mijinta be jima da rasuwa ba kuwa, suma tagwaye Allah ya karbi abunsa zazzabin dare daya....malam muhammadu be ki tayin abokin sa ba kuwa ya nemi auren fatsime bafulatana me kyau asalin kyan fulani da kunya, ba jimawa kuwa akasha biki amarya ta tare gdanta....zaman lfyh sosai suke da uwargdansa goggo kasancewar fatsime yarinya ce me ladabi da biyeyya.. Shekara na zagayowa ta haifa mishi santalelen yaro da ya dauko iyayenshi wajen kyau, ran suna yaro yachi sunan kakanshi SALISU.. shekara biyu da yayen Salisu ta haifi kaninshi Abubakarr, daga shi kuma ta kay akalla shekara biyar kafin ta haifi autarta mace aminatu....gaba daya yaran malam uku ne kasancewar Allah be bashi rabon a wurin goggo ba sai a wurin fatsime itama uku kacal Allah ya bata...karaf cikinsu salisu babba shi ya dauko malam a komai da komai domin har goggo magajin malam take kiranshi...Allah yasa mishi tsoron sa, kawaici, nutsuwa, kaifin tunani da kaunar Qur'ani da kuma sauran littatafan addini....kafin ya shekara goma yayi sauka, kafin ya rufa sha biyar kuwa ya haddace Qura'ani kaf dinsa da littatafae masu dinbim yawa...@ lokacin samartakan sa kuwa yazama babban Malami sosai. sunan magajin malam ko ya bishi....shima abubakar kaninsa yana nashi iya karatun haka Aminatu kafin ma tae aure ta haddace Qur'ani da sauran littatafae...shi Abubakar ya dage sosai da karatun boko shiko magajin malam zallan arabic dinne agabanshi sai ko kasuwanci....mutum ne mae akidar sunnah sosai da tsoron Allah, yanada matukar tsantseni da bin dokokin Allah tamkar dae mahaifinsa...shekaran shi ishirin da biyar yaje sarin kaya kano @ nan ya hadu da khadija, mahaifinta balarabene, mahaifiyar ta shuwa arab...ko ba @ fadi ba kunsan kyakkyawa ce masha Allahu... basu shekara da haduwa sukay aure irin na mutunci da tsarin addinin islama... basu dade da aure ba Allah yama malam rasuwa....@ lokacin abubakar na kusan shekarar karshe a jami'ah..shi kuma magajin malam dakyer ma ya kammala secondary ya tsaya @ haka yayinda aminatu tae aure @ kano...bayan rasuwan malam gaba daya almajiran sa suka dawo karkashin magajin malam...daya tashi auro khadija sai ya kama haya @ gombe ya zauna ganin ya daukota a birni kar ya kayta kauye ga rashin wuta da ruwa lokacin...basu dade da dawowa gombe ba sunan magajin malam ya kewaye gari yazama babban malami sosai yanda indae kace sheik sadis magajin malam koda karamin yarone to ya sanshi....malam yayi dace da mace mae ladabi da tsoron Allah, shekaran su biyu da aure suka haifi diyar su ta fari HANAN, Bayan shekara biyu suka haifi HAMIDA, bayan shekara uku aka haifi muhammad takwaran malam...sai auta usman affan....iya yara hudun nan Allah yabama malam...yarane da dik wanda ya daga edo ya kallesu sai ya sake kallon su sbdh farin fata da kyawu da Allah ya basu..gdan farare ko gdan kyawawa lakabin da akema gdansu...kaf cikinsu kuma babu wanda Allah ya azurta da kyan HANAN....hanan me kyauce, doguwa sosai, me kira, kira erin wanda matan ZAMANIN nan ke mutuwar samu...gaba tudu baya tudu, tanada kyawawan edanu masu balain daukar hankali @ doguwar fuska mae dauke da dogon hanchi..hanan dae kyanta tamkar wata matar novel komi perfect...gdan malam gdane daya gina shi bisa tarbiyan islama...dik da erin tarbiya da sa edo da yayi akan yaransa...daga shi har mahaifiyar su umman hanan sai suka zubama hanan edo sbdah ganin yanda Allah ya halicceta.. gata da surar da zaiyi saurin jefa me shi halaka...mussaman @ wannan ZAMANIN...baya ga haka tun tasowar ta suka fahimchi macece mai son enjoyment da dik wani kyale kyale da ado na zamani....saidae ganin hakan da sukayi yasa sukayi tsayin daka sosai akan tarbiyanta fiye da dik yanda dan'adam ke tunanin....ga dae kanwar ta hamida etama masha Allahu dik da dae bata kay hanan ba...amma ita sam kyale kyalen duniya baya gabanta kamar iyayenta...Malam da umman HANAN sunyi nasara domin kuwa dole dole hanan ta sama kanta hakuri da sabo da kalan gdansu....ta nada ilimi sosai da kaifin hadda sbdh yanda malam yae tsaye akan karatun su musamman na addini....jan edo da takura da mummunan hukunci ma baka isa abaka karatu baka kay ba ko @ islamiya da take kofar gdansu wanda wani attajiri ya bude ya dankata @ hannun sheikh salis....karatun alqur'ani kuwa da kanshi yake basu kullum da asubahi, da kuma bayan magriba...da ka shiga gdan malam kasan baka shiga gdan kudi ba sai rufin asiri kawai da Alhamdulillah na musulunci..Iyalensa kuwa kullum gwanin sha'awa sbdh ruf ruf zakagan su ko @ ina kuwa daga sama har kasa. Ko gidan malam kazo kasancewar umman HANAN nada injin markade wanda mata ne kawai ke shigowa gdan sai kuma kananan yara zaka ga su HANAN sanye da hijab iya guiwa....@ waje kuwa ita hanan harta nikab me barin ido a bude malan be yarda tayi amfani da shiba sai dae ta rufe ko inanta....makarantan boko ma sunci darajan bappan su abububakar da yayi karatun yasan darajan sa ya sanya shi matsama malan sosai har ya yarda yasanya su @ jibwis anan ta kare secondary school. Har yanzu da HANAN ta kay 19 yrz chan kasan zuciyar ta kullum cike take da kunci da takaicin erin gdan da Allah ya halicceto ta ciki....@ wurin kawayenta na makaranta take ganin hausa novels @ nan ta koyi karantawa...daga lokacin data fara karance karance @ boye wani sa'in ma cikin Qur'ani take boyewa ta karanta domin bata isa koda hamida ta gani ba balle umma bare malam yaji labari saidae wani ba ita...daga lokacin ta sanya ma xuciyar ta kaunar rayuwar karya, rayuwar ado, rayuwar enchi....inta fita waje zata islamiya kuwa taga sa'anninta da gyale wayyo Allah har kwalla take sbdh tsabar yanda takeson rayuwar enchi...kullum mafarki ko tunaninta ita kuma yaushe zata rayu daidae da ZAMANI ba erin rayuwar kauyanchi da takura erin na gdansu ba....wani boyeyyen buri ko nace mafarkin HANAN shine auren namiji dogo, fari, me saje, me pink lips, me faffadan kirji, namiji dae erin mazan d kullum ake kawatawa @ novel...tun ba tafi 11yrz ba take da wannan burin wanda ke boye can kasan ranta babu wani wanda yasani..domin batada kawa ko daya da zatace dey are close...sam malan be yarda da wannan ba..bata zuwa wurin kawa babu wacce ke zuwa wurinta..iyaka wadanda take haduwa dasu @ makaranta su aramata novel....wannan kenan.Kabiru Hashim....(KB me zamani) sunan matashin dan kimanin shekara 31 kanuri...kb dan babban gdah ta fannin dukiya da kuma jama'ah...Mahaifinshi Alhaji Hashim Jada babban dan kasuwane da ke yawo kullum kasashen ketare... gdansa na kano inda matansa biyu suke, uwargdan yaranta takwas, Sadiq, Salim, Kb, Habib, Salma, Salima, Safiyyah, Meenal auta...Amaryan shi nada ya'ya hudu...Heedayah, Haifa, Jabir, Umar... tamfatsetsen gdah ya shirya bangare bangare, ba kuma iyalensa bane kadai a ciki harda kannensa biyu da matansu da yaransu....babu wani hadin kay ko son juna a tsakaninsu kowa sabgan sa yake..gdane na en boko dik abnda kaga dama yi kake...kullum gdan cike yake kowani side da hayaniya daban daban...abokanen yaransu maza d mata kullum suna cike a gdan...wasunsu farare wasu bakake..wasu sun dauko iyaye mata wasu maza...Alhaji hashim jada be cika zama @ nan kano ba cikin iyalensa kullum yana hanyan neman kudi a cewarsa su yake ma wahalan @ ZAMANIN yanzu in bakada kudi kay wulakantacce...Hajiya Aysha mahaifiyar su kb kuma uwar gdan Alh hashim jadah bafulatace...@ cikin yaranta kb kwata kwata beyi kama da etah ba...da babanshi yake kama hashim jadah...kb dogone, baki sosae me bakin labba wanda inka ganshi karon farko zakace yana shan sigari.. yanada kananan edanu kullum kaganshi kaman me jin bacci daga kasa ya ajiye dogo kuma siririn gemu...shima kamar babanshi ya yarda da zafin nema sosae dan bayan kammala karatun shi na masters wanda a bangaren kasuwan cin yayi..ya fada harkan business din with two hands...sauran en'uwansa na ciki daya yawanci sunfi kama da mamansu...kaman habib kaninsa wanda ya biyo masa masha Allahu....kungan shi? Tamkar mijin novel...farina erin farin fulani me kyau. Dogo me kyawun fiska dana edo ga saje me kyau daya hadu da meshi dan gaye dan kuwa habib dan gayene sosai me son adone....kb nada tarun abokai rututu wanda shi kansa besan adadinsu ba gashi da son fantama da yin abun burgewa....yana balain kaunar yaga ya keta kowa a cikin abokanen sa ko sa'anninsa, sa'annan abunshi yafi na kowa kyau da birgewa...burin shi dik inda ya wuce ayi magana..kuma komi nasa yazama dabanne. Wannan yasa abokanen sa mar lakabi da kb me ZAMANI..mahaifiyar su nada kirki saidae babu abunda ta tsana kaman a takura ma yaranta sbdh haka dik da yanayin gdansu yaranta sun fita daban kasantuwar ubansu ne me kudin familyn kuma taqi jinin taga komin kankantar damuwa @ tattare da danta...a cikin yaranta kabir was her favourite sbdh komai indae za ayi na fantamawa da burgewa zai iya emptying account dinshi....Habib too was her darling son yanda kawayenta da mutane ke sonshi suke yaba kyanshi da gayunshi suna fatan ya nemi auren wasu daga yaransu........
Mu dawo labari....@ hankali zaki fahimchi inda muka dosa.....
Basmah er-lele✍
YOU ARE READING
HANAN.....
Romancehhhhh idan na tashi aure, ba aure erin naku ba zanyi bash, ba mata erin matayen ku zan aura ba! aure zanyi wanda kaf birnin KANO sai sun san yau ana bikin KB....idan natashi zaben mata kuwa ko kasar Lebanon taje sai ta zama abar kallo wallahi......