*10 December 2022 fita ta Uku daga cikin taskar jerin Gwanon Gajerun labaran da Chubaɗo ke kawo muku duk ƙarshen mako mai taken 👇*
*SILAR KENAN*
mallakar: Zm chubaɗo (fulanii) ✍️
*_Da sunan Allah mai-Rahama maijin ƙai, Salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira annabi muhammad (SAW)_*
*Note*
*MEYE ILLAR gajeran labarine sannan kuma Is a true life story bawai ƙagaggen labari bane, wannan labarin ban rubutashin don ya baku nishaɗi kaɗai ba🙅♀️ A'a Na rubutashi ne don ya zama ayar dazata hankaltar da iyaye mata akan su zage damtse wajen sanin irin ƙawayen da ƴaƴansu ke mu'amala dasu ne*
Page: 1 to End
KANO STATE (jalla babbar Hausa) a cikin Unguwar Ƙoƙi
Tsohuwace ƴar kimanin shekaru 60 Zaune saman tabarma tana mirzar gyara mai gishiri, sanye take cikin riga da zani na atamfa kanta ɗaure da ɗankwali mara nauyi, daga inda take zaune ta ɗaga murya tace," ke Zuriya maza fito ki sauke wannan ruwan da kika ɗora tun kafin itacen ya gama ƙonewa."
Daga can cikin ɗaki Zuriya ta amsa da " to Inna ina zuwa. Assignment ɗina nake so in ƙarasa tukunna." cewar zuriya wadda ke kwance a saman gadon Bonon Inna tana riƙe da wayarta mai sauƙin kuɗi.
Lumshe idanunta tayi sannan ta buɗe akan screen ɗin wayar, idonta ne ya sauka akan group ɗinsu ita da abokananta na makaranta taga sun tara messages dayawa, hakan yasa ta shiga cikin group ɗin don ganin abinda ake tattaunawa akai.
Littafin hausa taga an turo guda biyu wanda ke ɗauke da sunan fitattun marubutan Yanar gizo, wanda a turamce ake kira da Online writers.
Sannan ta fara bin hirar da ƙawayen nata keyi tana karantawa.
Ɗan siririn tsaki taja don gabaɗaya ta kasa Fahimtar inda hirar tasu ta dosa, don haka ta kashe Data ɗinta sannam ta sakko daga saman Gadon ta fita tsakar gida inda Inna ke Zaune.
Tana fitowa inna ta tsareta da ido tace,"Daddawar Ɗaka an fito kenan. Keda wannan yarinya inda a gidan Sarauta Saude ta Haifeki wllh da an shiga uku da zaman Ɗaki, Allah dai ya jiƙan Saude da Rahama baiwar Allah, badan ƙasa ta rufi idanunta ba ai data sha fama akanki."
Murmushi kawai Zuriya tayi sannan ta zauna a gefan inna ta ɗora kanta bisa kafaɗunta cikin nuna ƙau tace,"Tunda Mama ƙasa ta rufe nata idanun ai ke gai a tareda ni inna. Duk faman da zata sha dani kema zaki iya wakiltarta a matsayin madadi." cewar Zuriya
"Zamana a tareda ke ba tabbatacce bane ƴar nan, don haka karma ki bari zuciyarki ta amince miki cewa zan iya zame miki madadin Saude duba da yanayin shekaruna. Nidai fatana ɗaya ne a gareki ubangiji ya baki abokin zama na ƙwarai wanda zai iya zame miki madadin Mahaifiyarki." cewar Inna
Turo baki Zuriya tayi kamar zata rushe mata da kuka tace,"Don Allah Inna ki dena yawan Ambatawa kanki mutuwa, wai kinsan yanda nakeji kuwa a duk lokacin da kike gayamin haka kuwa?" zuriya ta faɗi hakan hawaye na kwaranyo mata a saman black beauty face ɗinta.
Murmushi Inna tayi dai-dai lokacin data watsa soyayyiyar gyaɗar dake gabanta a baki tace,"Mutuwa ai ta zama dole musulmi yayi zancenta Zuriya."
Kuka zuriya ta saka bata dena ba har seda Inna ta miƙe ta bar mata tsakar gidan, sannan tai shiru tana sauke Ajiyar zuciya.
Uniformɗinta na makaranta ta kwaso daga ɗaki ta zuba ruwa a bokiti sannan tasa Omo ta wanke su tass sannan ta koma ɗaki. Bata ƙara fitowa ba saida aka kira Sallar magariba sannan suka fito sukayi alwala suka koma ɗaki ita da Inna
A haka Rayuwarsu ke Tafiya kullum cikin tsantseni da godiyar Ubangiji. Mahaifin Zuriya Malam Muhammad Alasunah sana'ar fataucin dabbobi ya keyi daga garin kano zuwa garin Delta. Wannan dalilin yasa bai cika zama a gida ba kullum yana tafe tun bayan mutuwar Mahaifoyar Zuriya, amma kuma duk wani abu da suke buƙata yana sauke nauyinsa daidai gwargwado.