DEEYERNARH chapter 1

2 1 1
                                    


DEEYERNARH

By LATEEFAH IBRAHIM

(MA,EESHERH)
A short and existing true life story
Da sunan Allah Mai rahma Mai jinkai

Godiya ta tabbata na Allah Mai kowa

da komi wannan littafi ne na tunatarwa da Kuma nasiha na
biyayyan iyaye banyi Dan cin mutunci ko zagin kowa ba Allah ya bada ikon amfani da kyawawan
halayyar cikinsa.
Dawowarta daga banki ba jimawa su ihsan suka shigo mummy mummy sukaxo da gudu Kai
Hafiz dagani kar ku karyani ummi ce take mata dariya ta zo suna runhumeta jadda Kinga
mummy ko dariya duka sukayi wayan diyana yadau ringing bakuwar layin dake ta kiranta tagani
Bata daga ba, text ta gani ya shigo kamar haka Assalamualaikum amincin Allah ya tabbata a
Gareki yake abin kaunata Dan Allah ki bani damar yin waya dake.kirane ya shigo sai ta daga da
sallama a bakinta ansawa yayi suna gaisa wa yace mata Dan Allah zan iya sanin sunan ki Dan
bincikena bai nuna min ba introducing din kansa yaci mata nine CEO din kamfanin da kike siyan
Kaya a China Amma ni asalin Dan garin kanone wlh tunda nayimiki standard registration a
kamfanin mu naga passport dinki sai naga kin shiga rai na surutun ne taga ya isheta tace yamata
magana ta WhatsApp aikuwa baifi minti uku ba messages dinshi suka shigo suka fara chatting nidai sunana Farhan Ana kirana da saif ban Taba yin aure ba
kuma wallahi da zaki bani dama zan aureki shuru tayi tace mishi sunana Fateema also known as
diyana nayi aure a shaikaran da ya wuce Amma Allah yayiwa mijina rasuwa yarana biyu mace da
namiji Maryam da sa,eed shuru yayi yace sonki ya wuce tunaninki a Raina inasonki wallahi
Fateema ki amince Dani magana sukayi sosai tace ya Bata lokaci tayi tunani sukayi sallama tanata
murmushi ummi sai kallon ta take Tana murmushi.
WACECE DIYANA
Diyana dai asalin sunanta FATIMA SA'EED ABDULLAHI ya ce Ga malam sa,eed abdullahi , diyana mace ce mai hankali,biyayya da sanin ya kamata mahaifiyar ta Maryam wato ummi yar Nijer ce su hudu ne ita,adda bilki,adda kaltum da kuma kawu karami wato aliyu ummi tana saida kosai Wanda diyana ke talla talakawane masu addini da tarbiya diyana tanayin karatu Boko da Arabiya tanada kanne biyu maimuna da aliyu da yayi uku uthman,zainab da Khadija Wanda duk sunyi aure Malam sa,eed talakane sosai Yana saida goro amma bai hanashi addini ba, malam sa,eed dan jahar Kano ne da matarsa Maryam Amma suna zaune da kaninshi daya da suke uba daya sulaiman da matarsa inna wato halimah yaransu uku hajara,nafisa da yahaya saikuma kannensa mata biyu Inna salamatu da Inna hajara rana daya abba yana kasuwa sai tunanin tanayin rayuwa yake gashi ya rasa Mai zaikai
gida a dafa Ba ciniki

da asuba Inna ta dafa taliyan murji sunaci Abba ya kalleta yace ummin diyana wallahi bansan ya zanyi ba kwata kwata abinda zamuci da Rana Yana neman gagaran mu ummi hankalin tayita kwantar masa abban diyana hakuri zamu ci gaba dayi insha Allah bazai gagari Allah ba a kasuwa rasa ynda zaiyi yasa ya tafi abokinsa ya basa dari biyu Yayi gida ranar harda Naman naira saba'in akaci a Miya washe gari a riban kosan ummi tabawa diyana naira hamsin ta siyo koko sukasha da kosai uku uku albarka Abba take sawa ummi a zuciyarsa ya shirya ya tafi kasuwa su diyana kuma yaune zasu gama neco sai sauri take Dan 9:00 zata shiga exam gashi saura minti ashirin da biyar wanka ta fada sharp sharp ta shirya ta tafi,da isar ta, ta gaida invigilator zata shiga ya daka Mata tsawa karfe nawa yanzu Saida ya shanyata na wajen Rabin awa ta samu tayi Ana fitowa zata fito hassana ta bigeta saitace Hassana kiga kin bugeni ko ki juyo budan bakin Hassana sai cewa tayi me xa,a huge a jikin matsiyaciya kallo jikinki Dan Allah banza ni tsantsanin kayanma nake ta tofar yawu tayi gaba diyana kukane ya kubce Mata taci kukanta gasu mangal sunata rungume rungume da hotuna ta sa jakarta tayi gida tunda su aliyu Basu tashi ba, yanzu Abu yaci tura ko naira Darin da Abba yake kawowa ya gagara ummi wani sarkan ta ta ciro ta dau igiyan sarkan tace Abba ya siyar da kyar ya karba tace ya Kara jarin goro fitan Abba a gida harda hawayensa saboda farin ciki ya nufi inda ake Saida sarakuna aka siya dubu uku Abba Yana zuwa kasuwa zaiyi sarin goro yaga wayam kudi sun zube Amma dayake mutum ne mai tawakkali sai ya danne gashi da kunya yaje yacewa ummi sun zube haka yasa ya rasa inda xaisa kawai ya Fara hawaye wajen malam muhammadu ya tafi akan ya bashi rancen kudi ya canja Sana,a dubu ashirin ya ranta Masa da sharadin sati uku malam sa,eed yaji dadi yaje yayi sarin turarurrukan awu ya Fara siyarwa wasa wasa yana Abu ba cin riba Sai faduwa ga kudi da sauran kayan duka baza Sufi dubu biyar ba tunani yake sosai harda zazzabin kwana uku gashi jibi alkawari zai cika abin duniya ya Masa yawa ya rasa inda xaisa kanshi bayan kwana uku yaje ya samu malam muhammadu ya mishi biyani malam muhammadu yace baisan wannan zance ba ko ya biyashi ko yayi kararsa malam sa,eed ya Rasa mai zai cemishi ya hakura Yayi ta bashi hakuri Yaki magana har takai ga mai unguwa a kaje gun mai unguwa akayi sulhu akan bayan kwana biyu xai biya KO ya biyashi da wani abun malam sa,eed dai shuru yayi Dan yasan indai ba sata ba Ba hanyar da zai samu dayaje gida ya fadawa ummi Kam Sai tunane tunane take tayi akan kar a koresu a Dan karamin gidansu na gado wasu kayan aurenta Dan kunne ta dauko tacewa Abba zata siyarda su abbane ya rufe ido yace a a akan bashi zata siyar da kadaranta bayan ta siyar komai na dakin ta haka sai har kwana uku yayi bayan anje wajen Mai unguwa ne yayi ta fada Sai aka tambayi malam muhammadu Mai yakeso a biyashi dashi a gidan malam sa,eed maganar farko yace zaiyi sadaki da kudin ya basa auren nafisa dago Kai yayi yace bashida iko akanta tunda ubanta Yana Raye washe Baki yayi yace fati fa nan dai Mai unguwa yace yasa biki wata daya a Take malam sa,eed ya shiga rudani Yana bawa Mai unguwa hakuri akan diyana yarinya ce bayan kowa Yayi shuru mai unguwa ya yanke hukuncin bawa malam muhammadu auren diyana a maimakon bashin da ake binsa.haka malam sa,eed ya dawo a rude ya sanar wa ummi tashin hankalin da ba,a samishi Rana kuka ummi tayi sosai bayan dawowan diayana a makaranta zata tafi talla Abba yace mata DIYANA na bada aurenki ga abokina malam muhammadu Nan da wata daya dafe kirji tayi tace Abba aure ihu tasa ta shiga daki wajen ummi tana cewa ummi Ina cikin hayyacina Kuwa miye Abba yake cewa hakuri da kwantar da hankali ummi ta mata haka dai rayuwa ta juyawa diyana ta daina zuwa makarantar islamiyya Boko Kuma tayi neco kawai batayi jamb tunda iyayenta sukace ba hali Kuma necon ma wani me ya dauki nauyin na marasa Hali ya biya mata ,Tana zaune tana ta kuka a zuciyarta tace ko laifi tayiwa Allah ga talauci ga masifa mamarta Sai fada Take mata ke diyana baxakiyi shuru Ba dagowa tayi tana ummi an cuceni a ce sa,ar ubana Zan aura shuru mamarta tayi tace Sai yaushe xaki yadda da kaddara haka ta tashi ta Taya mamarta wankin da take sannan ta gyara gidan tayi sallah a haka dai rayuwa tayi Gaba.
Yau ta kasance biki saura sati uku kawar diyana tayi sallama ta shigo ta sameta tana jefa kosai amarya kinsha kamshin dagowa tayi tana kallon ta daga dogon tunanin da take sannu da zuwa Aisha Bismillah ga tabarma xama sukayi ta tashi ta kawomata ruwa Aisha tace diyana xancen ankone ya kawoni yaushe xamu fidda saura fa 3weeks hawaye diyana ta goge tace kujeku kuwai ki cire duk Wanda ya muku auren farinciki shi ake yiwa shiri.shuru Aisha tayi tace diyana ki kwantar da hankalin ki jikina Yana bani alkhairi ne diyana kallon ta Take Suna Dan hira sama sama har Aisha ta tafi ,shara da wanke wanke tayi xata dibo ruwan wanka su muna suka dawo daga makaranta da ta shirya abinci ta zuba musu tayi tagumi a haka ummi tazo ta sameta ji tayi Kamar tasa ihu Amma ta dake tace diyana taso muyi magana dakin ummi suka shiga ummi tace tunda yanzu biki saura sati uku Zaki daina tallar kosai inyaso zannayin kadan kadan a cikin gida Allah ya miki albarka ameen ta ansa ummi tace tashi kije kici tuwo .wasa wasa biki saura sati daya Yan uwa sun fara zuwa daga garurruwa tunda Yar farice dole suzo diyana Kam Sai kuka da tunani


DEEYANARHWhere stories live. Discover now