BABI NA DAYA

576 16 3
                                    

Wa yasan gobe?

▶1⃣

safiya Abdullahi musa huguma

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Zaune take dirshan bisa carfet din dake mamaye da qaton dakin nata,ta tanqwashe qafafunta yayin data tallafe kumatunta da dukka tafin hannunta,lokaciguda kuma ta zubawa food flask din abincin dake gabanta ido,a zahiri idan ka dubeta zakayi tsammanin flask din take kallo sai dai sam ba haka bane zuciyarta da ruhinta sun lula wata duniya ne ta daban,da yunwa ta shigo gidan saidai sam ta kasa sa koda loma guda ta abincin a bakinta,cikin kwanakin tana cikin wani yanayi wanda ta kirashi da jarraba ko musifa dake tunkaro rayuwarta

Wannan ne karo na hudu a rayuwarta da idaniyarta tayi tozali dashi saidai ya zame mata masifa,tun daga ranar da ta dora idonta akansa wani baqon lamari ya ziyarci zuciyarta da gangar jikinta,zata iya kiran lamarin da zazzafan so wanda ya zamto mata tamkar harara a duhu,dalikinta na fadar haka kuwa shine wanda zuciyarta ke budurin a kansa baisan Allah yayi ruwan halittarta ba a doron duniyar subhana,tayi kukan tayi takaicin yadda zuciyarta tayi mata rashin adalci ta hanyar kamuwa da soyayyar wanda batasan koshi waye ba?,meye sunansa?,a ina yake?,taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta jawo flask din ta bude da niyyar taba wanu abu a ciki kota tsira daga fadan umminta,ilai kuwa tana loma ta biyu taji sallamar ummin tana daga tsaye ta dubeta tace"yanzu fadila tun shigowarki kika damemu da zancan jin yinwu amma kusan aqalla awa guda banga wani abun kirki da kika ci ba?,tadan yamutsa fuska tace wlh ummi da yunwar na shigo amma kinga na kasa ci"ummi tace ,haka dai kika iya kullum kamar wata qanqanuwar yarinya sai anyi fama dake akan cin abinci ko?,yayi miki kyau ai kinsan ulcer dai ba gidanku daya ba bare kice idan ta kamaki zata miki sassauci,tayi dan murmushi tace kiyi haquri ummi insha Allahu yanzu zan kawo miki flask din empty,ummin tadan harareta tace ai jikina kunne ne,fadila tadan qumshe dariyar da keson subuce mata,har takai bakin qofa ta juyo tace"af na manta ki shirya yanzun zaki kaini gidan alh salim kwana biyu su shiru muma shiru"tadan sosa kanta dake a tsefe saidai ta tufke shi da band tace anya ummi zan gane ma gidan?,ungo wannan ja'ira cewar ummi da ta watsa mata daquwa yace"nima in banda abbanku yace in tafi dake zaki maku siyayyar kayan make up da da driver zanyi tafiyata"tayi ko saurin miqewa tace yauwa ummi dama jiya nayi masa zancen kayan,tace ato minti goma ki sameni ina falo ina jiranki,ta amsa tana qoqarin shiga toilet dinta dake manne da bedroom din

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tsaf ta shirya cikin abaya baqa mai sulbi saqar qasar dubai wadda aka mata ado da jajayen dutsina masu sheqi,ta nannade tulin gashinta tayi a cuci dashi sannan tayi rolling da wani dan kyakkyawan jan mayafi,simple make up tayi amma kasancewarta tana da wani sassanyan kyau sai ta fito gwanin sha'awa,ta daura agogo na fata ja sai plate shoe da tasanyawa qafarta mai ja ne mai baqaqen igiyoyi,wayar hannunta kawai ta dauka hade da key din motarta ta sake kallon kanta a madubi,cikin zuciyarta ta qaryata masu cewa abu mai duhu baya giwa baqi kyau,duk da cewa ita din ba baqa bace irin matan nan ne masu launin fata(chaculet colour)wasu kuma suce black beauty,fatarta batayi haske can ba kuma kai tsaye ba zaka kirata baqa ba tamkar irin black american haka yanayinta yake,fadila nada wani irin kyau mai sanyi wanda tashin farko bazaka gama tantance kyawunta sai kuna tare wato qananun kyau ne da ita,ba abu mafi daukan hankali a tare da ita irin qirar jikinta cocacola shape,idanunta manya masu dauke da gazar gazar din gashi wanda hakan ke taka muhimmiyar rawa gun tafiya da zuciya gami da ruhin mazaje da dama,goshinta kam irin qananun Gashinnan ne kwance luf wanda ko tayi dauri basu boyuwa,muryarta a sanyaye take cike da wani sirri wanda idan tayi magana take janye hankalin jama'a da dama,fadila tako ina Allah ya bata zubi da tsari wanda yasanya take burge mutane ba maza kawai ba hatta ga yan uwanta mata ma,sai dai gwanar miskilanci ce,sam magana bata dameta ba,tafi ganewa tayi karance karance maimakon zaman tadi,fadila yanzu haka daliba ce a jami'a bayero kano tana karantar mass com,duk da cewa abbanta yayi mata sha'awar karantar medicine ganin cewa mass com bana mutum ne mara son magana ba amma data nuna masa tafi sha'awar mass com din sai ya barta da zabinta kasancewarsa mutum ne mai sauqin kai,sai ya maida zabin nasa kan 'yar uwarta farida,alh abbas ahmad shine mahaifin fadila dan kasuwane mai rufin asiri,domin Allah ya bashi wadata irin wanda ko wane dan adam ke fatan samu ba abunda aka nema a gidansa a ka rasa,asalinsa bafulatanin bauchi ne,yana sana'ar sai da shaddodi da yadiddika cikin kasuwar kwari,yakan tura babban dansa wasu lokutan china ko india domin shigo da kayan su kuma zuzzuba a shagunansu dake cikin kasuwar,ya auri mahaifiyarsu haj amina a maiduguri cikakkiyar shuwa ce wadda Allah ya qaddari aurensu tun bayan da yayiwa manemanta dintinkau a zuciyarta,anan garin kano suka ci gaba da zama tunda anan kasuwancin nasa yake,haihuwar farko suka sami da namiji inda yaci sunan ahmad,baiyi wani tsawon rai ba Allah ya karbi abinsa,shekara daya tsakani suka sake samun wani yaron aka mayar masa da sunan ahmad din,daganan haihuwar tayi musu dif tamkar aun daina,wanda a tsakanin har amina ta soma fuskantar qananun maganganu irin na dangin miji duk da cewar ba a kusa suke ba,sai bayan shekaru goma Allah ya sake qaddara musu samun wata haihuwar,ta haifi 'yar kyakkyawar budurwa taci sunan fadila,shekara biyu tsakani Allah ya sake kawo wani rabon nan ma mace ta haifa aka sa mata farida,kasancewar fadila mara saurin girma sai suka taso kai daya da farida idan ka gansu zakayi tsammanin twince ne don kamarsu daya saidai farida tafi fadila garin jiki da kuma farar fata,tasowarsu tare yasanya komai daya ake musu hatta makaranta tare aka sanya su,sai da suka shiga jami'a ban bancin course ya raba su,shekara shidda da haihuwarsu umminsu ta sake haihuwar da namiji inda aka sa masa muhammad tun daga lokacin kuma haihuwar ta musu bankwana

Babban wansu ya ahmad yayi aure tuni da matarsa anty hafiza harsun samu albarkar twince duka mata ,rayuwar gidan rayuwa ce mai ban sha'awa cike take da son junansu suka taso girmama juna da qaunar juna,sai dai tsakanin fadila da farida akwai tsokana fada da wasa na tsakanin sakuwa da sakuwa sai dai duk da haka farida na respecting din fadila

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

S.A huguma

WA YASAN GOBE? sai AllahWhere stories live. Discover now