BABI NA BAKWAI

102 2 0
                                    


Wa yasan gobe? Safiyya Abdullahi musa huguma 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 ▶7⃣ Fadila ta juyar da kanta daya barin tace"kaina ke min ciwo"farida ta gefanta ta zauna tace"kinyi dai kuka wanda ya haddasa miki ciwon kai,sis ni 'yar uwarki ce,bai kamata ki dinga boyemin wasu abubuwa da ya kamata ace na sansu ba,yadda nima bana boye miki komai bana boye miki damuwata nake neman shawar warinki akan komai,ko dan tsokanarki da nake ne yasa kikemin kallon am too young?,komai ai da tym dinsa,amma idan kina ganin na takuraki am sorry sister"ta fada tana shirin tashi,sai ta bawa fadila tausayi,farida na sonta sosai,tana damuwa da damuwarta any time,ta riqo hannunta tace"is not lyk dat sister baki takurani ba,I will tell yuh everything,but b4 den bani paracetamol nasha,and kimin alqawarin daga ni sai ke babu maijin wannan sai wanda na amincewa hakan"ta gyada kai tace "I promise sister" To fadila dai sauqi bai samu ba har sai data kwana biyu a kwance tana jinyar jiki da zuciyarta sannan ta samu qwarin jikinta da taimakon farida ta hanyar bata shawarwari da kwantar mata da hankali,ba abinda ke sake daga mata hankali irin lafuzan da suka fito daga bakin abinda tafi so a duniyarta har yau sunqi bacewa daga dodon kunnenta ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Yammacin talata ne wanda ya zamto dukkaninsu suna da abinda za suyi cikin makaranta don haka suka tafi a amota daya suka kuma dawo tare kasancewar lokaci guda kowacce ta gama uzirin da ya kaita,tare sukayi sallama suka shigo suka tadda umminsu a falo ita da muhammad dake gefanta yana ta kumbure kumbure,ta musu sannu da dawowa suma suka mata sannu da gida sannan suka haura samansu kowacce ta nufi dakinta don watsa ruwa,farida ta riga fadila kammalawa har ta sauko ta shiga kitchen ta ciko plate da couscous da vegetable soup wadda ta wadata da hanta,fadila ta sauko sanye da pakistan riga da wando irin shigar farida kenan saidai bambancin colour na fadila dark pink ne na farida kuma light blue Itama kujera ta samu dake kusa da ummin ta zauna,ta dubin sashen da muhammad yake wanda tunda suka dawo ya musu sannu da zuwa bai qara cewa qala ba tace"ummi halan yau akwai abinda ke damun parrot dinki naji yau gidan so silent gwanin dadi ba hayaniya"ummi tace"rabu dashi,haka kawai yazo ya tarar dani ina kallon labarai shi wai dole sai ba canza masa tasha zai kalli qwallo"farida ta kalleshi"meye amfanin t.v din dakinsa"ummi tace"duk yabi ya lalata socket din dake dakinsa wai shi koyon gyara an canza masa wasu ya sake kuncesu to ba sai yaje yayi ta yi ba nidai ba mai takurani ni da falona idan mutum yaji haushi ya tashi ya bani guri"ta fadi hakane don dama ya isheta ta koreahi tun dazun yaqi tafiya,ai kuwa ya tashi ya bar fallon yana shirin sa kuka,fadila ta gimtse dariyar dake son qwace mata don tsakanin ummin da muhammad ba'a shiga tasan kuma nan da anjima shi zata lallabo tace yayi mata tausa,fadila tace"ummi mun hadu da haj barira fa?"ta juyo ta dubeta tace "a'ina?,dama tana gari ne uwar tafiye tafiye?"farida da takai lomar abinci bakinta ta karbi zancan"a danja ummi,danja ta tsayar da mu sai da tasa mukayi parking gefan titi,farida ta qyalqyale da dariya😂 tace"kai matarnan ummi Allah ya zuba mata surutu"ummi ta mata daquwa tace"ungo wannan mamarku ce,da Allah yayi ma ke farida ai da tuni ta zama surukarki"farida ta sake kecewa da dariya😂ta kama haba tace🤔"Allah ya tsare,wai shi abdus-samad ma idan banda abunsa ummi qawata fa rumana yace yqna so amma don ya raina ni yaje ya cewa hajiya ni yakeso,ni bansan ma inda tasan labarin bikimmu ba take tambayata nace mata saura three weeks,ai kauwa har zancan abdus-samad din.ma tayimin wai na dai qishi"ummi tace"ato kunya ma ta isheki" Ummi ta juya ta dubi fadila wadda ta zubawa t.v🖥 ido tayi shiru tana sauraransu ,duk da fadila miskila ce amma ta sake zama so quiet fiye da da,ga wani rama da take dan kumarin da a da take dashi yanzu ya zabge babu shi duk a cikin kwanakin ummin na ankare da ita,abun ya dameta sosai har take sanar da abbansu,ya kwantar mata da hankali ta hanyar cewa"kada ta damu ai dama yawancin 'yammata idam aurensu ya taso gadan gadan hakan na faruwa sai tace amma ai bata ga hakan a gun farida ba yace mata ai kowa da irinshi wani ma qiba yake yi maimakon rama,ummi ta yanke tunaninta tacewa fadila"ki shiga kitchen ki sami abinci ki ci"ta dan noqe kafada "ummi sai anjima"ta bata rai😠 tace"wani anjiman kuma?,kinga tashi ki debo abinci kici tun kafin ranki ya baci"tasan ummi ba wasa don haka a kasalance ta miqe ta nufi kitchen ummi tace mata"ki taho min da kunun aya" Taliya ta zuba da miyar kifi(haka umminsu take gwanar girki shi yasa da wuya kaje gidan ka tadda abinci kala daya a kitchen dinta takanyi kamar kala biyu dai dai yadda zasu iya cinyeshi)kusan sili dai dai fadila ke zara tana ci ummin na kallonta tayi banza da ita,yayin da farida ke mata kallon tausayi😒, Wayar ummi ta soma ruri alamun ana kiranta tasa hannu ta qmsa hadi da yin sallama,"haj maimuna lpy lau........lpy qalau wlh........ah mun gode Allah"fadila dake gefe gabanta ta fadi ta tabbatar kiran daga mahaifiyar Aliyu ne ,ko yaya ta ji wani abu da ya danganci gidansun sai ta shiga fargaba,tana tsoron mai zai biyo baya ne a nan gaba?. Tsinto.muryar ummi tayi tana cewa"yanzu da nufinki haj sai dai naji a gari?ai Aliyu dana ne don zai auri fadila sai na kasa zuwa rakiyar lefansa gidan wasu?ita fadilan ba'a zuwa kaiwa za'a zo kawo nata Wata mummunar faduwar gaba ce ta shigeta,lallai ya tabbata Aliyu nasu ne ita da wata,ji tayi wani daci ya mamaye mata halshenta abincin ya qarasa ficewa a aranta don haka ta zame ta shige kitchen ta maida shi cikin cooler ta rufe,taja plastic din kujerar dake kitchen din wadda sukan ajjiye saboda zaman aiki ta zauna a kai,daganan din tana iya jiyo muryar ummin nata na mata sallama tana cewa"Allah ya kaimu goben,Allah ya nuna ma..........bata qarasa ji ba tayi saurin saka hannunta ta toshe kunnenta qwalla nabin fuskarta😢 ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Washegari gaba daya jikinta a mace yake murus ta kasa fita ko ina tana kwance a daki komai ya cakude mata,har la'asar tayi ummi ta shirya tacewa farida itama ta shirya ta kaita tana jiyo farida na mitar ita fai bazata ba ummi idris kawai ya kaiki,"kinci uwaki ja'irar yarinya to naqi idris din ya kaini ke zaki kaini idan kuma ba zaki ba bani maqullan ni nayi driving din da kaina",haka farida ta shirya babu son ranta suka fita sukabar fadila ita daya a gidan,fitarsu sai taji kamar an qara mata kasalar,kimanin awa guda da tafiyar tasu tajiyo sallama daga bakin falon qasa,ta miqe ta yafa mayafinta ta fito bakin verandar saman benan sani mai gadinsu ne yace"uwar dakina yallabai ne yazo"gabanta yadan fadi saboda wanda zuciyarta ke raya mata shine"wanne yallabai?"ta tambayi malam sani ya saki dariya😃 yace"yallabai Aliyu jan zaki"tayi jim kamar tace baxata ba,sai kuma ta tuna da maganganun da Abbanta yayi mata daran shekaran jiya ta juya ciki tana cewa"kace ya jirani ganinan zuwa"bata wani jima da yin wanka ba don haka body spray ta fesa ta dauki hijabinta ta sanya ta zura slippers din wankanta ta fito,yana cikin sitting room din bakin get,ya dan kashingide akan kujera three sitter waya yake da alamu kuma yana jin dadin wayar don har wani lumshe idanunsa yake,bata ce uffan va ta samu gu ta zauna zamanta da minti biyar ta fuskanci da wadda yake wayar jin zancan wadanda suka tafi kai.lefe da yayi,ya doshi kusa minti ashirin yana wayatsa ba abinda ya shalleshi kamar shi kadai ne a dakin sanann ta jisu suna sallama da juna cike da tsantsar soyayya,wata allurar kishi ce ta soketa ta kauda kanta gefe tayi kamar batasan budurin da yake ba, Bayan ya kashe wayar sai shiru ya baqunci dakin,bakajin motsin komai sai qarar a.c "ke"taji yace,banza ta masa kamar ba da ita yake ba taqi ko da kallon sashinsa,taji ya sake cewa"da ke nake"ta dago ta watsa masa wanu kallo na baka isa ba,bata mai da kanta ba taji yace"baki isa na roqeki ba amma ina baki shawara da umarni kije kice bakya sona,idan ta kama ma zance miki please ko dan nima ki barni in samu peace of mind da wanda nake son aura"sai taji zuciyarta ta karye gaba daya tausayin kanta sai ya kamata lokaci guda,tabbas aliyu baya qaunarta ko qanqani,batasan sanda hawaye ya subuce mata ba,ta sake tabbatarwa da kanta so bala'ine kuma masifane,haqiqa tana cikin jarrabawa mai girma,musamman irin wannan son na SON MASO WANI,sai taji bata da wani zabi da ya wuce ta tashi ta bashi guri,ta miqe tsam ta fice tana lalauben hanya,tabbas ba shakka yau da ita ta zabawa kanta Aliyu ta tabbatar da a yau ta rabu da shi koda sonsa ai zama ajalinta,da kuna zata iya duban mahaifinta ta roqeshi ya janye maganar aurensu da Aliyu da tayi hakan ta jima tana kuka a dakinta sanann daga baya tabi ahawarar da zuciyarta ke bata na ta nemi matemaki mana a cikin lamarinta?,ta wanke fuskarta ta shafa hoda ta zizara kwalliya a idanunta donbta rage musu kodewar da sukayi,after dress ta zira ta dauki key din motarta,tana saukowa taci karo ba daqar leda a falon,bata bi ta kanta ba ta fice,tana bude motar ta ta dannawa mlm sani horn akan ya bude mata qofa sai da tazo saitinsa sannan ta tambayeshi wa ya shigo falo da kaya?"nine yallabai ne yace a kawo miki,inata sallama ma naji ba'a amsa ba sai.........,ta daga masa hannu kawai ta fice Cikin minrina qalilan ta isa gidan ya ahmad saboda gudun da ta tsula anti hafiza na falo ita da biyunta taganta tamakar wadda aka jeho ta zube a kujerar falon tana haki sai kuma qwalla ta fara sintiri a fuskarta,kallo daya anty hafizan tayi mata ta tabbatar ba lafiya ba ta cire yan biyu da suka zube jikin fadilan sunata murnar ganinta ba tare da lura da halin da take ciki ba,ta kiu ra maqociyarta zainab tace ta turo 'yar aikinta ta wuce dasu gidanta tayi baqi Kusa da ita anty hafizan ta zauna ta kamo hannayentabta riqe sannan tace"lpy me ya faru haka?"fadika ta sake fashewa da kuka tana cewa"na shiga uku anty,innalillah,anty zuciyata bata yimin adalci ba ta jefana cikin mawuyacin hali,anty ki taimakamin,me yasa zuciyata ta yimin hka anty?why?why?, Anty hafiza ta dafa kanta tana shafawa tana cewa"calm down ki nutsu ki gayamin meke faruwa?" Tasa bayan hannunta tana share hawayen dake kwararo mata sannan ta saki ajiyar zuciya tace"anty tun kafin na San shi waye zuciyata ta dade da kamuwa da matsananciyar soyayyarsa💘,tun daga lkcn na rasa sukuni a zuciyata kwata kwata,kullum kwanan duniya qaunarsa na qara ninkuwa ne a zuciyata kamar jaraba abun,ina cikin wannan haline muka fara face to face da shi saidai abu na farko da ya fara shiga tsakaninmu fada ne,hakan ya zamana har zuwa lkcn da mahaifin Aliyu salim maitama ya nema masa arena gun abbammu ba tare da nasan shine ba,na shiga matsananciyar damuwa😣 a lokacin da ta bayyana an bada arena ga wani,sai dai sanda nayi tozali da aliyu a matsayin wanda aka bawa ni sai farinciki😊 ya mamaye damuwata Sai dai kuma me?anty ga tarin mamaki na sai kalaman qiyayya suka zamo kalaman farko da na fara samu daga masoyina,kalaman da suka kusa tarwatsa zuciyata💔,qarara aliyu ya nunamin bai qaunata ba nice choice dinsa ba samirah ce muradinsa,meye aibuna naty?wane naqasu nake da ahi wanda ya janyo aliyu ya tsaneni?ban can can ci so bane daga gurinsa bane anty? Aliyu yana sonki zai kuma soki fafila"ta fada tana girgiza kafadarta,kukanta ya tsaya cak sai hawaye dake shatata ta ski baki tana kallon anty hafizan da itama ido ta zuba ma ta tashiga girgiza kai tana cewa"bazai soni ba naty baya kuma sona din ya fada anty da bakinsa fa yace"kada nasan ran wata ran zai soni"anty hafiza tayi saurin tarar numfashinta tace"✋🏻ke da'alla can rabu da shi shike da kansa?WA YASAN GOBE?ai sai allah"ta karyar da kai cike da neman agaji da mafita😧"amma anty haka zamu rayu da shi?rayuwar aurece naty wadda ba yau ko gobe za'a yita a watse ba" anty hafiza tayi murmushi😊 tace"ki kwantar da hankalinki,abu na farko da nake so gareki shine ki miqawa allah lamuranki babu abinda ya gagari allah,abu na biyu ki zamo mai juriya haquri gami da kawaici ki zamo mai controlling din anger dinki ,ni kuma insha 'allah nayi alqawatin doraki akan step na gaba,nayi alqawarin baki shawarwari na gari harsai inda burinki ya gama cika Cikin hikima da dabara ta zauna tana bude mata babi babi na hikima da dabarun zaman tare gamida kwantar mata da hankali har fadila ta ji nutsuwa ta shigeta tace ni anty abinda ke dada tayr min da hankalin ganin yadda nake jin zallar soyayyarsa a zuciyata to shi haka yake jin zallar qiyayyata"tave cool down sister na gaya miki kada ki damu irin wananna ita take fa juyewa wata rana ta zama zazzafar soyayya ke dai ki dinga yiwa soyayyar tasa linzami kada ki bari ya fuskanci akwaita a ranki don kada ya samu jin dadi da sakewa na wulaqantaki harsai lokacin bayyanatan ya yi Daf da sallar magariba yaya ahmad ya dawo bayan sun gaisa yake zolayarta"lpy kuwa amarya nàga tana ta qarewa haka?"tayi murmushin yaqe tace lpy lau yaya"anty hafiźa tayi saurin tare tambayar ta hanyar cewa"abban twince aì kasan fama haka na faruwa ga mutum idan aurensa yazo"ya girgiza kai xikin gamsuwa da bayaninta yace"hakane aure yaqin mata,Allah yasa ayi a sa'a"anty hafiza ta masa amin Bayan isha'i tayi haramar tafiya bayan anty hafiza ta tsareta dole ta sata cin abinci ,antyn ta rakota bakin mota tana sake kwantar mata da hankali fadilan ta dubeta tace"anty unason don Allah ya zama sirei wannan zancan""haba fàfila kada ki damu dake da aysha daya nake daukarku(qanwarta ce aysha)fadila tace anty na gode Tana driving tunani ne fal cikin ranta duk da tana jin ta samu relief sosai cikin ranta,ita kanta mamakin kanta takeyi tasha jin yadda mata 'yan uwanta ke yaba kyau da ajinta👰🏻 bare maza wadanda ita kanta batasan adadin masoyanta na dili da na bòue ba wadanda ke jatumtar sanar da ita da wadanda take musu kwarjini suke batin abuna zuciyarsu,wadanda ke kuka akanta bazata.iya tuna yawansu ba don ita dama Allah bai dora mata kule kulen samari ba amma yau kamar almara sai gata a wata wawakekiyar qofar jarrabawa,ta saki ajiyar zuciya sanda ta iso bakin get din gidan malam sani ya budw mata qofa ta shige ta tsaida motarta bayan ta daidait parking,a gefabta taga motar farida hakan yasa ta gane sun dawo,ta saki doguwar ajiyar zuciya tafito daga motar ta kulle ta tunkari falon nasu

WA YASAN GOBE? sai AllahWhere stories live. Discover now