▶4⃣ Sai da motar ta saitu akan titi sannan tace mata"gidan ya ahmad fa zamu"ok" inji farida,"sister wai me ya faru naga kamar wadda aka biyo a guje?"taja tsaki tace"wani dan rainin hankali ne yaso wulaqantani bai san bana daukan wulaqanci ba"ta bata lbr yadda sukayi da shi akan toshe ma juna hanya da sukayi,me farida kuwa zatayi idan ba dariya ba,"kefa 'yar wulaqanci ce shi yasa ban fiya saki cikin lamarina ba,a yar madaidaiciyar harabar gidan sukayi parking,kai tsaye suka nufi falon gidan,ba kowa cikin falon da alama matar gidan na ciki don haka suka dinga kwada sallama,daga kitchen matar gidan ta fito anty hafiza kenan kyakkyawar bafullatana,tana ganinsu ta saki fara'a😊 cikin barkwanci tace"lallai yau baquntar tamu ce"suka saki dariya😀dukkaninsu suka gaidata cikin girmamawa ta amsa musu cikin kulawa tana tana tambayarsu ummi,suka ce tana lpy tana gaidata,fadila ta zaro packet na chaculet tace gashi injita a baiwa twince,wai ni ina suke nema anty?""tace yau ai ranar school ne suna can amma suna hanya don bala ya tafi dauko su,""na manta wlh"ta fada tana qoqarin kwanciya bisa doguwar kujera"anty hafiza tace"ah ya haka ina murna kuku tazo kuma naga tana neman bin lafiyar kujer?"fadila ta dan murmusa 😊tace " anty yau saidai amin afuwa yau kasala nake ji""na miki"inji anty hafiza,farida dake canza tasha a t.v tace"qyaleta anty muje na canjeta yau tsokano fada tayi sauran kadan taci na jaki badan Allah ya kawoni na ceceta ba""tab wucenan wlh wa ya isa yayi gangancin taba mana ita?😳""fada mata dai anty😏"cewar fadila,suka shige kitchen nan suka barta a falon Gyara kwanciyarta tayi don taji dadin yin tunaninsa,shi wa?,idan bata manta ba A.S mai tama binta tace da ita,A.S mai tama ta shiga maimaita sunan ita da zuciyarta,"to me A.S mai tama take nufi?"A dai duk inda aka zaga farkon sunansa ne,to ahmad ne ko ko abubakar ko abdul?,oho itama bata sani ba,wani murmushi ne ya subuce mata😊 sai tunaninta ya dawo kan abinda ya faru tsakaninta dashi dazun,sassanyan muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunnenta,kyawawan idanunsa yanayin zubinsa da tsarinsa,sai ta tuna sanda ya fito a fusace lokacin data murguda masa baki ta harareshi,nan ma dariya ce ta subuce mata,"lafiya kuwa?"ta tsinci muryar farida na tambayarta,ta hade rai tace"lpy lau me kika gani?"farida ta dan tabe baki tace"hmmm tun dazunfa kike murmushi har da dariya ke kadai kamar wadda ta fara soyayya"da sauri fadila ta kalleta tace"lallai yarinyar ni kikewa wannan titsiyen?to gyada na zama na soye qarewar soyayya"anty hafiza dake zaune saman kujera bata sa baki ba sai yanzu tace"um um yaya fadila wannan fa sign ne na falling in love😜"fadila ta miqe daga kwanciyar tana cewa"kai anty,please kada ki biyewa shirmen farida,ita 'yar sa ido ce komai ta gani idonta na kai,kuma sai ta sanya ma question mark😏",ta gyada kai sannan tace " alright idan tayi wari maji,Allah yasa alkhairi ne""amin amma ba abinda zaiyi wari ma anty",nan gidan suka wuni har 'yan biyu suka dawo suka yini tare da su,suna son yaran sosai ko dan su kadaine jikokin gidan nasu,sai bayan magariba sukayi sallah sukaci abinci har yaya ahmad ya dawo ya tarar da su,bayan sunyi shirin tafiya ne ya ahmad ya baiwa ko wacce 4000 anty hafiza kuma ta basu turarurruka. to daren ranar sam fadila bata samu bacci ba,kusan kwana tayi tunanin A.S maitama,duk da ta danji dadi don aqalla tasan yanzun yasan da fuskarta a duniya,koda bazai iya shaidata ba bare tana tunanin mawuyacine ace yayi saurin manta ta ko dan irin karon da suka yi,har washegari da taje school bai janye motar tasa ba,sun dauki aqalla sati guda a haka sannan taje ta tarar ya cire,a gida tace ne kawai tana tana garage ana duba mata ita ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Cikin wannan yanayin suka soma attachment,ranar laraba aka turasu domin tattaunawa da wani fitaccen dan kasuwa,ita da abokiyar karatunta ne hafsat sai wani ma'aikacin gidan radion khalid da zasu tafi tare qarfe hudu na ranar larabar. cikin yellow din atamfa ta shirya mai zanan blue din qananun taurari,skert ne rafa da riganshi wanda dinkin yayi mata cif a jikinta kamar don ita aka qera atamfar,ta maqala qananun fashion na dutse masu kalan blue,ta daura dan siririn agogo na fata ,qafanta blue din hill shoes ne mai madauri sai mayafi data yafashi a kafada bayan ta soka daurinta wanda ya fito da dogon gashinta ta qasan daurin,jakarta ta dauka 'yar madaidaiciya wadda ake maqaleta a gwiwar hannu ta feshe jikinta da turaren shamsul imarat,shigar ta haska fatarta sosai ta fito dagwas da ita,farida dake nade a tsakiyar gadon fadilan tana charting ta dago ta dubeta"gsky yaya fadila kinyi masifar kyau,tsiyar abun daya da baki kula kowa,sai ance anasonnki kuma ki kama mita bayan laifinki ne saiki yi shiga ta janye hankali kuma kice ba wanda ya isa ya kalaki"banza tayi mata ta dauki wayarta dake kan dressing mirror ta fice,farida ta dan daga murya yadda zata jiyota tace"a dawo lpy antyna Allah ya hadaki da mannau ya biyoki har gida😜"bata dai ce mata ci kanki ba ta wuce dakin ummi don tasan a wannan lkc tana daki tana azkar,daga bakin qofa ta tsaya don ta kusa makara tace"ummi zan tafi""to Allah ya tsare hanya ki kula sosai kuma kuna kammala abinda kukaje yi ki taho gida kada ki yadda kiyi dare a waje"tace insha Allah ummi",acan gidan radion suka hadu,bata shiga ba ta yiwa su Hafsa waya su fito su wuce don a motarta suka tsara za suyi tafiyar,Hafsa na zaune a baya yayin da khalil ya shige gaba,tsaf fadila ta gama karantar manufarsa saidai tayi banza da shi tamkar bata fuskance shi ba,tun zuwanta gidan yake rawar qafa a kanta saidai ya kasa furta mata kamar sauran maza da yawa,tana da wani irin kwarjini ne a idanunsu ita sam baya burgeta,ya fiya surutu shi yasa sam bata son ko aiki ne a hada ta da shi,kamar yanzun ya takura mata sai zuba yake shi ala dole sai ya burgeta,Hafsa na baya tana ta tuntsira dariya 😂don tasan halin kayarta sarai,daqa qarshe c.d plate ta dauka tasa sannan yayi shiru A hankali suke binkwatancen har suka gano gurin,qaton get din gun aka bude musu gu ne a tsare ahankali aka dinga nuna mata inda zata bi har taje inda aka tana da don ajiyar motoci tayi parking suka fito,ta jingina jikin motar tata tana qarewa gun kallo,tamkar ma'aikata gun yake saidai ya tsaru sosai komai neat,khalil ya qarso gunsu bayan yaje yayi tambaya yace muje can sunce mu jirashi yana fitowa,wani dan gune da ka qawatashi da flastic din kujeru da teburinsu kowanne yaja kujera guda ya zauna sun dan dauki mintina har fadila ta soma qosawa da zaman jiran Tun daga nesa da ta hangoshi qirjinta ya hau luguden bugawa,ji tayi tamkar ta tashi ta bar gurinsai kuma taga idan tayi hakan ta bada kanta,don haka sai ta basar ta zarme da bude jakarta ta soma fiddo da kayan aikin da zasu buqata,qashin mayen tutarensa da taji ya mamaye gurin shi ya tabbatar mata da qarasowarsa,sallamarsa ta same tabbayr mata da hakan dukkansu suka amsa saidai ita ta kasa dago ido ta dubeshi ta fake da laluben jaka,ya .iqawa khalil hannu sukayi musabaha hafsat ta gaidashi,sai a sannan ta dago kanta caraf suka hada ido👀 saidai ga mamakinta dauke kansa yayi tamkar bai taba ganinta ba,a hankali ta radawa hafsa"da wa za muyi hirar ne?""gashinan a gabanki a.s maitama "inji hafsat"take taji ta dan rude amma cikin dabara ta gayyato dakiya da nutsuwa ta yafawa kanta,kasancewar Ita ce mai tambayoyin jfsat da khalil na tayata da rubutu dolenta ta jawo kujerarta ta sake matsowa daura da shi ta sanya 'yar qaramar recorder dinta a tsakiyarsu suka sake zama verry close aunyi face to face sosai,wani yanayi ya dinga shiga zuciyarta da gangar jikinta wanda hakan ya haifar mata da kasala,tanason tayi.masa tambaya ta farko saidai ta kasa,har sai da hafsat ta dan dungure sanna tayi ta maza ta dago ta fuskanceshi👀,saidai ga mamakinta hannauensa na harfe ne bisa qirjinsa yana mata wannan salon jallon rainin nasa😏,da fari munason muji ainihin cikaken sunanka,ta fada yayin da ta mayar da dubanta kan radio dinta taga tana nadar sautin yadda ya kamata,shiru taji har yayi yawa ta dago ta sake dubansa a karo na biyu,saia taga ya saki hannunsa ya dauke idonsa daga kanta ya kalli khalil yace"ko zakuyi musayar aiki ita ta ta karbi rubutun kamar ba zata iya aikin ba"khalil ya dan rusuna yave ranka ya dade zata iya haka tsarin aikin yazo"ya kalleta cikin gatsali yace"zaki iya?"batayi qasaaqwiwa ba tave aisai an gwada aknsan na qwarai"ta mayat masa da irin yanayim yadda ya yi mata tambayar,cikin ransa yake jinjina rashin kunyarta tare da fafin nasan maganinki" a zuciyar sa ya fadi hakan Ku biyoni muje......
YOU ARE READING
WA YASAN GOBE? sai Allah
RomanceZAMAN KISHI DA GWAGWARMAYA TSAKANIN MATA HUDU A HANNUN MIJIN DA BA AUREN SOYAYYA SUKAYI BA.