Page 1

35 4 5
                                    

A hankali sautin kukan ta Ke tashi daga cikin dakin da suke ciki, daga jin yanda kukan Ke fita zaka san cewa ba karamin abu bane ya saka ta wannan kunan, irin kukan nan ne mai shiga zuciyar duk wani mutum mai imani. Dakyar ta tsagaita kukan ta dago dara-daran idanunta da suka can za launi zuwa ja ta dubi mahaifiyar ta dake zaune bakin gado cike da tausayi, cikin rauni muryar dake nuna ba tun yanzu abun Ke cizon ranta ba tace " me yasa ummi a koda yaushe mu hausawa muka banbanta da ko wace kabila da al'ada me yasa matan hausawa suke going through a lot of marital problems, mu ba mutane bane da baza a tsaya a dubi raunin mu ba, shin ba zuciya bace a jikin mu da baza a tsaya ayiwa rayuwar auren mu kallo na tsanaki ba. A koda yaushe namiji shine Ke yin dai dai mace kuwa sai dai a bata hakuri koda kuwa yanka naman jikinta akeyi a gidan me yasa meyasa ummi mace bazata ji dadin zaman aure bane, laifi ne dan ka auri bahaushe dan uwanka wlh ummi ko makiyi na bazan tabama sha'awar auren bahaushe ba balle masoyina nima dan anmin dole ne ba yanda na iya " wani irin kuka ne ya Kara kwace mata. Ummi ma hawayen take yi cike da tausayin gudar jininta wannan lamari da girma kuma da wahala yake, ko auren dole tayi sai haka. Gaba daya hausawa sun mai da auren su wani iri, a cikin 100 baifi ka samu 25 bane a cikin matan hausawa Ke jin dadi. Me aka maida ya mace ne? Wannan abun ba tun yanzu ba tun a karon kanta itama yake damun ta tabbas ta fuskanci kalubale kala-kala ko tace har yanzu tana kan fuskanta. Amma ya zasuyi kaddarar suce a haka kuma dole suyi hakuri su runguma,dama rayuwar duniya bata zuwa ma dan adam gaba daya cikin jin dadi.

Daga labulen dakin akayi cikin dakakkiyar muryar sa ya doka sallama ganin yanayin da suke ciki ne ya saka shi murtuke fuska kamar bai san wani abu dariya ba "Ke me kika zo yi yau kuma? Jiya ba kin zo ba yawon na menene kuma?" Ya tambaya yana kallon Suhaima dake durkushe. Cikin sanyin murya tace "Abba kayi hakuri wlh nayi iyakar bakin kokarina amma na kasa dan Allah Abba kar kace na koma gidan Malam Audu wlh nan gaba Abba gawata za'a kawo maka Abba..". Bata karasa ba ya katse ta cikin matsanancin fada "bana son maganar banza suhaima, wlh sai dai a kawo gawarki na miki sallah a mika ki gidan ki na gaskiya, su duk sauran yan uwanki ba hakuri sukeyi ba a nasu gidan auren mahaifiyar ki gata nan itama ba hakurin take ba,to bari na gaya miki wani abu daga ranar da aka daura aure soyayya ta kare sai zaman hakuri. Dan haka bana son wata maganar banza tashi ki bar nan kuma karki sake dawowa nan kusa sai da kwakwkwaran dalili shashashar banza ana nuna miki annabi kina rufe ido toh idan kika kaso auren ki sani baki da gurin zama ke da yaran ki a gidan nan".

Cikin tsananin mutuwar jiki ta mike ta dauki Nana khadeeja dake bacci ta goya handbag dinta ta dauka ta juyo ta kalli ummin su cikin dasashshiyar murya tace "ummi na tafi" ita kadai tasan yanda take tsananin tausayin yaranta mata, kasa dagowa tayi tace "Toh Allah ya tsare ki gaida su Abubakar ". Abba kam dauka Kai yayi ya fice yana mita.

*********

Suhaima Kam rashin sanin abunyi yi ne yasa ta koma gidan ta badan taso hakan ba amma tabbas zata gyara wannan abun zata bashi *damar karshe* idan Kuma yayi wasa da damar ba abunda zai hanata barin gidan sa Koda kuwa Abba kashe ta zaiyi auren ta da Malam Audu ko da kaca aka daura shi sai ya sake ta.
Sai da ta fara shiga makotan su kiran Abubakar da Amina dan tasan zuwa yanzu sun taso daga islamiyya, bude kofar gidan tayi ta shiga da addu'a, wani rauni zuciyar ta tayi abubuwa da yawa na Kara dawo mata a kwakwalwa kamar yanzu ne komai ke faruwa. Tunda daga ranar da babanta ya fara mata maganar auren malam audu har zuwa yanda akayi auren aka rabata da da duk wani farin ciki na rayuwa.

Damar KarsheWhere stories live. Discover now