4

10 2 0
                                    

*Damar Karshe*

*Neeshar*

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

Page 4

Kamar yanda Abba ya fada wata uku kuwa aka saka bayan an gama duk wani abu daya kama ta ayi na neman aure anyi an gama har an saka rana, Abba so yake ya aurar da ita kafin ya daina aikin sa na masinja shi yasa yace a saka bikin wata uku tunda dama malam Audu haya kawai zai kama.
A bangaren Suhaima kuwa yau ciwo gobe lpy gaba daya ta koma kalar tausayi duk ta rame tayi baki tun ummi na bata hakuri har ta gaji tayi shiru sai dai kawai tana taya ta da addu'a, aunty zee dake birnin kebbi ma tazo har tayiwa Abba magana sai dai fadan daya rufe ta dashi yasa tayi shiru akan takaici bata kwana ba ta juya abunta, sai dai yanda taga yar uwarta ya bala'in daga mata hankali sanin halin abban su ne yasa tayi shiru.
Duk wanda yaji wannan hadin auren sai yayi mamaki gashi dai malam Audu ba Kudi ba ballantana ace auren Kudi ake so ayi mata,sanin halin Abba yasa kowa yayi shiru ya zuba masa ido ko yan uwansa na haihuwa ido kawai suka zuba mishi Tunda yace mata karamar kwakwalwa ce da su basu san inda duniya ta sama gaba ba kanin sa kawu Bello dama bashi da bakin cewa komai shi yasa tunda yaji wannan katobarar yaja bakin sa yayi shiru. Matan malam Audu kuwa ko a jikin su tunda kowa shi Ke daukar nauyin kansa toh dan ya Kara aure a gurin su ba wani abu bane itama tazo ta zauna idan zata iya.
Haka aka cigaba da shirin biki ummi ta kwashi dashenta ta bama su Hajara siyan kayan kitchen suma suka hada da nasu kudin suka siya mata abubuwa masu yawa, Abba kuwa dama kayan daki ne nashi acewar sa uwa mace ita ke kayan kitchen. Lokaci na matsowa fargabar Suhaima na karuwa gaba daya ta nema walwalarta ta rasa kullum cikin zullumi da kunci take ga zaman daki daya aure ta kamar amaryar daki.

Bayan sati biyu malam Audu yazo duk da bata jin dadi haka Abba ya tasa keyarta ta fita waje, kamar ko yaushe idan yazo har kasa ta duka ta gaida shi dariya yayi yace "haba amarya dan Allah ki daina cemin baban nan wlh duk sai kisa naji kunya" ita dai takaici ya isheta gashi bata jin dadin jikinta shi kuma sai wata maganar Banza yake gaya mata ko kunya baya ji. Jin tayi shiru yace mata "dama zuwa nayi Naji ko kina da hidimar da zakiyi a biki?" Tace "aa" yace "haba Sai kace auren zaura ai ko makida sai a Kira a rakarkashe na kwana daya a dai san cewa anyi biki" ita dai ba tace komai ba dan duk ta kosa ya tafi, hannu yasa cikin aljihu ya ciro dubu talatin ya bata "gashi kiyi hidimar biki dashi" kin karba yayi sai da ya fara balbaleta da fada kafin ta karba da sauri ta shige ciki. Tsaki kawai yayi ya wuce yana mita "tama san daya akayi na bata dubu talatin din nan da karki karba ki gani idan ban koma da abuna ba". Tana shiga cikin gida parlon ummin su ta shiga ta kai mata kudin ta wuce dakin su.
Bayan kwana biyu Halima ta zo gidan cikin maganar da suke take tambayar ummi ko za'a kawo lefen Suhaima ummi tace "toh ban sani ba abban ku dai baice komai ba akai shi yasa nima ban tambaya ba gudun fada" kankance ido tayi tace "kuturun to me zata saka Idan aka Kai ta gida" Abba da basu san shigowar sa gidan ba yace "uwar ki zata saka kinji nace uwar ki zata saka kinga Halimatu ki fita idona" ya juya ya kalli ummi yace "kin tara yara a gaba kuna zance Banza akan abunda ba wanda ya Isa ya canza shi" caraf ummi tace "Allah zai iya sauya komai kafin wayewar gari" harara ya dalla mata kafin ya kalli su Suhaima dake zaune kansu a kasa yace su tashi su fice kafin ya balla su da gudu suka fita Halima na barin yarta a kasa Sai da ummi ga dauke ta. Tsaki yayi ya shige daki yana mita, ummi kuwa ta fice ta kaiwa Halima yarta dake kuka.
A haka aka shiga watan biki, duk da dai ba wani abu zasuyi ba saboda yanda bikin yazo musu kari kuma da amarya bata da Lpy shi yasa gaba daya bikin baiyi armashi ba, amma dai ba laifi mutane sun zo gida ya cika da dangi da abokan arziki.
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya, yau ta kama asabar kuma yaune mutane suka shaida auren Malam Audu sifawa da matar sa Suhaima Abbas, idan kaga fuskar malam Audu
kamar wanda akayi wa albishir da gidan aljanna baki har kunne sai gaisawa yake da mutane da suke taya sa farin ciki.

Barakalla gida ya cika da yan biki dangi da abokan arziki duk sun zo, ga komai na abinci da abun sha wadace abun sai son barka.
A bangaren amarya kuwa wani zazzabi ne ya rufe ta tun cikin dare har zuwa yanzu dakyar aka samu tayi wanka tasha tea da magani ta saka kaya ta kwanta, dama ita ba kwashe-kwashen kawaye ba sai kawarta guda daya Mastura da suke tun primary suna tare sai kuma Yan Islamiya dinsu da suka zo.

Bayan sallahr isha aka fara shirye shiryen Kai amarya gidan ta. Da lallashi ya Hajara ta saka ta Kara yin wani wankan ta dauko mata atampha dinkin riga da zani ta saka, gaba daya tayi wani sukuku idonta kuwa yayi jajur tun tana kukan fili har ta gaji ta koma na zuci ganin ba sarki sai Allah ta hakura ta koma lallashin kanta da kanta.

Da misalin karfe takwas da rabi aka fito da Suhaima zuwa dakin umma, rungume juna su kayi suna sakin wani marayan kukan daya taba zuciyar duk wanda ke gurin, yan uwanta da suka san dalilin kukan kuma sai sharar hawaye sukeyi cike da tausayin halin da yar uwarsu zata shiga dan kowa yasan halin malam Audu. Ganin ummi ta kasa magana yasa yan uwanta dake gurin fara yiwa suhaima nasiha mai ratsa jiki da kuma bata shawarar daukar kaddara a duk yanda tazowa bawa. Haka dai tana kuka aka fitar da ita daga dakin umma zuwa parlon dake soron gida shima sai nasiha yayi mata tare da gargadi mai karfi akan auren malam Audu daga karshe ya damka mata sadakin ta aka tafi da ita a motar ya Haris.

**********•

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana tunani farkon saka kafarta cikin gidan nan shine mafarin duk wani abu dake dawainiya da ita, duk wata damuwa, kunci, fargaba, rashin samun kwanciyar hankali sai da ta shigo gidan malam Audu tayi arba dasu yanzu gashi har aurenta ya tasarma shekara 4 da yara biyu.

Kitchen ta shiga ta fara kokarin daura masu abincin da zasu ci, tana girki tana sharar hawaye ta rasa dalilin da yasa Abban su ke irin wannan abun gaba daya yaki bata dama ta fadi abunda ke damunta ballanta na yayi kokarin gyara komai ajiyar zuciya ta sauke a karo na ba adadi tana fadin "Allah ka kawo min karshen wannan masifar da nake ciki" eh masifa mana ace ko abincin da zasu ci sai dai ta nema da kanta gaba daya kamar malam Audu bai san wani abu hakkin aure ba.........

✘Ø✘Ø(❁º◡º❁)

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 04, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Damar KarsheWhere stories live. Discover now