2

9 3 0
                                    

*DAMAR KARSHE*

*Neeshar*

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

Page 2

*WAIWAYE*

08-07-1973

Malam Abbas mutum min Bungudu ne karamar hukumar jihar Sokoto, shine babba a gidan sai yan uwan shi mata hudu da autan su namiji, duk aBungudu suke rayuwa sai dai shi a sokoto yake rayuwar sa da iyalinsa gaba daya, mutum ne mai rufin asiri,dan aikin masinja yake yi kuma yana yar buga bugar sa dake Kara kawo masa Kudi. Matar sa daya Hadiza mace mai matukar hakuri da kawaici ga addini da sanin ya kamata. Yaran sa bakwai Haris shine na farko sai usman sai Aliyu Sai Hajara sai zainab sai Suhaima sai autar su Halima. Gaba dayan su sunyi aure a nan sokoto sai Zainab kadai dake aure a kebbi. Mahaifinsu mutun ne mai matukar wuyar sha'ani idan yaso abu ba wanda ya iya ya hanashi aiwatarwa, irin hausawan iyayen nan ne dake daukar abu da muhimmanci especially akan ya mace.
    Yaran sa gaba daya sun taso ne cikin tarbiyar da suka daura su akai, sun samu tarbiyya mai kyau daga mahaifiyar su mai sanyin hali da tausayi mahaifin su kuma tsayayyen uba da ko dariyar sa sai dai a waje. Idan zai shigo cikin gida gyaran murya kawai yake yi zaka ga kowa ya shiga hankalin sa saboda "Senior citizen" kamar yanda suke kiran shi ya shigo
    Matasan yaran sa gaba daya sun kammala karatu ya Haris na aiki a eco bank, usman kuma kasuwanci yake yi kuma Alhamdulillah ana samu dai dai gwargwado, Aliyu kuma malamin makarantar secondary ne shima ba laifi yana da rufin asirin sa. Matan kuwa dama iya secondary school kawai suke gamawa yake musu aure. Haka akidar sa take a cewar sa karatun 'ya mace ba wani fa'ida ne dashi ba cikar mutunci su shine gidan miji.
  A cikin yaran sa Suhaima ce karshen aure dan ko Halima da take auta ta rigata auren, hakan yasa malam Abbas mugun saka mata ido taji gaba daya zaman gidan ya ishete a gurin mahaifiyar su kawai take samun sanyi amma da malam ya shigo take shigewa daki idan ba haka ba ya dinga masifa kenan kamar ya ari baki.  A cikin wannan halin ne abokin mahaifin ta malam Audu yace yana sonta Malam Abbas kuwa yayi murna yayi farin ciki, bayan sallahr magrib ya shigo gidan kamar yanda ya saba fuska ba walwala, bayan ya zauna ummi ta kawo masa ruwa ta ajiye. Kallon ta yayi yace ta Kira masa Suhaima cikin sanyin jiki ta fita dan tasan bazai wuce maganar taki fitar da mijin auren bane zai mata, ita kuwa tana tausayin yarta kuma kullum cikin sakata take a addu'ar ta akan Allah ya mata zabi na gari.
  Bayan sun shigo cikin parlon ta samu guri daga bakin kofa ta zauna kanta a kasa tana tunanin kuma me zai faru yanzu.
    Gyaran murya yayi cikin dakewa ya fara magana "Suhaima" dagowa tayi ta kallesa ya harareta yace "ba kallo na zakiyi ba amsa ni zakiyi" cikin Kara mutuwar jiki tace "na'am abba" Kara gyara zama yayi yace "Tunda kin ki fitar da miji gashi har kanwar ki tayi aure kina nan kin shashanci to ni na zabar miki dan bazai yiwu na zuba miki ido Ina kallo ba kina gwada tsayi damu a cikin gidan nan" wasu hawaye masu zafi suka zubo mata tace "toh Abba" yace "yauwa ba kuma neman shawara nake dake ba ko mahaifiyar ki data daure miki gindi kina zaman gida ai aure shine cikar mutunci ku duk samarin dake zuwa kofar gidan nan bada gaske suke yi ba tunda har yanzu ba wanda ya yunkoro yazo gida hakan yasa na zaba miki miji da kaina kamar yanda addini ya halasta mana, ba kowa bane sai malam Audu abokina".

Cikin razana ummi da Suhaima suka dago Kai suna kallon Abba shi kuwa ko a jikin sa ya cigaba da magana "dan haka zuwa gobe zan masa izinin fara zuwa gurin ki na gama magana zaki iya tafiya". Wani kuka ne ya kwace mata ta mike a guje ta fice daga parlon ummi ta mike zata bita ya watsa mata wani kallo hakan yasa ta koma ta zauna zuciyar ta na suya cikin danne kukan dake son kwace mata itama tace "haba malam, in dai malam Audu baban su Halifa ne ya mata tsufa matan sa fa uku, ya za'ayi ta auri sa'an wanda ya haife ta ai aure lokaci ne dashi idan lokaci yayi Allah zai kawo mata miji dai dai ita ba sai ka dinga tallan ta ba yanda Allah ya kawo ma yan uwanta masu son su itama haka Allah zai kawo mata nata haba amma ace malam audu abokin ka haba malam a kara dubawa dai dan Allah".

Daga mata hannu yayi yace "dakata malama ba wai neman sharawa nake daku ba na gama magana a bani abinci".

Share hawayen da suka zubo mata tayi ta miki jiki a sanyaye ta fice zuwa kitchen.

    Sai karfe 9 ta samu ta shiga dakin da yanzu ya zama mallakin Suhaima kawai, a dunkule ta same ta kwanta saman abin sallah, a hankali takai hannu ta taba goshin ta, firgigit ta mike zaune,sosai zaka hango zallar tashin hankalin dake cikin idonta fita ummi tayi ba jimawa sai gata ta dawo da ruwa a cup da paracetamol ta ajiye sai kuma ta fita ta dawo da plate din tuwo, zama tayi tana kallonta a hankali ta dinga diban abincin tana bata a baki ba musu Suhaima ta dinga karba tana share hawayen dake zubo mata, ba wani da yawa taci ba tace ta koshi,magani ummi ta ballo ta bata tasha cikin sanyin murya ta fara mata magana "Suhaima komai mukaddari ne kin san halin abban ku tunda ya riga ya yaken hukunci ba mai iya canza shi ki cigaba da addu'a Allah baya bacci idan auren ki da malam Audu ba alkairi bane cikin ruwan sanyi Allah zai warware komai Insha Allah bana so ki saka komai a ranki zan Kira yan uwanki gobe idan Allah ya kaimu bana so ki sakawa kanki damuwa ki kwantar da hankalin ki kinji ko?" Cikin sheshekar kuka tace "Insha Allah ummi nagode" tace "yauwa sai da safe karki manta kiyi addu'a" tace "Toh" bayan fitar ummi ta sulale ta kwanta akan sallayar hawaye masu zafi na zubo mata. Sai da akayi sallar asuba ta samu bacci ya dauke ta.
   12pm gaba daya yaran malam Abbas sun hallara sakamakon kiran gaggawa da ummi ta musu da sassafe aunty zee ce kawai babu a ciki saboda ba a kusa take ba. Sanin halin Abban su yasa tace su bari sai 12 kafin nan ya fita sai su zo saboda gudun fitinar sa. Hayaniyar yan uwanta ce ta tashe daga bacci toothbrush dinta ta dauka ta fita bakin pampo taje da dauki buta bayan ta deba ruwa ta shiga bandaki, bata jima ba ta fito tayi shirin wanka gaba daya bayan ta shirya ta fice zuwa parlor. Bayan duk sun gaisa ummi ta mata tayin breakfast ba musu ta dauka ta fara tsakura a hankali kanta a kasa, cikin sanyin murya ummi ta fara musu bayanin abunda yasa ta Kira su ba matan ba har mazan sai da suka razana cikin tsananin tashin hankali Hajara tace "haba ummi haba wannan wane irin hadi ne? wai sai yaushe ne Abba zai daina abunda yake yi" caraf Aliyu yace "gaskiya ummi bazai yiwu ba haba dududu shekarar Suhaima nawa da za'a hadata da malam Audu Ina ma laifin ace Halifa Ke neman ta amma malam Audu ko kunya babu" tagumi ummi tayi tana sauraron korafin kowa Halima dake kuka tace "dan Allah ummi wannan karon kar kiyi shiru a cuci ya Suhaima dan Allah wannan sayin halin naki ne Ke sa abba na Kara yin abunda yaso da rayuwar mu ya hanamu cigaba da karatu da ace yanzu mazan mu basu bari mun koma ba ya zamuyi duk da dai aunty zee bata cigaba ba sai dai Allah ya azurta mijin ta ba abunda ta nema ta rasa amma ya Suhaima fa Wlh ko abinci gidan malam Audu wahala yake yi" ita dai Suhaima kanta na kasa tana wasa da spoon din hannun ta hawaye kuwa kamar an bude pampo. Dogon numfashi ummi taja tace "toh kun dai san halin mahaifin ku Nima haka nake hakuri dashi Amma abunda nafi so daga gare ku shine ku taya yar uwarku da addu'a Allah ya mata zabin daya fi alkairi". Suka ce Ameen kafin suka cigaba da tattaunawa akan maganar dan ba karamin daga musu hankali maganar tayi ba.

✘Ø✘Ø(❁º◡º❁)

Damar KarsheWhere stories live. Discover now