*NDAIGOL AM*
( _Haihuwata_)By
Sadeey09139216255
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI,YA ALLAH KASA YADDA NA FARA LITTAFINNAN LAFIYA KASA NA GAMASHI LAFIYA.*
*WANNA LABARIN BA KIRKIRERRE BANE ,TRUE LAFE STORY NE*
*☀️ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION🖇️*
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
_MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA, HUMM WANI ABUN SAI ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION👊🏾🦋 RUWA KAƊAI KE MAGANIN ƘISHI☀️_
*"ALƘALAMINMU YANCINMU⚔️*
Page 1️⃣-2️⃣
---- Zaune yake akan d'aya daga cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun da ke cikin k'awataccen parlour Wanda ya kawatu kuma ya had'u,mai zaman mutum biyu,
A zahiri TV yake kallo sai dai a badini kuma ba TV yake kallo ba, zaka lura da hakan ne idàn ka karanceshi domin ko kefta ido bayayi saboda nisan da yayi a wata duniya wacce babu ranar da Allah zai wayi gari ba tare ya Yaje ba,
Tunani yakeyi na mamaki tsawon shekarun da aka kwashe ana dauke kudinsa ta account duk da irin matakan tsaron daya sawa bank account dinsa amma yasan every Monday sai ancire masa makudan kudade wadanda har ila yau ya rasa daga ina matsalan take, shin daga shine? Ko kuwa na bank dinne?
Macece wacce a kallah ba za ta haura 45 ba ta shigo palourn bakinta d'auke da guntuwar sallama,ganinsa a haka yasa ta yin wata shegiyar murmushi mai d'auke da tarun ma'anini Wanda ita kadai ta sani.
Karan ajiye tray d'in data shigo dashi mai d'auke da 2 cups sai just and water ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin d'aya tafi,
Kallonsa tayi kana tace "har dai ila yau ka na kan wannan banzan tunanin naka ko? Hmm tukunna ma,kana ta juya ta fita abunta,
Numfashi ya sauke kana ya d'auki bottle water ya ballen marfin ba tare da ya juye a cup ba kawai ya kafa kai ya hau sha.
Zaune suke parlourn yayin da kowa ke abunda yakeyi,
Maza biyu ne sai mace d'aya,
Namiji kuda d'aya Wanda a kallah Shekarunsa zasu kai 30 mai suna fahad, daga ganinsa za ka san lallai tarbiya da mutunci basu samu gurbin zama a wajen shi ba, duba irin askin dake kanshi,
zaune yake a kan 1str shisha ne a hannunsa yana sha kaman Wanda ya samu abunda yake so don har wani lumshe ido yakeyi,Sai mai bi Wanda ba zai haura 27 ba mai suna Ameen shima dai kaman na fahad ne duba da kayan jikinsa da kuma askin Dadan dake kanshi,
shi kuma waya ne a hannunsa kiran iPhone 11 pro,yanata aiki akanta Wanda daga motse-motsen da yakeyi zaka San ba abun arziki yake aikatawa a ciki ba,Sai kekkyawar budurwar wacce ba za ta wuce 25 ba ita ma dai wayar ce a hannuta tana chart a ciki,a yayin da kekkyawar fuskarta ke dauke da sihirtaccen murmushi.
Shiga tayi cikin parlourn
Kallo ta kare musu d'aya bayan daya,kana ta kada kai ta shiga daki,
Hajiya Khadijah matar Alhaji Abubakar nura kenan,******
Amina! Amina! Amina! yake kira,Wacce ke zaune akan gado ta jingina da allon gadon, sai dao ko kira daya batajiba sakamakon nisan da tayi a tunanin data fada Wanda ya dauketa tsawon lokaci,
Hannunsa yasa ya dan bugi cinyar ta yasata dawowa daga tunanin,
Kallon ta Yayi kana ya kada kai yace"haba Amina har yaushe ne zaki daina wadannan tunane-tunanen? Bazaki fawwalawa Allah komai naki ba? Shifa haihuwa na Allah ne ko kinason ja da hukunci Allah ne?
YOU ARE READING
NDAIGOL AM (HAIHUWA TA)
FantasyNaso haihuwa sai dai kash HAIHUWATA bata min rana ba,domin ta kasance bakin cikina, zubar hawayena,sannan kuma Dana sanina.