NDAIGOL AM
(Haihuwa ta)By
Sadeey
*Alhamdulillah 4 today, today I'm +1 and also -1🎉🎉🎉🎉🎉
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
'''MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊAN TARWA GAMIDA WA'AZANTARWA HUNMM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITE'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITTE'S EVER💖 '''
*ALƘALAMINMU ƳANCINMU*Free page 5️⃣-6️⃣
———Daddy ne zaune a lambun gidansa ya bawa kofar shigowa baya yayin da iskan bishiyoyin wajen ke kad’awa Wanda ya haddasawa lambun wani Ni'imtaccen sanyi mai shiga zuciya,baka jin karan komai sai na tsuntsaye masu shawagi a sama wadanda suke mallakin lambun ne,
Tunani yakeyi sai yaushe yayansa zasu so shi su daina abunda sukeyi ña cutar dashi ...?
Yana ganin kaman tunda fahad ya tashi bai ta'ba bacci mai dad'i ba... ciwon hawan jinin d'aya sameshi ma yasani ta dalilinsu ne... shi kam yaya zayyi ne da rayuwarsa...?
dama haka HAIHUWA take ne ko kuma tasa HAIHUWAr ne a haka...?(to fans sai ku bashi amsa😂) shi ai tunda fahad ya kai 26-28 ya sake masa komai nasa na kasuwanci.... Ameer na girma shima ya bashi nashi,domin a ganinsa a lokacin da yaransa suka girma to shi kuma wannan lokacin ne zai huta,sai Ameerah wacce take mace da bai damu da damuwanta ba , bai nuna mata komai ba domin shi a ganin sa HAIHUWAr ya mace ba komai face asara..., yasan HAIHUWAr mace babu abunda zai kareka shiyasa bai wani bawa Ameerah muhimmaci a rayuwa ba don yasan *6iddo debbo dun zanawal goddo* yasan ya mace duk wahalan daka sha a kanta karshe gidan wassu zata,dama masu iya magana sunce ya mace: *Bishiyar gidanka,inuwar gidan wassu,* wanñan dalilin yasa ko damuwarta bai damu daya sani ba.... In fact shi a HAIHUWArta ma bayyi farin ciki ba, yafi farin ciki a haihuwar su ameen kasancewarsu *'ya'ya maza*....(Ya manta yaya na gari kawai ake nema ba komai ba,ya manta cewa. *yaya mata ma yaya ne* , sannan yaya mata alkhairi ne, shi dai kawai son yaya maza ya rufe masa ido.)
A rayuwarsa tun yana yaro ya tashi da burin abu biyu *KUDI..!* *HAIHUWA..!* yana ji idan baka da wadannan abubuwan to tabbas rayuwar ka incomplete ne,wannan dalilin yasa ya bi duk hanyar da ya bi yasan Yayi kudi sannan kuma ya sai HAIHUWA wacce ta zamo masa masifa da bala’e.....
wani Abu ya tuna da ya shude wanda a kalla zai kai shekaru 35 kenan.....
Numfashi ya sauke kana ya dauki glass cup daya tsiyayi ruwa ya kafa kai fara sha sai daya shanye na cikin cup din ya sake k’arawa kafin ya fara sauke togwayen ajiyar zuciya, kana ya dauki wayarsa ya fita daga lambum,......
Tun bayan kai masa ruwa take tsaye gaban window dake dakinta Wanda yake kallon cikin lambun shiyasa take iya kallon duk wani motsinsa,
Danne abunda ke taso mata tun daga cikin zuciyarta tayi cikin wani yanayin da ita kadai tasan yadda takejin ta sauke Numfashi tare da sake labulen dake hannuta.
*****
Haka Amina ta zauna ta tiki aikin kaman wata karamar yarinya wacce batasan dadin jikin ba,sai dai kaman yadda inna ta fada kafin 5 ma ta gama kasancewar 6 Alh.Abdullahi ke dawo wannan yasa ta dauki warmers daga side dinta ta sa nata da nashi tamkar ita tayi, sanna ko da ya dawo ma bata nuna masa komai ba,sai Dan gajiyan daya gani tattare da ,Iya dai Yanzu komai fes, ranta fari kaman farar auduga aganinta ko ba komai itama zata rama nata ko da kwatan kwata ne açikin abunda tayi mata,tunda ita gani take ita ta hana Abdullahi kara Aure don haka ita kuma yanzu ta fara muzguna mata karshe idan ta gaji taje ta tone abunda ta binnewà danta wanda ko maganan karin aure baya son ji.( *Note* Iyaye mata muyi hattara don matar danki bata HAIHUWA bazaki zauna kina muzguna mata ba,Allah shike bada HAIHUWA ,idan kuma ita taki haihuwar da gangan to Allah zai saka miki tunda dai shi ba azzalumin ko bane. )
YOU ARE READING
NDAIGOL AM (HAIHUWA TA)
FantasyNaso haihuwa sai dai kash HAIHUWATA bata min rana ba,domin ta kasance bakin cikina, zubar hawayena,sannan kuma Dana sanina.