3-4

6 2 0
                                    

*NDAIGOL AM*
       (Haihuwa ta)


             By
 
      Sadeey

09139216255

FREE PAGE
3️⃣-4️⃣ 

———Monday 7:40   mutanen gidannane  zaune akan dining mai kujeru shida dake cikin parlourn mahaifiyar su suna breakfast,daddy ne baya gurin kasancewar a paloun sa yake cin abinci,
kowa cikin shiri da alamun aiki zasu,

7:40 . suka gama tare da tashi kana sukayiwa mahaifiyarsu sallama wacce ta bisu da addu'a kaman yadda ta saba duk da ba amsawa suke da amin ba, a yayinda Ameerah ta tashi don tattara wajen don itace zakkan hankali a gidan,

★★★★★
Kaman yadda suka saba yau ma ajere suka nufi side d’in hajiya don gaisheta, duk da  amsa gaisuwarta takeyi ba,sai dai bata gajiyawa da zuwa ba,

Alh Abdullahi ne ya fara gaisheta kaman yadda suka saba,

Cikin dari-dari tace

”ina kwana Iya? Fatan kin tashi lafiya,

” Lafiya klau Amina,

ba Amina kadai ba hatta shi alh Abdullahi ba karamin mamaki sukayi ba don tsawon shekaru bata  amsa gaisuwar Aminan ba wacce har ta daina damuwa,

gane hakanne yasa Iya fara kuka tare da kunce bakin zaninta ta fara fyace hanci  kana ta fara cewa

” 'Yannan kiyi Hakuri da abunda ya faru wallahi sharrin shaidan ne da rufin zuciya ,amma yanzu na gane kuskure na HAIHUWA dai Allah ne ke bayarwa amma shaidan ya rufe min na kasa ganewa,San Allah kiyi Hakuri ki yafemin Aminatu sato ta karasa tana hada hannayenta biyu alamun neman tafiya, amina dai shuru tayi don  bata yarda da wannan abun ba,sai dai Alh abdallah kam ya yarda (tsakanin d’a da Uwa .)

ganin tayi shuru ne yasa Alhaji Abdullahi kaman hannun ta tare da gyad’a  mata kai,

Kunya Amina taji yasata sauke numfashi  kana ta tabbatar da ta yafe mata.

Bayan dan hiran da suka ta6ane  wanda Iya da Alh. Abdullahi  ke yinsa  don ita dai Amina bata magana kasancewar bata saba ba.

Alh Abdullahi me ya mike  da alamun tafiya zayyi.

ganin haka yasa Amina mikewa itama  da  niyyar tafiya.

”Addu'a  Iya tamishi tare da cewa  a’a Amina Dan Allah zauna  ki tayani hira kinga  Mairo mai aikina jiya ta tafi  K’auye ta karasa maganar cikin sanyi,da to Amina ta amsa,yayinda Alh. Abdullahi  bai kawo komai a ransa ba sai ma farin cikin da yakeji, ya musu Sallama ya fita.

Motan Abdullahi na barin harabar gidan,kaman iya jira take  ,take fusksrta ta changer ta komai asalin Iya na da ,

Cikin tsuke fuska ta kalli Amina tace ” idan kid’a ya changer to dole rawama ya changer na kori  Mairo  ne saboda ba anfanin  biyanta bayan gaki,aikin  me kikeyi a gidan idan garin Allah ya waye? don haka daga yanzu komai na gidannan kece zaki na yinsa,tunda bakida aikina sai aci ayi bacci a tafi kashi  bazaki haihuba kuma bazaki barshi ya sake aure ba,nidai naga jafa’i duk marigayi (malam Masir)ne yajamin wannan ibtila’en anbi an mallakemin d’a kwaya daya kaman zuciya a jikin   d’an Adam,to wallahi daga yau kin daina girki a 6angarenki kece zaki nayin komai na gidannan har da sharan tsakar gida da yiwa furanni bayi (Kasanacewar bayan rasuwar mlm Nasir,Alh Abdullahi yayi renovating gidan)  wanke motoci ma idan ta kama ke zakiyi,daga yanzu aikin zai fara ki tashi ki  share bangarennan duka,sannan Ki shiga dakina kaf kayan cikin wardrobe dina ki fito dasu ki wanke  don duk warin ajiya sukeyi,sai ki dora mana abinci  sannan daga yanzu abinci biyu za'anayi na safe sai na rana na gaji da asaran da akesa Dana yanayi  babu gaira babu dalili, da akwai yara ne to ba makawa za'ayi abinci har dana hudu  amma babu kam ba za'ayi ba wallahi, sannan Abu na karshe ki tabbatar kafin 5:00 kin gama don banason ya dawo ya taraddake kina aiki a gefennan ,abu na karshe kuma ko da wasa kika sanar dashi wallahi ni da kene idan kunne yaji to jiki ya tsira.

NDAIGOL AM (HAIHUWA TA)Where stories live. Discover now