EPISODE_01

87 7 12
                                    

🔮🔮🔮
           *SIDDABARU*
                  _A Mafia Story_
                                 🔮🔮🔮
  
_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

              ✨✨ *APRIL 2022*✨✨

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
    

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣1️⃣*

Busar iska ake mai cike da ni'imar ubangiji,inda kuma sararin samaniya ta gauraya da haduri baki wuluk,kasar wannan haduri ko wata farar haske ce, ta haskake ilahirin gurin,abin gwanin ban sha'awa.
A daidai wannan lokaci kuwa wata farar mota, ta bayyana cikin *high-speed* kai tsaye ta nufi bakin rafi,inda mutane ke zuwa domin shakatawa,But surprisely babu wanda ya kasance a wannan guri ta sanadiyar wannan haduri.

Wani santalelen saurayine ya fito daga cikin wannan gabjejiyar mota,bayan motar ta tsaya dap da bakin ruwan,fuskar sa kuwa babu annashuwa ko kadan,fitar sa ya naimi wuri ya zauna sannan yayi tagumi alamar yana cikin damuwa,Soma tuno wasu kalmomi yayi,kalmar ko ta saka shi zuwar da kwalla...
Wannan kalma ko itace *we can't be more than friends,because I don't have a filling for you*

Hakanne yasaka shi jifa da wayar dake hannun sa,sannan ya saka hannu ya share kwallar dake zubo masa a fuska yin hakan dayayi yana tunanin zata rage masa wani part cikin kuncin dayake ciki, but dadɗa cusashi cikin damuwa hakkan yayi *he keeps on acting like everything is alright* amma kuma yin hakan babu abinda ta ragarmai......

Soma zabga ruwan sama akayi babu kakkautawa kaikace da bakin kwarya ake,dukda ruwan saman da ake zabgawa hakan bata saka ya koma cikin motar tasa ba, zama yayi akan ruwa,har daukewar ta 8:22 na dare.

Zaune yake sai famar kakkarwar tsiya yake hakwaran sa kuwa na bada sautin kak kak kak,Nan yake sai yajiyo wata kara mai kamada rushewar kayan kwalba abaya sa,nan da nan ya juya ya fuskanci gurin sannan kuma ya cike da mamaki domin dogayen bishiyoyine bila adadun bayan sa,babu alamar wani a kusa amma yajiyo karar rushewar tarkace,hakan ta sakashi cikin fargaba.

Nanfa ya mike ya soma waige waige indako ya soma jiyo ana kiran sunan sa cikin rad'a  *Eshan!! Eshan!! Eshan!!*

Abinka da mai naiman matsifa,bin wannan sautin yayi tayi har ta kaisa izuwa wata lambu mai cike da al'ajabi...
Cikin wannan lambun al'ajabi dai ko'ina furanni ne masu launin jan hankali sararin samaniya kuma taurarine tako'ina ga kuma farin wata....wanda ya haske gurin.

Nan yake yana ta washe hakwara sai yayi arba da wani haske wacce hasken natama abin sa'awa ne,da ganin haka yayi saurin karasawa gurin inda ya tarar da wata *kundin* wacce akayi mata ado da jan karfe sannan kuma aka tsarata irin ta zamanin daa.

Da ganin wannan littafi ko yasa hannu ya dauka, nan da nan hasken ta yaye,ya koma normal Kundin....
Da ganin jikin wannan kundin kuwa kasan ba abanza aka tsara ta ba,a jikin nasa anyi rubutun kalmomi biyu wanda shine *KUNDI* da kuma *AL'AJABI* wacce idan ka hadasu biyun zasu baka kalmar *kundin Al'ajabi*
Bayan ya dauki kundin sai damin 🦋🦋🦋🦋 butterfly suka kewaye sa,hade da jansa izuwa wata kujera wacce aka tsarata da furanni suka kuma zaunar dashi....haka wasu suka zo masa da wata hular fulawa👑suka daura masa.

SIDDABARUWhere stories live. Discover now