🔮🔮🔮
*SIDDABARU*
_A Mafia Story_
🔮🔮🔮
_________________________*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________✨✨ *APRIL 2022*✨✨
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣2️⃣**AKWATI*
Haka wannan akwatin ya gangaro izuwa kasan wannan tsauni,Yayinda suka tsaya kallon sa har dirar sa kasan,kafin nan suka Juyo cikin fushi hade da ɗago bindigar su sukayi nuni da ita kan *Awais*"Babu Abinda zata hana ni fasa maka kai,idan da nasan abinda zaka aikata kenan."
Fadar Eysha kenan inda Malik yayi sauri cewa."Munyi da Jafaru karfe Goma shep zamu hade a nan gurin,kunga kenan mintuna Talatin kacel muke dashi na samo wannan akwatin dan haka ya kamata mu gaggauta nemo wannan akwatin tunkan jafaru ya karaso."
Dajiyo wannan batu na Malik sai Eysha tayi ajiyar zuci hade da sauke bindigar ta Juyo ganinta izuwa kan Malik,Haɗa fuska tayi yayinda suke kallon cikin Idanun juna..
"Zamuji da Al'amarin Awais later."
Sake furta hakan Malik yayi itako bata ce dasu komi ba ta Juya ta soma tafiya cikin sauri haka Malik ya biyo ta abaya Awais ma haka...Sauka sukayi izuwa inda suke tsammanin akwatin zai fadi amma suka tarar babu komi aiko Malik jujjuyawa yayi yayinda yake haske guraren da Touch light but still Babu alamar akwatin a kusa....
Alama Malik yayi musu da hannu da su zaga su duba ko zasu sami akwatin but still bayan sun zaga babu wanda ya sami akwatin...Haka suka sake hadewa a guri guda.
"Shin Akwai wani labarin ko kuma wata alamar?."
Hakan Malik ya tambaya yayinda ya haske fuskar Eysha da Touch light itako girgiza kai tayi alamar A'a shi ko Awais gajeriyar murmushi yayi sannan yace dasu."Wata kila fiffige tayi ta fire akwatin."
Aiko kafin ya rushe baki sai yaji an sharara masa tafi a fuska, aiko ba kowa bane yayi wannan illa Eysha dake tsaye gefen sa,ganin hakan ya sakashi haɗa rai hadi da yunkurin kaiwa Eysha martani,But shiga tsakani Malik yayi yayinda suka soma kaiwa juna suka suna mai zagin juna cikin cacan baki...."Ku daina Wannan shashancin."
Cikin kara Malik ya furta hakan,aiko tsit sukayi nan Malik ya hau surutun cewa."Ku wai Maike damun kune eh,meye anfani wannan rigima yanzun?,kowa dai yanzu yasan yayi kuskure amma mai makon mu naimo hanyar magance Wannan kuskure a'a ku ba hakan kuke tunani ba sai bata mana lokaci kuke da wannan fadace faɗacen naku na banza,karku manta dai nine jagora a wannan aikin dan haka ya zamanto dole kubi umurni na domin mession namu har yanzu bata kare ba,and we all know Idan har wannan aiki bata tafi yadda aka tsara ba dukkanin mu makomar mu itace mutuwa."
Aiko da jiyo wannan zance dukkanin su jikin su tayi sanyi nan Eysha ta sauke Idanu hade da cewa...
"I'm sorry Malik."
"Why?."
Tambayan da Malik din yayi kenan inda Awais yayi saurin basa ansa."we are sorry sabida wauta irin tamu ce masu gajerun tunani take kokarin taɓarɓarar mana da wannan aiki."