🔮🔮🔮
*SIDDABARU*
_A Mafia Story_
🔮🔮🔮
_________________________*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
_________________________
✨✨ *DEC 2023*✨✨
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
Wattpad Link 👉👉https://www.wattpad.com/story/307225239*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣5️⃣*🅿️REVIOUSLY 🅾️N SIDDABARU🏴☠️🏴☠️🏴☠️
_A shirin daya gabata,an tsaya a inda tawagar ƴan shan jini sukayi awun gaba da Eshan inda suka garkameshi a cikin wata kurkuku a karkashin kasa..._
_al'amarin su bera da shaho kuwa tsinkar kansu sukayi a jensin bil adama yayin da ta cikin wannan suffar suka tarar da wata wacce ta kasance a suffar Yusra,bokanyar nan ta cikin kogo kuwa tura dakarun ta tayi Izuwa doron kasa da su kawo mata gawar Yusra da kuma Eshan a raye domin cika burin ta_
_haka Kuma Zain ya baro gida da niyar fadawa duniya domin naiman waraka daga bakar sammun dake bi biyan sa,a Yayin wannan tafiya kuwa kaddararsu tazo daya data su Malik yayin da suka dire a samar motar su bayan shi Malik din yaji rauni a kafadar sa._*EPISODE 0️⃣5️⃣*
Cikin sauri tsohon Zain ya shigo gidan yayin da yake taku kaikace wani abinne ya faru,har tuntube yake yi Yayin da yake wannan tafiya
"Zain! Zain!." haka tsohon yake ta kiran sunan nasa amma shiru kake ji gidan babu kowa,haka ya shige dakin Zain kai tsaye inda ya tarar da Dakin babu kowa,dashike ba haduwa da Zain bane dalilin zuwan sa gidan shiyasa bai wani tada hankalin ba wajen naiman sa.Kai tsaye ya nufi makwancin Zain inda ya zube akan gwuiwowinsa yakuma sa idanu karkashin gadon da Zain yake kwana akai, gajeren murmushi ya yi bayan ya tarar da wannan akwatin daya shigo gidan dashi daren jiya.
Kurama wannan akwatin ido yayi bayan ya ciro ta daga karkashin gadon... cen sai ya yi furucin cewa "babu shekka akwatin nan ne suka zo naima, gaskiya ne jitajitan da mutane ke yaɗawa a gari,jiya wasu da ba'a san ko su waye ba kuma ba'a san Meya kawo suba sun shigo wannan gari, saida Ni kadai nasan dalilin zuwan su wannan guri domin kuwa ba komi bane ya kawo su illa wannan akwatin."Bayan ya furta hakan sai ya yi shiru na wasu dakiku kafin nan ya bawa kansa shawara cewa "gaskiya ya kamata nasan Meye a cikin wannan akwatin,domin na gane ma kaina."
Daukar akwatin ya yi izuwa falo inda ya jibge a kan center table,kokari budewa yake abin ya gagara nan sai ya yanke shawarar ballawa aikuwa bayan ya aikata hakan sai ya bushe guri guda dan mamaki.
"Zain!." Abinda Ya fara fitowa daga bakinsa kenan dan rudewa da kuma mamaki hakan ta faru ne ta sanadiyyar tarar da kaya kin sakawan Zain ne a cike cikin akwatin.
Idan muka kyale wannan dattijon cikin dakin Zain muka laika bangaren zain kuwa zamu riske shi yayin da ya toshe kunnuwan sa da hannayen sa biyu ya kuma saukar da kansa kasa yana furucin "Not again." Yana ta girgiza kai alamar a'a.
Ya dauki lokaci yana hakan cen daga karshe ya kwarma bagidajiyar ihu wacce yasa duk kwalaben dake wannan guri suka dagargaje dan zafin wannan sautin, faruwar haka yasa direban dake tuka wannan mota ya taka biriki a lokacin da Zain yake wannan ihu domin kuwa bayan Farfasa glass din da wannan kara ya yi ta kuma fi karfin dokin kunne dan kuwa idan da ya dauki lokaci yana wannan ihu da kuwa duk sai kunnuwan su ta daina ji,Duk da haka sai da kunnuwan su ta daina jiyo sauti na wasu dakiku kafin nan ta dawo daidai,shiru kake ji gurin babu mai motsi hatta Su Eysha da suka kasance a saman wannan mota,kowa dake cikin wannan mota cike yake da mamaki hadi da kuma waige waige domin Babu wanda yasan inda wannan kara yake fito,haka kuma babu wanda ya budi baki yace kala sai zuru zuru suke da idanu.
kwatsam sai suka ji an dire daga saman wannan mota, kai ganin su sukayi izuwa gurin inda suka tarar da Eysha tsaye,takawa tayi cikin kasaita har ta shige wannan mota aikuwa ganin yacce take ta jujjuya idanu yasa direban yayi kokarin jan motan domin ya kara gaba amma sai ta zaro bindiga daga kugunta ta daura masa aka,ba tare data fadi komi ba haka wannan direban ya janye kudirin sa, tsayawa kallon juna sukayi har Awais ya sauko daga saman motan nan da Malik a hannun sa,yayin da Malik din ya kasance a wani yanayi makamancin suma.