🔮🔮🔮
*SIDDABARU*
_A Mafia Story_
🔮🔮🔮
_________________________*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
_________________________
✨✨ *APRIL 2022*✨✨
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
Wattpad Link 👉👉https://www.wattpad.com/story/307225239*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣4️⃣*🅿️REVIOUSLY 🅾️N SIDDABARU🏴☠️🏴☠️🏴☠️
_Al'amarin wannan tsohuwa kuwa fashewa tayi da muguwar dariya.. hadi da kuma cewa "daga karshe saiga wanda na ɗibe shekaru da dama ina jiran baiyanar sa ya taho har inda nake,da murmushi a Fuskan ta takirawo wani sunan da Eshan Din da kansa shima baisan inda ya samin wannan sunan ba ASHRAF _the Protector_ maraba da zuwa duniya ta."_
_Abubuwa da dama sun faru tsakanin tsohuwa, Yusra da kuma Eshan wacce ta haɗa da konewar Fuskar wannan Tsohuwa ta sanadiyar feshin jinin Yusra data zuba a Fuskan ta, hakan kuma ta kubutar da Eshan & Yusra daga hannun wannan izuwa wata muguwar sahara mai Babbaka sassar jiki, kasancewar su a wannan guri yasa suka sake fadawa hannun wasu mutanen na daban wacce suka masu maraba da zuwan kaman haka._
_"TANVEER the Rays of light muna maraba da zuwan ka."_
_Bayan ta furta hakan tayi gajeriyar murmushi._*EPISODE 0️⃣4️⃣*
CIKIN KOGO
Shesshekar kuka ne ke tashi yayinda wannan tsohuwa ta kasance tayi wani irin zama na takaici hadi da boye fuskanta,yayin wannan kuka kuwa ta dauki lokaci mai matukar tsawo tana hakan,cen daga karshe saita fashe da muguwar dariya hadi da mikewa tsaye tana kai komo,nan sai konenniyar rabin fuskar Tata ta baiyana wacce ganin wannan konenniyar fuska kadai abin tsoro ne.Wannan tsohuwa daukar wata ƙatuwar kwanu tayi ta jibge akan teburin dake gaban ta, sannan ta soma wani surkulle cikin kwanun aiko cikin kankanin lokaci ta haɗa wata tsumin siddabaru wacce ta ɗura cikin wata ƴar kararramar kwalba mai feshi kamar ta tirarai bayan tayi hakan saita dauko wuka ta yanke hannun ta na hagu sannan ta soma lissafo wasu kalmomi tsafi,aiko cikin Abinda bai wuci dakika guda ba saiga wasu kyawawan ƴan mata biyu sun baiyana gaban ta,itako ba tare data ce dasu komi ba ta mika musu wannan tsumin siddabaru sannan ta dauko wata ƙatuwar madubi dake yashe a saman teburin ta shafi ciki nan da nan saiga fuskar Yusra ya baiyana yayinda ta kasance kwance take a kungurumin daji,nan wannan tsohuwa ta hade fuska hadi da cewa.
"Yusra kenan wacce kaddaran su tazo daya dana Eshan."
Furta hakan tayi bayan ta shafi wannan madubi saiga Eshan ya baiyana yayinda suke kallon abinda ke faruwa dashi a daidai wannan lokaci wato durkushen da yake gaban tarun mutanen nan masu sanye da jajayen kaya...
"Abinda nakeso ku aikata min shine ku kawo min Eshan da ransa amma kafin nan ku tabbatar kun gindayar da rayuwar Yusra domin idan har suna a tare babu mahalukin daya Issa ya ci galaba akan su."Aiko ba tare da wayennan tsula tsulan ƴan matan sun ce kala ba suka bushi Issa suka ɓace kai tsaye,idan kuma muka tsunduma cikin madubin da wannan tsohuwa ke ride dashi a hannu zamu tarar da ESHAN yayinda ya kasance gaban wannan taro na mutane masu sanye da jajayen kaya.
Jagaban wannan zuga dake tsaye a baya tattaki tayi har gaban Eshan sannan ta yaye Kellen dake fuskarta hadi kuma da cewa
"TANVEER the Rays of light muna maraba da zuwa."
Bayan ta furta hakan tayi gajeriyar murmushi, wacce wannan murmushi ne yasa Eshan daga tafin hannu yayinda ya daidaita tafin hannu nasa da kafaɗar sa kuwa saiya dunkule ta,aiko ganin haka yasa wannan mata ta mika hannun ta daga inda take tsaye aikuwa saiga wani bakin kaca ya fito ta cikin hannun rigar nata sulululu yayiwa hannu Eshan sarka, Eshan ko ganin abinda ya kudiri niya ta riga ta faru ya saka shi yayi gajeriyar murmushi wacce ta saka jagaban tawaga tace dashi.