🔮🔮🔮
*SIDDABARU*
_A Mafia Story_
🔮🔮🔮
_________________________*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
_________________________
✨✨ *APRIL 2022*✨✨
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
Wattpad Link 👉👉https://www.wattpad.com/story/307225239*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣3️⃣**ZAIN*
Cikin yanayin bacci wannan dattijon ya kwantar da Zain yayinda ya jawo barko ya lullube sa da ita.. Bayan yayi hakanne ya mike tsaye hadi da cewa... "Bacci mai daɗi jika na."
Haka wannan dattijon ya furta Bayan nan ya wuce ya kyale shi kwance,aiko fitar sa da wasu dakiku Zain ya sake komawa a yanayin mafarki hade da shure shure Al'amarin Jafaru kuwa Ganin an datse masa kira ne ya sakashi hada rai hade kuma da sake daura wayan a kunne da niyar sake kiran nasu amma sai yaji wayar a kashe aiko sauke wayan yayi hade da cewa... "Yara dani kuke wasan." Bayan ya furta hakan sai ya turawa Gafur sakon cewa *"I found something,ya kamata kazo ka duba."* Bayan nan yayi gajeriyar murmushi... Kai tsaye Gafur ya taho gurin,inda ya tarar dasu,issar sa da tawagar nasa keda wuya Jafar da saura abokan aikin suka rusuna suna mai nuna girmamawa hade da kwasan gaisuwa.."Jafar hakan na nuna cewar wayenda sukayi wannan aika aikan suna kusa,amma bai kamata daga ganin wannan alama mu amince da fadar wancen yarinyar ko kuma mu daina farautar ta ba,tunda na riga na sanar da shugaba kuma ya bada umurnin kawo ta araye,ina ganin yanzu aikin ya rabe mana gida biyu... dole yanzu musan yadda zamuyi mu rabe gida biyu domin tafiyar da wannan aiki yadda ake bukata, inaso muyi kokarin samun wannan akwatin kafin Susan Maike ɗauke acikin."
Dajiyo hakan sai Jafar yayi gajeriyar murmushi hadi da yin wani batu a kasan ransa... Cewar shine "Yanzu ne zaku fahimci abinda ake nufi da Rayuwa ko mutuwa."Yusra.
"Eshan Ya kasance abin farauta ne ga ire iren mu domin shidin ya kasance cika makin iko ne na duk duniya,amma kuma zaki zame min katanga ga cikar buri na toh yanzu mai kike ganin zan aikata kenan ga wannan katanga dake kokarin tare cikar buri na?." Bayan furta hakan datayi saita fashe da dariya wacce tasa hanjin cikin Yusra kadawa"Yusra shin kin tsorata ne,ko kuma dai mamaki kike ne,shin na sake sanar dake wani abin mamakin?." Tambayoyin da wannan tsohuwa ta jerawa Yusra kenan bayan Yusra ta jiyo hakan sai ta soma kakkarwan tsiya ta kuma gagara bude baki,Haka wannan matan ta sake da cewa
"Yusra kina tsaye ne akan karfin ikona shin ko kin sanda hakan?." Yusra ruɗewa tayi domin batasan nufin wannan matan ba,haka ta ɗago Idanu tana kallon Fuskan wannan mata yayinda Itako tsohuwar ta sauke Idanuwa kasa alamar tana yiwa Yusra nuni dashi... Aiko sauke idanun da Yusra zatayi sai ta tarar akan iska take tsaye domin ramine mai matukar zurfi a kasanta.
"I'm sorry!." Kalman karshe kenan data fito daga bakin wannan tsohuwa aiko furta hakan keda wuya sai Yusra taji ta zurme cikin wannan ramin haka ta Kwarma bagidajiyar ihu yayinda take sauka izuwa kasan wannan Rami,wannan tsohuwa kuwa juyawa tayi ta koma ta kyale Yusra cikin wannan hali.MALIK
Idan muka gangara bangaren su Malik kuma yanke shawarar karasawa kauye mafi kusa dasu sukayi ta hanyar bin wata shatin sawu.. kuma sun kasance suna mai kyautata zaton mai wannan sawun shine wanda yayi gaba da akwatin,kuma fa hakane domin wannan sawu shine sawun dattijon nan wanda yake kula da jikansa wato Zain Amma Kuma Taya zasu gane hakan? tunda iyakan sawun kafafunsa kadai suka gani.... Haka suka kasance suna bin wannan sawun kafafu har ta kaisu wannan gari,amma kuwa rashin Sa'an da sukayi shine isarsu kauyen keda wuya aka soma zabga ruwan sama again... Aiko tuni suka naimi shatin kafafun suka rasa. "We are all in Danger now!." Fadar Eysha kenan inda Awais yayi saurin cewa da ita "Bai kamata muyi saurin karaya ba Eysha."