🪂🪂🪂🪂🪂🪂
*SAHIBUL AMRAT*🕊️👑🤺🎺
*Zainab Habib(Mom Islam*
_Banyishi dan wani ko wata na ,inhar yazo dai-dai da labarinki arashine👌_
_________________9-10
tun daga ranar Hindu ta koma gurin Hajya Rabi.
Hindu fara ce tana da ƙiba amma bamai muni ba ,ba wata kyakkyawa bace amma baza'ace mata mummuna ba.
Bayan dawowar Hindu ,Hjya Rabi ta fara shawarar haɗa Hindu da prince aure ,amma gefe ɗaya bata sonsa ko kaɗan , prince ya lura da irin tsanar da Hjya Rabi take nuna masa hakan yasa ya dena zuwa sashinta koda kuwa nemansa take sai dai tazo da kanta ,
Hajiya Amina mace ce mai mutunci bata jin ƙyashin yiwa kowa abin arziƙi ,
Lokacin da Hindu ta cika 50days a gidan su prince Hjya Rabi ta sami mai martaba akan tanason a haɗa auran prince da Hindu , mai martaba sam bai amince ba sabda rawar kan da yarinyar take dashi , bugu da ƙari tarbiyya bata isheta ba ,amma yace "ni nawa mai sauƙi ne inhar Ibrahim ya amince to nima na amince "cikin farincki ta dinga jerawa sarki kirari daga ƙarshe tabar gurin .
Burinta shine inhar Hindu ta auri prince sun warke sarki na mutuwa prince zai hau mulki idan prince ya mutu yaron Hindu Za'a naɗa , dalilin kenan.
Back to story.
Hjya Amina ce zaune a kishingiɗe jikin wani haɗaɗɗen filo ,gefe kuma jakadiya ce zaune tana ɓarewa Hajiya Amina ayaba , Hajiya Amina ta kalli Jakadiya kana tace "ni kuwa Hindu tana nan ?" Jakadiya tace "ranki shi daɗe ai ɗazu ma na ganta a gurin yarima ,ga dukkan alamu saɓani suka samu "Hjya Amina tace "mai ya kaishi shiga harkarta ?" Jakadiya ta sunkuyar da kai kana tace "Allah ya taimakeki wlhi basan meya haɗasu ba "Hjya Amina tace "shikenan .
Washe gari ta kama Alhamis da misalin ƙarfe biyu na rana bayan anyi azhar ,Prince Khalil ya shigo side ɗin Amminsa ,tun daga nesa dogarai suke kwasar gaisuwa har ya so ɗakin Ammin nasa ,sallama yayi kana ya ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa yace "barka da hutawa Ammi da fatan na sameki lafiya " Jakadiya dake gefe sai kirari take yiwa prince tana cewa "Allah ya taimaki ɗan sarki jikan sarki takawarka lafiya yarima mai mai jiran gado "Ammi ce ta ɗaga mata hannu alamar ta basu guri , cikin girmamawa jakadiya tace na barki lafiya .
Tashi zaune Ammi tayi ta kalli fuskar prince taɗanyi murmishi wanda ita kaɗai tasan ma'anarsa ,kafin tace ",ubana kwana biyu na lura dakai kana cikin matsala wani abunne ya faru ?"ɗan rausayar da kai Khalil yayi kafin yace "Ammi Hindu ta fita a harkata wlhi zan saɓa mata "Ammi tayi gyaran murya kana tace "ni kaina ba son haɗin nan nake ba ,saboda Hindu bata da kamun kai ko kaɗan ,adu'armu kaɗai ce zatasa mai martaba ya janye da kuma kaima idan baka nuna kana so ba " hankalin Prince Khalil a tashe yace "Ammi kinsan mama da naci idan ta nacewa mai martaba zai iya amimcewa " Ammi tace "karka kawo komai a ranka ,kai dai kaci gaba da adu'ar neman zaɓin Allah ,nafilolin daren nan daka saba karka fasa.
Tunda suka fara magana wata baiwa ke tsaye a bakin ƙofar tana girgiza kai , shirun da taji Ammin prince tayi ne ya sata wucewa part ɗin hjya Rabi da uban gudu har tana tuntuɓe ,ta zube gaban hjy Rabi tace "Allah ya taimakeki uwar ɗakina Allah ya ƙara nisan kwana wata magana naji a sashen su yarima mai jiran gado "keeee...! Hjya Rabi ta daka mata tsawa tare da sauke ajiyar zuciya mai zafi tana huci tace "karki sake cemin yarima mai jiran gado dan in Allah ya yarda bazai gaji wannan sarautar da yake taƙama da ita ba inhar ba auren gimbiya Hindu yayi ba ,inhar ina numfashi a doron ƙasa bazan bari Ibrahim ya gaji sarauta ba , inada yaƙinin zan haifi wanda zai zamo sarki ko ta halin ƙaƙa ai mai martabar bawai ya tsufa bane bare ace kwanan nan za'a naɗashi ,ta ƙarashe maganar tana dafe kanta .
Hindu dake kwance a kan cinyar Hjya Rabi tace "to Umma idan har ya kasance mai martaba ya rasu kafin lokacin da zaki aihu fa ?" cikin ɓacin rai Hjya Rabi ta kalleta ,delo yasata yin shiru badan ta ƙarƙare maganarta ba .
Hjya Rabi ta kalli baiwar tata kana tace "Iyami wane zance kika jiyo ne ina sauraronki "
Baiwa Iyami tace "magana suke akan wai yarima bazai auri Gimbiya ba " da sauri Hjya Rabi ta janye Hindu daga jikinta kana tace "wlhi ƙarya ne ,ashe ma bacci nake ".
Bayan anyi sallahar la'asar .
Tunda Prince yabar part ɗin mahaifiyarsa ya koma nasa part ɗin , a palo ya sami hadiman nasa an cika dinning table da kayan ciye-ciye , kallonsu ya shigayi ɗaya bayan ɗaya , gaban table ɗin yaje ya tsaya tare da ƙare musu kallo sbda ganin baƙuwar fuska da yayi , haka kawai yaji jikinsa na nunar masa akwai wata matsala ,cikin takunsa na ƙasaita yaje gaban sabuwar baiwar ya tsaya kana ya nan naɗe hannunsa a ƙiji ,shigowar Abdallah ne ya dakatar dashi daga faɗar abinda zaice "Abdallah shine yaron waziri kuma babban abokin prince Khalil , Abdallah ya ƙaraso da sallama yana murmishi ,bayi na kwasar gaisuwa a gabansa ya riƙe hannun prince kafin yace "muje dan Allah kaji wata magana " sai da prince yaɗau lokaci sannan yace "jeka ina zuwa " ba tare da Abdallah ya ƙara magana ba ya wuce kasancewar yasan koda yaƙara magana ba lallai ya sami amsa ba , prince ya tako har gaban baiwar wato Iyami yace "a kira masa Jakadiya "cikin sauri ɗaya daga cikin bayin ta tashi tare da ɗan sunkuyawa ta fice "tana zuwa ta sami Jakadiya Hauwa'u wacce ta ke kula da part ɗin yarima Khalil ta zube gabanta jiki na rawa tace "bansan waye ya kawo sabuwar baiwa ba "amma dai yarima yace a kiraki "
Jikin Jakadiya na rawa itama tace "to a ciki wacece baƙuwa ? bayan kowace baiwa ya santa kuma nike zaɓota ?".
Suna tafe suke maganar gudun kar suyi babban laifi , suna ƙarasowa babban palon prince sukaci karo da bayin su uku a tsugunne ko wacce da alamun tashin hankali a fuskarta , Jakadiya ta ɗan sadda kanta ƙasa kana tace "Allah ya taimaki yarima mai jiran gado ,fuska ɗaya ce ban santa ba dan bani na kawota ba Allah ya temakeka " wani irin murmushi prince yayi a zuciyarsa yace "baya rasa nasaba da mama ita zatayi hakan tabbas zan basu mamaki ", a fili yace ",babu komai ku barta , a fili dukkansu suka sauke ajiyar zuciya Jakadiya kam hankalinta bai gama gamsuwa da wannan yarinyar ba .
Sbda Ammin prince ce ta zaɓa masa Jakadiya a matsayin mai kula dashi kasancewar tun yana yaro take kula dashi , kuma indai zatayi abu tsakani da Allah take har yanzu bata yunƙurun cutar da Ibrahim ,dalilin da yasa ya yarda da ita kenan.
Prince yama mance da shugowar Abdallah dan zama yayi aka haɗa masa tea yasha da soyayyan dankali , sai da ya gama ikonsa sannan ya wuce bedroom ɗinsa , su kuma hadiman suka ci gaba da gyara gurin .
Yana shiga bedroom ɗin ya sami Abdallah zaune yana kallon wani indian film , Abdallah ne ya juyo tare da cewa "barka da yamma my prince "barka prince yace yana cire gilashin dake manne a fuskarsa yace "shine da ka tafi sai yanzu ka dawo ? Abdallah yace "tuba nake naje anguwarsu yarinyar nan ne ga dukkan alamu bata da tarbiya " prince ya gyara zama kafin yace "ka mance a gidan da muka ganta ne ? "Abdallah yace "tabbas gidan da ake cewa na karuwai ne ,amma meya kai wannan yarinyar gidan ?"prince yayi murmishi kafin yace "asara ka sani ko uwartace babbarsu ?, Abdallah ya jinjina kai kana yace "nidai abin da nakeso dakai shine ka yafe mata "a tsawace prince yace "infa yafe mata kace ?yarinyar da ta yimin zagin tozarci ? to barin gaya maka wata magana idan har bakada labarin ,ba'a taɓa prince a zauna lafiya ,saina rama , ina yafiya amma baga wanda ya zageni ba ,waye ubanta waye uwarta wane matsayi suke dashi ?sai tayi nadamar abin data aikata " cikin ƙasa da murya Abdallah yace "muyi a hankali yarma kar mai martaba yaji komai ya dagule".
Ƙarfe 6:47 pm ) Lokacin ne da aketa kiraye -kirayen sallahar magrib kama daga masallacin gidan har dana maƙota , bayan Abdallah da prince sunyi alwalah sunyi sallah , suka wuce gurin mai martaba , tunda suke fito ake gaishesu har suka shige fadar mai martaba ,Abdallah ne kawai ke amsawa ,da sallama a bakinsu suka ƙarasa ana ta yiwa prince kirari ,yayinda mai martaba keta faɗaɗa fara'arsa.
Bayan sun kuwashi gaisuwa a gurin mai martaba fadawan suka bar gurin da sauran mabiyansu , Prince ne yayi gyaran murya kafin yace "ya Abbana nazo maka da wani albishir "cikin jin daɗi da ƙaunar ɗan nasa yace "Ibrahim ina jinka "Abdallah dake zaune kansa a ƙasa ya besan me prince zaice ba .
Prince yace "Abba Abdallah jiya ya sameni akan yana son Hindu ! da sauri Abdallah ya ɗago tare da kallon prince irin kallon da bai taɓa yi masa ba ,shiko prince murmishi yake ,yaci gaba da cewa "kuma shima Abdallahn yana sonta " mai martaba ya faɗaɗa murmishinsa kafin yace "to masha Allah shine Abdallah ya kasa faɗa sai kai ka ari bakinsa kaci masa albas? har yanzu kan Abdallah a ƙasa yake yana mai jin zuciyarsa na dukan uku -uku ,mai martaba ya mayar da kallonsa ga Abdallah kana yace "hakane babana ?" cikin jin nauyi Abdallah yace "Allah ya ƙarawa Abba lafiya da nisan kwana " hakan yasa mai martaba ci gaba da murmishinsu na manya.
A zahiri dai fuskar Abdallah bata nuna komai ba sbda a sunkuye take kuma ya amsawa mai martaba fuska a sake.
Bayan sun ƙara kuwasar gaisuwa sun fice ,
Mai martaba yayi hamdala dama yana yiwa Hindu adu'ar zaɓin Allah sabda maraicinta , sai gashi yau Allah ya zaɓa mata ɗansa wato ɗan wazirinsa Alhmdulilh a fili yace "yarinya ce mai biyayya nasan bazata bani kunya ba.Suna fitowa dogarai da fadawa suka dinga jera kirari har suka ɓace , hannun prince Abdallah ya kama ya kaishi bedroom ɗinsa ya zaunar dashi kan haɗaɗɗiyar kujera , cire masa alkyabbar jikinsa yayi kana ya janyo kujera wata marar nauyi ya zauna gaban prince kana yace "haba yarima mai yasa zakayimin haka ?kasan ko me mai martaba yace min bazan iya ƙetarewa ba ?".
Shafo sajen fuskarsa prince yayi kana yace "kai dan uwarka ni zaka rainawa wayo ,meya kawo hoton Hindu wayarka ?mai yasa duk lokacin da bayi suka rakata gurin shukokin gudannan kake leƙenta ?".
Tsit Abdallah yayi ,kafin yace ",sai aka ce maka babu so na ƴan uwantaka sai na aure koh ?"
Hararasa prince yayi kana kafin yace "haka dai kace ,inason a haɗa bikina da naka " ido waje Abdallah ke kallon prince sbda tunda suka taso bai taɓa ganin yayi budurwa ba amma yau shine harda maganar aure.....!Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud'inki ta wannan account d'in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224
Idan kuma kati ne zaki d'auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224 y'an Niger suyi magana ta wannan number +22784506476 .
MOM ISLAM