🪂🪂🪂🪂🪂🪂
*SAHIBUL AMRAT*🕊️👑🤺🎺
_Funny love and romantic story_
*Zainab Habib(Mom Islam*
Free page
_Ina mai baku haƙuri akan soyayyar da zaku gani a cikin littafin sbda haka labarin yazo ,ina fatan zaku fahimceni _
_____________________7-8
Ɗan goga kana tace "barka da isowa ".
Alhji Ubaid dake ƙare mata kallo kamar yau ya taɓa ganinta yace "baby wannan wankan duk ni kaɗai ?" murmishi Shamsiya tayi kana tace "eh naka ne "
Bayan sun zauna tunanin wayar dake hannunta ya faɗo mata ,a zuciyarta tace "duk da farfashewar da gilashin wayar yayi bai hanata yimin amfani ba , sai ta zuba tagumi .
Alhj Ubaid dake karantar yanayinta sbda yaga damuwa ƙarara a fuskarta yaɗa dada matsawa daf da ita kafin yace "mai ƙamshi na tunanin me kike ?" cikin sigar shagwaɓa Shamsiya tace "uhm uhm ba wani mutumi bane ya bigeni wayata ta faɗi ta fashe gashi taƙi kawowa "
Alhj Ubaid dake tsananin son yaji anyi masa shagwaɓa ,ya ɗan jijigata alamar rarrashi kana yace "karki damu inhar waya ce kin samu baki da matsala amma kafin nan a bani abin "
Farr tayi masa da ido kana tace "yanzu kam ai ina period i promise jibi har sai ka gaji "bai wani damu ba ya tuntsire da dariya kasancewar a inda tayi masa magana dole ta ɗauke masa hankali .
Hannunta ya kama suka fito tsakar gida , mama na zaune da redio a hannunta ,duk da Alhj Ubaid yaga mama bai sake mata hannu ba ,itako mama sai murmishi take na jin daɗi.
Suna fita suka nufi gurin motarsa ,haɗaɗɗiyar motace mai kyau har wani fitar da raɓa take fara sol.
Alhj Ubaid ya buɗe mata gaba ta shiga ya shiga mazaunin driver ,bayan sun rufo motar a hankali ya fara driving yanayi yana satar kallonta ,a wani katafaren shagon siyar da wayoyi naga yayi parking da sauri ya buɗewa Shamsiya ta fito ,ya rufe suka shiga shagon da sallama , amsawa mutanen shagon sukayi tare da yi musu sannu da zuwa , wani daga cikin masu zama a shagonne ya ajiye musu kujerar roba guda biyu , bayan sun zauna Alhj ya kalli Shamsiya kana yace "mai ƙamshina wace iri kikeso ?"murmishi tayi kana tace "duk wacce na samu " Alhj ya girgiza kai kafin yace "ba girmanki bane dole sai wacce kikeso kamar inda nima na zaɓo tauraruwa " miƙewa tsaye tayi tare da nuna wani kwalin waya a jiki an nuna google pixel 2 , murmishi kawai Alhjn yayi tare da miƙa ATM ɗinsa , bayan sun miƙa masa pos yasa code aka cire iya adadin kuɗin wayar , jikin Shamsiya har wani tsuma yake tsabar farinciki da jin daɗi , a gurin ta rungume Alhj tare da manna masa kiss aka sanya musu a leda suka fito , kai tsaye hanyar da zata sadasu da gida suka nufa yana driving yana kallonta a karo na biyu yana murmishi , kafin yace ", Me ƙamshi na " na'am tace "masa fuskarta yalwace da fara'a kasacewar ta kasa ɓoye farincikin dake ranta , Alhj ya nisa tare da rage gudun da yake ya kamo hannunta kafin yace "ada nasan kinyi taraiyya da mazaje da yawa ,a halin yanzu na haneki da kula ko wanne namiji ,bana son tarkace pls ki kiyaye inahar kinaso mu zauna lafiya "tashi ɗaya idon Shamsiya ya sauya i zuwa ja jawur ta share ƙwallar data zubo mata kana tace "ni ban taɓa amimcewa da kownne namiji ba !babu saurayin da yasannni duk wanda ya gaya maka haka wlhi yayi ƙarya " da sauri Alhj yai parking a gefen hanya a zuciyarsa cewa yake "maganar wannan yarinyar ba abin yarda bane ko kaɗan ,uwarta fa gogaggiyar ƴar bariki ce , babu wanda bashi da tarihin UWAR BARIKI ta shahara gurin tara maza a gida ,gashi yanzu ƴaƴanta sun gajeta tun kafin ta mutu , tsinkayo muryar Shamsiya yayi tana magana tana cewa "nasan ko ita maman namu bazata amince ba bare kai da kasan gidanmu yayi suna a gari " uhm " Alhj Ubaid yace kana ya kalleta ya kuma kallonta sai kuma yace "nidai ki ajiyemin kanki karki bawa kowa kimin alƙawari yin hakan zai sa in tabbatar ke masoyiyace ta gaske "kallon wayar hannunta tayi ta tuno tsadarta ta kalli Alhjn kafin tace "nayi maka alƙawari " okay yace dan shi har yanzu yana ganin she is not... a haka suka ƙarasa ƙofar gidansu ta fito shima ya fito , har zata wuce ya tsayar da ita ,kashe mata ido yayi kafin yace "idan kuɗin acct ɗinki sunyi low ki kirani pls " murmishi tayi kana tace "insha Allah zan kiraka , ta wuce gida shikuma ya shiga mota .
Tana shiga ta samu mama ta tashi a gurin , ta shige ɗakin maman tana cewa "mama zokiga wayata , mama dake kwalliya a uwar ɗaki kasancewar zatayi baƙo bayan isha'i.
Maman tace "Shamagirl shigo " da sauri ta ƙarasa tana dariya ta ajiye wayar a cinyar mama ,waro ido mama tayi cikin farinciki tace "bayan 100k ɗin daya baki ?"eh Shamsiya tace " mama tace "to yanzu ba gashi kin samo arziƙi ba ,ana binki da arziƙi kina gudu , dariya sukasa tare da tafawa ,
Sallamar da baby tayi ne yasa mama amsawa tare da cewa "kinga Shamsiya tayi waya ƴar yayi " ta miƙawa baby wayar , taɓe baki baby tayi kana tace "aikuwa gashi nan Allah ya sanya alkairi "kasancewar murmishin yaƙe take duk basu lur da abinda take ciki ba , ƙasan zucitarta ji take kamar an caka mata wuƙa ,gefe koma tanajin wataran sai ta ɓatar da Shamsiya a doron ƙasa.A take a gurin taba mama kyautar 50k a cikin kuɗin da alhj yayi mata transfer , albarka sosai mama tasa mata kana ta miƙe bayan ta sanya kaya riga da wando mai roba.
Zama Shamsiya tayi a kan kujera mai zaman mutum biyu tare da jona wayar a chaji kasancewar akwai wutar nepa.Mama na fita ta danna number Alhj mai kuɗi ,ring ɗaya ya ɗaga tare da cewa "gani a ƙofar gida , cikin farinciki mama tace "ka shigo ina ɗakin da muka saba haɗuwa " kai tsaye ta wuce fridge ta ɗibo faro da fanta da cups , takai ɗakin .
Tana jerewa a kan table taji sallamarsa , kasancewar taɗan sunkuya yasashi rungumota ta baya yana cewa "nayi missing sosai " dariya taɗanyi kana ta juyo tana jifansa da murmishi mai kashe jiki .
Ihun da aka tsala ne yasa mama ficewa da uban gudu ta nufi ɗakinsu ,sbda muryar Shamsiya taji , tana shiga ta sami Shamsiya riƙe da kanta tana kuka , waro ido mama tayi kana ta buɗe wata samira ta ciro wani ƙullin magani ta ɗibo gaushi ta zuba mata ta luluɓeta , lokaci ɗaya ta dawo haiyyacinta .
Zama mama tayi a gefen kujera tana jera mata sannu ,a zuciyarta kuma cewa take "meyasa wannan yarinyar take yimin haka ? sai nayi baƙo wanda zan huta dashi sai ciwonta ya tashi anya bazan ɗauki mataki ba ?" duk a zuciyarta take wannan maganar , daga ƙarshe ta tashi ta koma ɗakin Alhj mai kuɗi .
Tana shiga ta samesa a tsaye yana murmishi tare da rungumota kafin yace "Hajiyata ni zan wuce " cikin rashin jin daɗi Uwar bariki tace "haba alhji baka karɓi tsarabarka ba zaka wuce ?" no karki damu insha Allah zan dawo zuwa gobe yanzu wani mitin ne na gaggawa ya taso min shiyasa " sam Uwar bariki bataji daɗin hakan ba amma sai ta ɓoye damuwarta , ya ciro bandir ɗin ƴan ɗari bibiyu ya bata tayi masa godiya ya fice.A Ɓangaren Prince tun da ya dawo daga fadar mai martaba yake jinsa cikin ɓacin rai , ya kasa mancewa da magan ganun da Shamsiya ta yaɓa masa , Abdallah ma ya fice tunda yaga idan sukaci gaba da zama faɗa zasuyi .
Nocking ɗin da akayi ne ya sashi ɗago kai da jajayen idanunsa ,a hankali ya buɗe bakinsa kamar mai koyan magana yace waye ?"
Cikin ƙasa da murya tace "nice " bai gane ko wacece ba ya tashi kana ya sakko daga gadon ya buɗe ƙofa ,ganin Hindu tsaye ga bayi a bayanta suna durƙushe ita kuma tana jifansa da murmishi yasa Yarima Khalil cewa "meya kawoki part ɗina ? ɗan murmishi Hindu tayi kana tace "ana gaisheka baka amsa ba " kallon bayin yayi kana yayi musu nuni da hannu alamar su tafi ,suna tafiya ya wanketa da mari ,wanda yai sanadiyar ɗaukewar jinta na ƴan daƙiƙu ,ya nunata kafin yace "nace karki ƙara zuwa inda nake kinƙi ji ko ? a kunyace Hindu ta juya ta kalli dogarawan dake durƙushe ta daka musu tsawa tana ce musu uban me kuka tsaya kallo ku ɓacemin da gani "dakatar dasu prince Khalil yayi kana yace "kai ku zauna kin wuce kinban guri ko saina ƙara miki wani ga dukkan alamu bai shiga jikinki ba " gudun karya kuma kunyata ta a gabansu yasa ta juya zuciyarta na tafarfasa .
WACECE HINDU?
Hindu ƴace ga Hajiya Rabi amaryar Sarki , Hajiya Amina itace babba , sai da ta shekara Ashirin da biyar shekararta ɗaya da aure Allah ya azurtasu da samun cikin Ibrahim Khalil , tun yana ƙarami ya taso da hazaƙa da wayo ,mai martaba yana ji dashi sosai sbda duk wani abu da yake buƙata inhar baifi ƙarfinsu ba ,baya rasashi ,bayan ya gama primary da secondary ,ya ya nemi mai izinin mai martaba akan ya amince masa da ƙarasa karatunsa a India inda ya karanci Business wato kasuwanci , bayan ya kammala karatunsa ya dawo gida Nigeria ya samu mai martaba ya ƙara aure ya auro Hajiya Rabi ,lokacin yana da 32yers a duniya , ganin Amminsa da Hjya Rabi suna zaune lafiya yasa bai kawo komai a ransa ba , har zuwa neman shawara yake gurinta .
Hajya Rabi harta shekara biyu Allah bai bata aihuwa ba,idan ta matsa akan maganar sai mai martaba yace "akwai lokaci , babban baƙincikinta shine inda taga duk wani taro ko shawara da hidimomi mai martaba sai dai yayi da prince Khalil , hakan yasa ta tsanesa kamar ta kasheshi , bata ƙaunar ganinsa tare da mai martaba .
Ranar wata Laraba da safe ƙarfe( 7:12) aka kirata a waya , da suri ta ɗaga tare da sallama , muryar Hindu taji tana kuka tana cewa "Hajiya momyna ta mutu bata nunfashi "a razane Hjya Rabi ta wuce gurin mai martaba tare da neman izininsa ,bayan ya amsa mata tare da cewa "Allah ya jishemu alkairi ta wuce ita da dogarai biyu da jakadiya a motar da take motar baya kuma ta dogarai .
Suna isa gidan suka sameshi a cike da mutane har anyiwa momyn Hindu sutura an kaita , Hjya Rabi tayi kuka sosai .
Bayan anyi bakwai Hjya Rabi ta nemi a bata Hindu zata tafi da ita ,daga danginta harna mahaifinta basu hana ba ,saima fatan Allah ya tayata ruƙo da suka yi mata ....!Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud'inki ta wannan account d'in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224
Idan kuma kati ne zaki d'auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224 y'an Niger suyi magana ta wannan number +22784506476 .
MOM ISLAM