🪂🪂🪂🪂🪂🪂
*SAHIBUL AMRAT*🕊️👑🤺🎺
*Zainab Habib(Mom Islam*
_Banyishi dan wani ko wata na ,inhar yazo dai-dai da labarinki arashine👌_
_____________________3-4
A hankali ta tashi ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da ɗauro alwalar magrib ta fito , tana fitowa taci karo da Affan a zaune ,bata ma san ya shigo ba sai ƙafarsa data buga ne ya tabbatar mata da hakan , a faɗace ya wurga mata harara kafin yace "karki ɗauka kinzo zama ne komawa gidanku zakiyi "ya miƙe ya fice .
Yakai kamar 10mins da fita ,momy ta shigo tare da cewa "tashi kije ga dadynku ya dawo ki gaishesa " cikin bin umarnin momy ta sanya hijab tafita ,kana taje ɗakin dadyn ,sai da ta tsaya a bakin ƙofa tayi sallama bayan ya amsa ta shiga .
Kasancewar yana sama a kan kujera hakan ya bawa Zainab damar zama kan kafeta tace "sannu da dawowa dady ina yini "Cikin sakin fuska dady yace "lpy lou uwata yau kece a gidan namu ?"
Murmishi Zainab tayi kafin tace "dady sai anjima "
Dady yace "to Allah ya tashemu lafiya amma dai zaki kwana mana biyu koh ?"
"Eh" tace tare da yin gaba.Dagannan ta koma bedroom ɗin momy sukayi sallama ta wuce ɗakin da idan sunzo da mamanta suke kwana .
Tana fita momy ta zauna a bakin gado tare da yin tagumi a fili tace "to me ya sami Zainab ?kodai ta gudu uban nata zeyi mata auran dole ne ?tana tsaka da tunani taji Affan na cewa "momy nadawo daga masallaci sai da safe "
Ba tare da ta tashi ba ,tace "Allah ya tashe mu lafiya my son ".
Koda Zainab ta kwanta sana'ar tata takeyi wato kuka ,sai dai yanzu babu ruwan hawaye sosai sai matsosu take amma sun ƙafe ,ga idanunta nayi mata zafi ,ta daɗe a haka batayi bacci ba har ƙarfe (1:10 am) na dare ,bata san lokacin da bacci ya ɗauketa ba.Washe gari ranar ta kasance Juma'a ,ranace da mutanen gidan suke breakfast ƙarfe (8:00am) taƙwas ,bayan sun yi sallah Zainab ta fito gaishe da momy ta samu bata ɗaki tana kitchen "kai tsaye Zainab ɗin ta bita kitchen tare da durƙusawa har ƙasa tace "momy barka da safiya "
Cike da farincikin ganin ɗiyar tata tace " daughter barka ina fatan kinyi bacci ya isheki ?"sadda kanta ƙasa tayi kana tace "eh momy nazo tayaki aiki ne "flaks ɗin ruwan zafi momy ta miƙo mata tare da cups guda uku tace "kai dinning " tom "Zainab tace takai dinning ta ajiye ta kuma dawowa ,a karo na biyu momy ta bata food flaks mai ɗauke da farfesun kayan ciki tace shima takai dinning ,daganan momy tace "an gama zanje wanka ki zauna ki fara ci ".
Batare da tayi musu ba taje ta ɗauko plets guda uku ta ajiye da cokali ta ɗauki guda ɗaya tasa kana ta haɗa tea ta ɗauki bredi .
Bata wani jima tana breakfast ɗinba ta kammala tare dayin hamdala ,tana shirin tashi Affan ya shigo cikin takunsa na ƙasaita zai zuba ƙamshi yake yace "keee ! ina momy ?" ko ɗago kai Zainab batayi ta kallesa ba tsawar daya daka mata ne yasa momy fitowa da sauri dan taɗan tsorata tace "lafiya Affan ?" yana wani cumo baki tare da harare -harare yace "momy wannan yarinyar nake tambaya ke amma bata bani amsa ba "murmishi momy tayi kana tace "ai ka fita sanin inda nake haba Affan yaushe zakayi hankali ? dole momy ta zauna shima Affan ɗin ya zauna ,dady daya fito yanzu suka gaishesa ya zauna sukayi breakfast , ganin Zainab bataci abinci ba ,yasa dady cewa "ƴata meyasa bakici abinci ba ?"kanta a ƙasa tace "dady ai tun ɗazu naci "
"Ok "
Dady yace "kana ya kalli Affan yace "yau bazakaje hospital ɗin bane ? " Zani " Affan ya faɗa kai tsaye ,inda abin da ya tsana bai wuce zuwansa aiki ba ,yafison a nemo a bashi yaci dady na gama yi masa magana yayi musu sallama ya fice.
Zuwa ƙarfe (10:am) Zainab tayi wanka ta taya momy gyara gidan suka dawo palo suka zauna , cikin sigar lallashi da ɗan tsokana momy tace "my daughter me yake saki kuka ko yanzu alhinin mutuwar mamanne ?" Zainab da kanar jira take , ta ɗago kai ta kalli momy ta fashe da kuka ,bayan ta share hawayenne tace "momy baba ...baba ... cikin rashin fahimta momy tace "to me baba yayi ?cikin kuka Zainab tace "momy akwai wata rana , lokacin watan mama biyar da rasuwa .