5-6

15 1 0
                                    

🪂🪂🪂🪂🪂🪂
*SAHIBUL AMRAT*

🕊️👑🤺🎺

*Zainab Habib(Mom Islam*






_____________________5-6

Itama momy tayi murmishi kana tace "aikuwa nagode "sukasa dariya .
sai da akayi isha'i sannan dady ya shigo ,kai tsaye bedroom ɗin momy ya wuce ya sameta zaune a kan sallaya tana adu'a , sai da ta shafa shima ya shafa sannan tayi masa sannu da dawowa yace mata yawwa , sukaɗan taɓa hira ta shiga toilet ta haɗawa dady ruwan wanka ya shiga .
Bayan ya fito ta taimaka masa ya shafa mai ta ciro masa kayansa yasa ta fashe shi da turare mai ƙamshi suka fito a tare ,cike da soyayyarsu wacce ko kaɗan bata tsufa .

*ƊAN ƊANO*
Bayan shekara 19
Wata hamshaƙiyar mota fara ƙirar Bugatti Chiron: 261 mph. ce ke sharara gudu a tsakiyar titin Hanwa low-cost , baƙar mota ce mai ɗauke da baƙin gilashi , yayinda wasu motoci haɗaɗɗu sharon guda biyu ke biye da motar , gudu suke sosai kamar zasu tashi sama , motar dake tsakiya ce taɗan rage gudu , leƙawa nayi na hango wani farin saurayi amma ba fari sosai ba , yana ɗauke da fararen idanuwa gashin kansa baƙi sosai gashi kamar na larabawa hancinsa dogo shi kansa yana da tsayi amma madai-daici yana da faffaɗan ƙirji ,shafo baƙin sajen fuskarsa ɗan rausayar da kansa kafin ya kalli wayarsa ƙirar iPhone 13 ya duba agogo ,ƙarfe(4:00 pm) na yamma ya gani kana ya mayar da wayar tasa aljihu kafin yace "Abdallah kaini gidan gona mu juya "an gama ranka shi daɗe Allah ya taimaki yarima mai jiran gado "Abdallah yace tare da juya akalar motar zuwa tudun wada ,motocin dake biye dasu a baya suma suka juya tare da bin bayansu , a wata anguwa sukayi parking motocinsu gaban wani farin get ,horn sukayi get man ɗin yazo da gudu ya buɗe musu , motar tsakiya ce ta fara shigewa mai gadi har ƙasa ya durƙusa yana cewa ɗan sarki jikan sarki Allah ya taimaki yarima mai adalci "murmishi kawai saurayin yayi kana suka tsaya a gurin ajiye motoci , bayan an yi parking aka buɗewa prince Khalil mota ,ya ziro kyawawan fararen ƙafafuwansa wanda suke cikin takalmin sarauta , gyara zaman alkyabbar jikinsa yayi kana ya juya ya kalli dogawaransa da suke masa kirari ya kalli Abdallah wato abokinsa da ya zamo masa driver a yanzu yace "bana buƙatar a biyoni Abdallah muje ciki "ci gaba da kirarin sukaci gaba dayi har prince Khalil ya ɓace daga ganinsu ma'ana sun shige ciki.
Da shigarsu Abdallah ya janyo wata haɗaɗɗiyar kujera mai ɗauke da sunan prince Khalil yace "ogana ka zauna man "sai da prince Khalil ya gama isa da taƙamarsa wacce kowa yasansa da hakan sannan ya zauna kafin yace "bismillah"
Wannan hali na prince Khalil yana birge mutane musamman ma mahaifinsa mai martaba abu ɗaya ne yasa mai martaba yake yawan yi masa faɗa shine , yayi aure yaƙi yayi dan har sun fara shawarar haɗashi da wata yarinyar ƙanin mahaifiyarsa shikuma yace a'a Allah ya taimakesa maganar bata isa gurin sarki ba .
Abdallah ne ya kalli Khalil kana yace "prince ya maganar Hindu ne "rai a ɓace prince ya kalli Abdallah kana yace "pls karka taramin zafin kai ba wannan maganar nakeson muyi ba so kayimin shiru ".
Murmushi Abdallah yayi wanda yasan dole suyi faɗa tunda ya takaloshi akan maganar ,
Prince ya kalli agogon hannunsa kana ya ɗan lumshe ido sbda iskar dake ɗan kaɗashi yana jin daɗi kafin yace "Abdallah so nake ka rakani gidan marayu akwai abinda zanyi a can so daga nan sai mu koma gida " tom an gama prince nawa "Abdallah yace "yana murmishi .
A hankali prince ya miƙe shima Abdallah ya miƙe suna fitowa prince yakai dubansa ga dogarai yace "zamuje anguwa so inaso ku koma gida" da sauri suka kalleshi kasancewar a durƙushe suke sukace "Allah ya taimaki yarima mai martaba yace "mu daina barinka kana fita kai kaɗai saboda abinda ya faru rannan "Abdallah dai yana gefe yana gudun yayi magana a tsigeshi , sai da prince ya ɗauki tsawon lokaci kafin yace "yanzu dai bazaku iya tafiya ba kenan "da sauri suka kuma sadda kansu ƙasa kana sukace Allah ya taimaki yarima umarninka zamubi "Abdallah yace "a kira da security "harara prince ya gallawa Abdull wacce ta sashi sunkuyar da kai nan da nan dogarai suka shiga mota suka bar gurin .
Bayan tafiyarsu prince ya kalli Abdull fuska a tamke yace "wai ni ƙaramin yaro ne da zasu sani a gaba suna gadi ?"kai kuma kaci gaba ".
Ya nuna Abdull .
Ba tare da Abdull ya kulasa ba ya shiga mota mazaunin driver shima prince ya shiga ɗayan side ɗin suka bar gurin , gaban wani katafaren plaza prince yasa akayi parking yace "Abdallah ya siyo duk wani abu da marayu suke da buƙata "cikin bin umarni prince yace "an gama "ya fito ,ganin prince ɗin ya fito shima yasa Abdallah cewa "haba ka koma man "no nima zanga gari "prince ya faɗa fuska a tamke "haka suka jera cikin harabar gurin suka shiga plaza ga mamakinsa bai san kaf mutanen gurin ba amma sai ji yayi ana cewa "ga yaron sarkin garinnan mai yawan zuwa gidan marayu ai ana nunoshi talabijin "kan prince a sunkuye Abdallah ne ke ƙare musu kallo har suka shiga cikin shagon , Abdallah ya fara lisaafa abubuwan da akeda buƙata , bayan an gama loda musu a bayan mota prince ya biya kuɗin suka fito dan shiga mota , karo sukaci da wata yarinya doguwa bata da ƙiba tana da kyan diri gata da hips da pink lips gashin idonta ya ɗanyi ja yayinda gashin girarta yake baƙi wuluk ,ikon Allah kenan .
Wayar dake hannunta ƙirar Gionee mai ɗan ƙaramin kuɗi wanda a ƙalla zaiyi 20k .
Faɗuwar da wayar budurwar tayi ne ya sata waro kyawawan idanuwanta tare da ɗorasu a na prince ,tashi ɗaya ta tako daf dashi tana huci suna iya jiyo nunfashin juna tace "sai na nuna maka kai ɗan ƙaramin ɗan iska ne !" da sauri Abdallah yace "ke bakisan ko dawa kike magana ba koh ? tsaki budurwar tayi kana tace "ba damuwata bane insan koshi waye amma wannan wayar daka lalata wlhi sai ka biyata ko in nuna maka inda ake tashanci " tunda ta fara magana prince ke kallonta yana wani killer smile tashi ɗaya ya dake yaja da baya kana yace "Abdull muje kawai " da gudu tabi bayansu cikin rashin sa'a har suka kai ka shiga mota suka rufe bata cimmasu ba ta bugi gilashin motar da hannunta kana tace "wlhi kokai waye kaci bashi " taci gaba da tafiya idonta yayi jajir kamar tayi kuka , a hankali suka dinga tafiya har sai da sukaga gidan data shiga sannan prince yace su wuce .
Sun kusa zuwa gida wayar prince ta fara ring , da sauri ya ɗaga cikin girmamawa yace "tuba nake mai martaba insha Allah bazan ƙara ba " sai kuma naga ya ajiye wayar ransa a jagule ,
Abdallah yasan a halin yanzu koda ya tambayi prince bazai faɗa masa abinda ya faru ba sai dai dan kansa in yaso .
A wani katafaren gida naga Abdull yayi parking gidane da ganinsa kasan gidan sarauta ne , duba da yanayin zane irin sarauta tun daga wajen gidan har i zuwa ciki ko ina yana ɗauke da tambari irin na sarauta , kirarin da ake musu ne yasa Abdull tafiya a hankali yana amsawa fuska a sake ,yayinda shi kansa yariman fuskarsa take a tamke babu alamun wasa ,dama yawan fara 'a ba aikinsa bane ko yawan magana miskilanci yafi masa yawa .
A hankali suka ƙarasa ciki naga Abdull yayi parking a inda aka tanadar dan ajiye motoci ,yana zuro ƙafafuwansa dogarawa suka fara yi masa kirari suna cewa "Allah ya ƙarawa yarima lafiya ɗan sarki jikan sarki .
Ko uffan baice musu ba ya wuce kai tsaye fadar mai martaba , a bakin ƙofar ya ƙirƙiro murmishin dole kana ya shafa fuskarsa tun daga goshinsa har haɓarsa tare da yin sallama .
Da shigarsa dogarawan dasuke zaune suka fara kwasar gaisuwa ,amsawa sukayi ciki harda mai martaba ya sadda kansa ƙasa ya kwashi gaisuwa gurin mai martaba kana shiru yaɗan biyo baya .
"To Alhmdulilh dama maganar da nakeson yi dakai shine , mai yasa kakeson fita kai kaɗai alhali kasan hatsari ne yin hakan ?"
Kan prince a ƙasa yace "tuba nake Abbana insha Allah bazan sake ba "
Murmishi mai martaba yayi wanda ba lallai ne ka gano hakan ba ,sbda rawani daya rufe masa ilahirin gefen fuskarsa "zaka iya tafiya " mai martaba yace yana kallon Yarima Khalil .
A hankali prince ya tashi tare da ɗan sadda kansa yace "na barka lafiya ya Abbana " prince ya fita.

Wani gida naga ta shiga ,gidane madai-daici yana ɗauke da ɗakuna uku daga gefe kuma wata matace wacce a ƙalla zatayi 40yrs tana sanye da dogon wando na jeans hannunta riƙe da kuɗaɗe masu yawa , shigowar budurwar da tayi ne da gudu yasa datijuwar cewa shamsiyya mai ya faru na ganki haka ? wacce aka kira da Shamsiya tana huci tare da cuno baki tace "mama wani saurayi ne ya bigeni na fasa wayata nayi ƙoƙarin binsa ya gudu "tsaki maman tayi kana tace "ke nifa banason ki dinga yawan fushi inhar waya ce sai wacce kika zaɓa amma kafin muci gaba da magana inaso kiyi sauri kije ki sallami alhaji Ubaid "waro ido tayi tare da dafe goshi kana tace "ni walhi bani son zuwansa mama dan Allah kice bana nan " waro ido maman tayi kana tace "ai kuwa baki isa ba ,ko kije ki bashi abinda yake nema ko inci miki mutunci "wata budurwa ce ta fito daga ɗakin dake kallon nasu tana ɗan yamutsa fuska tace "mama Sadiƙ fa yana ƙofar gida kuma yau dai Allah yayi taimako zai ƙaramin 20k ya zamo 50k "tafawa sukayi da maman tace "yawwa ƴar gari kinga irin abin da nakeso gashi ita wannan tana neman wancan attajirin ya gudu mana "ɗagawa budurwar hannu mama tayi kana tace "baby a dawo lafiya "
Da ƙyar Shamsiya ta yarda da zuwa gurin Alhji Ubaid sbda bata ƙaunar irin kwashen mutane haka ,hannunta mama taja tare da kaita wani ɗaki ,ɗakin cike yake da kayan kwalliya da kayan sawa kama daga turaruka mayuka da shu'umar humra da idonka idona da sauransu ,
Tasha mutsika aka sauya mata kaya i zuwa shadda ruwan madara tasha aiki ja tayi kyau sosai tasa mayafi ja da takalmi ta fito ,ganin fuskar babu fara'a yasa mama cewa "haba shamagirl ki ɗayi murmishi man "murmishi tayi badan taso ba wanda yasa point ɗinta dake kumatu loɓawa ta wuce gurin Alhji Ubaid ,tana shiga ta samesa zaune kan sofa wacce inhar sunyi baƙi to ɗakuna biyu nasu ne koda kwana zasuyi , hannunsa riƙe da kofin gilashi yana shan ruwa , jin shigowarta ya sashi ajiye cup ɗin hannunsa yaje da sauri ya rungumeta kasancewer shi ba wani mai ƙiɓa bane amma yana da ɗan jiki badai irin sosai ɗinnan ba, fuskarta a ƙirjinsa ta ɗan...!

Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud'inki ta wannan account d'in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224

Idan kuma kati ne zaki d'auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224 y'an Niger suyi magana ta wannan number +22784506476 .

MOM ISLAM

SAHIBUL AMRATOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz