13-14

21 1 21
                                    

15-16

Ammi tace "amma mai martaba yasan da fitarka ?"prince ya sunkuyar da kai kana yace afuwan Ammi, yana shirin ƙarayin magana yaga kiran baby da tsabar sauri bai tambayi sunanta ba ,amma yayi saving da Boss , ƙin ɗaga wayar yayi har sai da akayi kira uku sannan Ammi ta kai dubanta ga aljihunsa da wayarsa take kawo haske kafin tace ",Babana waye yake kiranka ?"prince yayi murmishi wanda ya ƙarawa fuskarsa kyau yace Ammi zan ɗaga ,Ammi dai tana zargin kamar dai budurwar tasa ce take kiransa ba ,Ammi ta miƙe tana dariya tabar gurin.
Ammi na komawa can ɗakinta prince ya bi kiran da baby tayi masa kafin yace "ya akayi ?"baby ta fara magana ƙasa-ƙasa tana cewa "Yarima anyi nasara dan nabi ta hannun mamanmu ne kuma tama yarda kaidai yau kazo sai ku gama komai ta kashe wayar.
Bata jira prince ya bata amsa ba.
A hanzarce ya miƙe ya fita daga ɗakin dogarawa nata kwasar gaisuwa ya wuce ɗakinsa ya samu an jera masa kayan abinci iri-iri , gefe kuma Iyami ce zaune , mugun kallo yayi mata kafin yace "tunda munafurcin bai kaiki ga nasara ba sai ki barmin ɗaki ,daga yau karki sake biyowa hanyar ɗakinnan ba Rabi ba koma waye ya aikoki " Baiwa Iyami ta miƙe tare da ficewa da gudu har tana tuntuɓe.
Kai tsaye side ɗin Hajiya Rabi tayi tana zuwa ta zube ta kwashi gaisuwa kafin ta fara magana tana sauke numfarfashi tace "Allah ya taimakeki Yarima ne ya koroni harda zaginki ta uwa ta uba "Hjya Rabi ta tashi daga kishingiɗen da take ta gyara zama ta kalli jakadiyarta kana tace "kumafa zai aikata "Jakadiyar tace "Allah ya taimakeki karki kulashi suna neman masifa ne shida uwarshi tunda kinyi gaba kin fisu ko a gurin mai martaba ki ƙyalesu "wannan maganar ta Jakadiya tayi tasiri a gurin Hjya Rabi har ta haƙura.
Washe gari ƙarfe 7:40 pm a masallacin anguwarsu baby yayiwa prince shi kaɗai ya fito ko Abdullah bai saurara ba ,yana fitowa ya kira baby yace gashi a ƙofar gida , ɗakin kayan kwalliyarsu ta shiga ta gyara jikinta da turaruka da mayuka masu ƙamshi masu ɗaukar hankali .
Tana fitowa prince ya ƙare mata kallo a zuciyarsa yace "wannan kayan dashi da babu duk ɗaya riga da siket na atamfa amma kamar zai yage , fitowar Shamsiya ne ya katse masa tunaninsa ya kai kaice kai yana wurga mata ƴar harara Allah yasa bata lura dashi ba, baby ta koma gida , cikin sigar wayewa pince yace "habba babbar yarinya ya kike yimin haka ne ?koda wane lokaci nazo sai kiƙi fitowa "a zuciyarsa yace kamar gaske " Shamsiya dake sanye da riga da zani na atamfa d hijab iya guwaiwar ƙafarta ta gaishesa da fari kana tace "kazo kawomin wayata daka lalata ne ?
Prince yace "abinda yafi waya ma zan baki insha Allah nidai in sami gurin zama a cikin zuciyarki shi nake buri mu kasnce abokan rayuwa " Shamsiyya tayi ajiyar zuciya kafin tace ....!

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 15, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SAHIBUL AMRATWhere stories live. Discover now