"I lose my own children, which kind of father is these? Ni ne na haife su, na raine su tun suna jarirai, amma akan wani ƙaramin dalili zan kawo yarana cikin wata uwa duniya cikin jejin da yake da mugwayen Animals na zube? What exactly wrong with me? Wallahi ina jin na haukace, i can't live without my children in sha Allah I'll bring them back to my house, ko mene zai samu su ya same mu tare" Ya faɗa yana share hawayen dake cikin idanuna, kafin a hankali yaywa motar key tare da reves ya juya baya zuwa cikin jejin. Almost 20mints yana driving cikin jejin inda yake effecting ganinsu, amma babu su babu alamar su, tsananin tashin hankali ya wanzu kan kamilalliyar fuskarsa wanda zuwa yanzu ya zame hiramin da ya yi covering face nasa dashi.. he was shock ganin baya iya gane ko inda ya zube su, balle ya gansu a wajan, yana matsanancin tausayin yaransa, Sairah nada hqr, ko ina taje za taci ribar zama da hqrin ta, Sara asalin mara kirki ce, ga baƙar zuciya, amma duk abinda da take sai an taɓa ƴar uwarta Sairah ne, idan ita kayiwa ko kallonka ba Zatai ba, amma kana taɓa Sairah za kaga ruwan bala'i.. parking ya yi cikin jejin tare da fitowa waje yana ƙara sakin wani irin raunataccen kuka mai tsuma zuciyar dukkan mai sauraran sa, bai taɓa zubar da hawaye ba tunda yake sai yanzu, yana da rauni akan Twins ɗin sa. Juyawa ya dinga yi yana kiran sunansa "Sara! Sairah! Sara! Sairah!" Shiru no respond, kamar daga sama ya hanki hijibin dake jikin Sara a yashe a ƙasa, gaba ɗaya jini ya ɓata sa, cikin tashin hankali ya zube a wajan tare da faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shi ke nan, na kashe yarana da kai na, Wata dabbar ta cinye min Twins" ya faɗa yana sakin kuka, kafin kuma ya fara sakin wasu surutai alamar ya fara samun matsala a ƙwaƙwalwarsa, haka ya ƙanƙame hijibin yana kuka tamkar ransa zai fita, dama Uba na gari na iya wufintar da yaran daya haifa da ƙwayayan haihuwar da Ubangiji ya dasa masa?....
A ƙasan wata bishiya suke a zaune, gaba ɗaya Sara bata hayyacinta wani irin tari take jini na zuba daga bakinta, duk yadda tasu ta samu kwari ta nunawa Sairah ba komai, amma hakan ya gagara, cikin tashin hankali Sairah ta riƙe Sara tace "mene yake maki ciwo twin na?" Numfashi Sara taja da ƙyar tace "Ba komai, kawai naji ƙirji na ya yi min nauyi ne, stop cry twin noting will happen to me, kukan ki shine damuwa ta" ta faɗa tana kama hannun Sairah, tare da share mata hawayen dake bin fuskarta... Girgiza kai Sairah tayi tace "Haba twin, taya hankali ne zai kwanta, bana mance time ɗin da muna primary school na nemi na rasa kuma a lokacin baki da lafiya, kina fama da ciwon ƙoda daga ni har Daddy babu wanda kika faɗawa, a kiɗime muka je hospital ɗin, muna zuwa Dr yace mana an ƙodar gaba ɗaya biyun sun lalace, amma wani saurayi ya bada tasa an cira an saka maki, munce masa waye amma Dr yace shima bai san shi ba, Yanzu haka silarsa yasa kike raye a duniya da kuma taimakon Ubangiji, duk da hakan kike tunanin hankalina zai kwanta? Ko kuma kina tunanin ke kaɗai kike so na? Sara a mahaifa guda aka haife mu, dole Soyayyar junanmu da kasance abu nada ban, ina Sonki ba zan iya bari na rasa ki ba" Sairah ta ƙare zan can tana sakin kuka, ganin yadda hankalin Sairah yay masifar tashi, yasa Sara ta saki wani Murmushin ƙarfin hali, tana danne wani tarin da yazo mata, tace "Haba twin akan wannan kike kuka? Haɓo nayi fa" Sairah tace "No Sara, stop laying baki ƙarya kada ki fara yanzu, Meke damunki, saboda Daddy ya barmu a nan? Kasan dole zai dawo ba zai iya rayuwa babu mu ba, ƙilan yana da wata manufa daya sanya ya yi hakan" shiru kawai Sara tayi domin muguwar zuciya ce da ita, a halin da take yanzu bata ƙaunar ma, a kira mata sunan Daddy, wanda yake son su da ƙaunar su yau shine ya juya musu baya, akwai kidnappers, Arms robber, bad Animals duk a ciki jejin duk da haka ya tsallake ya tafi ya barsu.... Kallon Sairah tayi da tayi lamo a jikinta tana sauke ajjiyar zuciya, a hankali tace "Twin da gaske ba Daddy ya haife mu ba" da sauri Sairah tace "A'a shine Daddynmu shine ya haife mu" gyara zama sosai Sara tayi tace "Look twin kin san bana ƙarya ko?" Slowly Sairah ta ɗaga kanta, Sara tace "Good, as frm today zamu daina amfani da sunan Daddy, na maki Al'ƙawari, zan zame maki fiye da Daddy, da kuma uwar da muka rasa, tun muna ciki, zan baki farin ciki ko da zan rasa nawa, ki daina kuka kinji babu abinda zai same mu sai abinda Ubangiji ya tsara" Sairah tace "Twin to me zamu na cewa sunanmu?" A hankali Sara tace "I'll think about that.... sleep" ta faɗa tana ɗura kan Sairah a cinyarta, kwaɓe fuska Sairah tayi tace "I luv u twin" Sara tace "Luv u too..." Sanyin safiyar daya shiga kaɗawa shine ya farkar da Sara daga baccin da take, tana farkawa idanunta ya sauka akan Sairah wacce take zaune ta zabga tagumi tana kallon ƴar uwarta, da mmki Sara tace "Mene?" Girgiza Sairah tayi tace "naga baki tashi ba, ina tsoro ne" Sara tace "yanzu fa" Murmushi Sairah tayi tace "Naji daɗi" Miƙewa duk sukai, suka fara tunanin inda zasu samu ruwan alwala, hannun juna suka riƙe suka shiga tafiya cikin jejin cike da tsoro ƙarar ƙwari da dabbobi sun cika ko'ina, a haka suka isa wata gaɓar ruwa nan sukai alwala, Sairah ta kunce ɗan kwalinta ta shimfiɗa, kana ta yi sallah tana idarwa ta bawa Sara hijib tunda nata ya Faɗi.. shiru duk sukai banda yunwa babu abinda suke ji, juyawa Sara tayi jin cikin Sairah na ƙara, a hankali ta miƙe tsaye tace "twin tsaya a nan ina zuwa" tana faɗin hakan ta bar wajan, wajan ruwan ta koma tayiwa ruwan ƙuri da idanu can ta hangi wani ɗan ƙaramin kifi a gefen ruwan yana tsalle, da sauri ta ƙarasa ba wani tsoro ta kama kifin ta ajjiye can nesa har ya mutu, tana da tsaye ko zata ƙara ganin wani kifin amma babu, juyawa tayi ta hada itace kamar yadda taga anayi a film, ta samu fararen duwatsu nan take wuta ya tashi, a nan ta fasa kifin sai farin ciki take Sairah zata samu abinda za taci.... Kifin ta ɗauka har zuwa wajan Sairah ta same ta kwance riƙe da ciki, da sauri tace "Twin come and eat fish" ta faɗa tana ɗura kifin akan wani leaf mai faɗi, jikin Sairah har rawa yake saboda yunwa, tace "Sara na kema kici to" girgiza kai Sara tayi tace "Ai naci, nawa ma yafi naki yawa" ta faɗi hakan ne domin tasan kifin ko Sairah ba zai isa ba, balle su biyun duk da cewa itama tana jin matsanancin yunwa, da kallo kawai tafi Sairah yawunta na tsinkewa, ganin yunwa zata kashe ta, yasa ta miƙe tayi baya can, wani kuren ganye ga gani mai kyau ga ruwa duk a jikinsa, da sauri ta tsinka ta shiga ci kamar mayunwaciya, sai da taci gayen da yawa Sannan ta goge bakinta, ta koma wajan Sairah lokacin harta gama cinye kifin, Murmushi tayi tace "Taso mu tafi" Sairah tace "where?" Sara tace "muje ko zamu samu wani garin a gaba" tafiya suka fara hannunsu riƙe dana juna...
A can Mascow Abeed ne zaune, a gaban Dr siya, yana sauraran abinda yake faɗa, gaba ɗaya a tsorace Dr Siya yake, domin gani yake kamar Zain ne ba Abeed ba, duba da cewa komai nasu iri guda ne, babu wani bambanci, shigarsu, magana everything... Taɓe fuska Abeed ya yi, kafin a hankali ya ɗan ja numfashi, kamar wanda akaiwa dole yace "Uhm all ears" Dr Siya yace "Har kawo yanzu babu wani magani da aka samu na ciwonka, kuma binciken ya ƙara tabbatarwa Tabbas ba zaka shige wata biyar ba a raye,but..." Hannu Abeed ya ɗaga masa alamar ya isa haka, Miƙewa kawai ya yi tare da gyara zaman mars ɗinsa ya fita daga office ɗin, ko maganin da Dr Siya ya bashi bai amsa ba, a ganinsa shi da yake dab da mutuwa wanne magani kuma zai sha?. A hankali yake tafiya cike da nutsuwa he was so weak and sick, mota ya shiga ya yi mata key ya koma cikin hotel ɗin...Zain ne zaune da wani three gauther sai Red ɗin Armless, yana vedio call da Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas, Murmushi Zain yay yace "Gashi ya dawo" A hankali Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas dake zaune kan wata tattausar ladduma gabansa cike da kayan marmari, yana tsaye da wata farar jallabiya mai kyau wacce tasha aiki irin ta sarakai, ga wata jar hula a kansa mai ɗan tsayi, wani ƙawataccen Murmushi Ya saki yace "Nuna min fuskarsa" Cikin e Sauri Zain ya saka hannu ya jawo Abeed dake tsaye yana sauraran abinda suke faɗa, zama yay kusa da Zain ya ɗan ɗura kansa a kafaɗar Zain ɗin, wani irin marairaicewa Abeed ya yi tare da ɗan kwaɓe fuska cikin Muryar shagwaɓa yace "Abba" wata mummunar faɗuwar gaba ce ta saukarwa Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas wacce bai san ko tame bace, addu'a ya yi kafin yace "Are You alright?" Shiru Abeed ya yi sai kallon mahaifinsa yake, can yace "Ina Naila?" Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace "gata" ya faɗa yana hasko fuskar Naila da sauri tace "Muhammadur Rasulullah s.a.w, Jama'ar Annabi yau ga gantalallun yara masu son cutata, a'a wlh Ubangiji yay min tsari daku, maza ku bambance min kanku" Dry Zain yay kafin yace "Nine Abeed, wan can kuma Zain" washe baki tayi tace "Yau koda naji, ai tunda naga wan can yana zare ido kamar na gafiya nasan billahi ba shine Abidin ɗin ba" Murmushi kawai Abeed ya yi ganin yadda har yanzu ta kasa gane su, Zain yace "Naila ya tsofa?" Da sauri tace "A'a wallahi mugun nufinka ya ƙare a kanka, wani garin ne kuma tsofa? Kai dan kaji wallahi sai dai ka mutu ka barni a raye" dry sosai Zain yay yace "Ai ke yanzu kina tunanin kaiwa wani lokaci mai tsayi haka? To ai bana jin ko wata biyar zaki kai a raye?" Da sauri Abeed ya kalli Zain gabansa na ƙara faɗuwa, mene ya sanya suke maganar mutuwa ne? Ko dai ya tabbata cewa zai mutu ne? Haɗe fuska Naila tayi tace "Wlh ba zan mutu ba, idan na mutu Allah ya tsine.." da sauri Abeed ya miƙe tare da barin wajan ya shige cikin bedroom zuciyarsa na tsananin harbawa, Meke faruwa ne? Yanzu ne lokacin daya dace ya bawa kansa farin ciki tunda ya tabbatar Ubangiji bai ƙaddara zai yi rayuwa mai tsayi ba, yanzu wacce hanya zai bi ya samu farin ciki? Wata zuciyar tace masa kawai kayi rayuwa mai ƴan a hankali ya buɗe baki yace "Club.....
Wattpad ya baku comments da vote ne😰
YOU ARE READING
ZAIN_ABEED
RomanceLabarin wasu tagwaye, maza da mata. Ɗaya mawaƙi, ɗaya lawyer, yayinda matan kuma Sarah, da Sairah suka kasance ƴan ƙauye kuma abokan hamayya wa junansu. Meke kawo su cikin Masarautar su Aberdeen? Uhm! Labarin daman yake, ba kamar sauran ba.