4

457 14 2
                                    


Mutanan masu kama da arnan daji sabis yanayi kirarsu da kuma halayya, sune suka ɗauki Sara wacce ko kuka ta kasa yi sai wata wahalalliyar ajjiyar zuciya take saukewa, she wish ace Ubangiji ya ɗauki ranta a yanzu, babu Abinda yake damunta kamar halin da biyuninta Sairah zata shiga, tana can tana jiran ta kawo mata abinci, ga wata ƙaddarar ta faɗa mata, bayan ƙaddarar data sanya Mahaifin daya haifesu da cikinsu shine sanadin faruwar hakan, da ace bai kawo su jeji ya zube ba, ya jasu a ciki kamar yadda ya saba, babu dalilin da zai saya su shiga wannan wahalalliyar rayuwar, a yanzu babu abinda ta tsana a duniya sama da Mahaifin daya haifeta....Gaba ɗaya kan doki suka hau yayinda ɗaya daga cikinsu ya saba Sara a ka faɗa suka juya tare da nufar cikin gari, tafiya sukai mai nisa har suka iso ƙofar shiga wata ƙatuwar masarauta mai suna *Zahel* Masarautar Zahel Masarauta ce mai ƙarfi, wacce ta shahara a ɓangaren tsafi, Masarautar ta gino a can baya wajan Shekara ta 2,000 da doriya da suka gabata, Masarautar Zahel sun ƙware wajan bautar Gumaka, Dodo, Rana, Ɗan-maraki...Domin girma ne da masarautar saboda girman ta ne yasa suke tunanin samar da sarakuna guda biyu, amma tsananin tashin hankali da son zuciya yasa komai ya gagara, har kawo lokacin da Sarki Mabus ya hau kan kara ga, mutum ne mai ƙarfin iko, wanda ko kallonka ya yi sai da dalili, babu ruwansa da sabo, duk yadda kuke dashi idan Dodo ya buƙaci jininka bashi zai, gashi da mahaukacin kuɗi wanda ba kowa yasan inda yake samu su ba, Yana da mata sama da 20, banda ƴan matan da yake duk wata ya kwanta dasu, idan Allah ya yi a lokacin Dodo ya buƙaci jinin budurwa yana gamawa da ita, zai bada jininta.. Yanzu haka ƴan mata ne sukai ƙaranci a cikin Masarautar babu wanda zai kwanta dasu babu wanda zai bada jininsu a bisa wannan Dalili ya baza dakarunsa wajan samo masa mata, shine sukai katari da Sara.. Sarki Mabus na zaune akan karaga daga shi sai wani ƙaramin abu ɗaya ɗaure ƙugunsa dashi sai wata babbar laya a ƙirjinsa, da wata ƙatuwar wular fata akansa, fuskar nan tasa baƙa ƙirin kamar yadda zuciyarsa take ɓaka, sai muzurai yake gefensa kuma ƙaton wani gunki ne wanda aka ajjiye a cikin fadar na musamman... Ɗaya daga cikin dakarun da suka kama Sara ne ya shigo cikin fadar tare da zubewa a wajan, ya buɗe baki zai masa kirari Mabus yay saurin ɗaga masa hannu alamar ya dagata, cikin wata kakkausar murya yace "Kun samo?" Jikin Badakaren na rawa yace "Ai mana afuwa, munyi neman duniya a wannan gari na Zahel babu wasu ƴan mata face raguwar ƴan matan da suka rage mana a cikin Masarauta, Amma munyi karo da wata ƙyakkyawar budurwa a cikin jejin Zahel, idan ka bamu dama yanzu mu shigo da ita" Mabus ya kalli Badakaren jin yace "ƙyakkyawar budurwa, yasan gaba ɗaya ƴan matan Zahel baƙaƙe ne, amma wacce halitta ce take rayuwa cikin jejin Zahel kuma budurwa ƙyakƙyawa? Kada fa yana zaune a wargatsa masa sihirin da yake jikinsa na shekara da shekaru, kada a hanashi shiga cikin gari ya aiwatar da abinda ya saba, a fili kuma yace "Ƙyakkyawar budurwa fara?" Badakaren yace "Na rantse da abar bauta kabas ƙyakƙyawa ce, ban taɓa ganin mai kyanta a wannan garin na Zahel ba" Miƙewa Mabus ya yi yana zagaye cikin Fadar tasa, kafin yace "A shigo da ita" fita Badakaren ya yi babu jimawa, suka shigo da Sara wacce take ɗaure da igiya ta galabata sosai, wata zabura Mabus ya yi lokacin da idanunsa suka sauka akan ƙyakkyawar fuskar Sara wacce tai wani irin fari na wahala, gashinta mai matuƙar tsayi duk ya wargatse, "Gadiya ta tabbata ga Abin bauta kabas, kunce ta" Mabus ya faɗa yana mai kallon ɗan aikensa yace "Maza kira min boka" Da sauri ɗan aiken ya fita zuwa sashen da bokan masarautar Zahel ɗin yake.. Kunce Sara sukai wacce bata ma san abinda yake faruwa ba, sai bakinta da yake motsi a hankali tana faɗin "Twin Ruwa, Ruwa Twin" Kallo guda Mabus yaywa wani sai gashi ya dawo da wata ƙatuwar ana kamar kuttu, ya buɗe ya kafa a bakin Sara, da sauri ta janye bakinta tana girgiza kai saboda jin ba ruwa bane, Burkutu ce (Giya) A fusace Mabus ya miƙe tsaye tare da ɗauke mutumin da mari yace "Ubanwa yace ka bata Burkutu? La'ananne, Abin bauta kabas ya yi Allah wadai dakai, ku fice min" gaba ɗaya fita sukai, not too long Boka ya shigo tunda idanunsa ya sauka akan Sara yaji gabansa ya faɗi, wata zallar kama idanunsa suke hango masa a fuskarta wacce ya kasa fahimtar kamannin waye? Zama ya yi tare da gaida Mabus, Mabus yace "A kallo guda naji ina kwaɗayin yarinyar nan, ka duba min gobenta yanzu na gani ko akwai ni cikin ƙaddarar rayuwarta, ma'ana ka duba min Zanan ƙaddarar ta" Boka ya zube kayan aikinsa tsaf, hadda Madubin tsafinsa, Sara wacce ke kwance bayan an bata ruwa sai sauke numfashi take tana kiran sunan ƴar uwarta Sairah, ƙuri Boka ya yi mata da idanunsa, kafin ya kama miƙa hannu zai kama hannunta cikin sauri Mabus ya daka masa tsawa yace "Kada ka kuskura ka taɓa ta" Ya faɗi hakan yana matsawa kusa da Sara tare da kama hannunta ya nunawa bokan, sun jima a haka kafin bokan yace "Ya yi" Mabus yace "Labarta min me ka gani, yakai La'ananan boka?" Boka yace "Abu na farko, dole ka auri Yarinyar nan, auren ta shine zai kare ka daga sharrin wasu mazan da suke tunkaro ka, na biyu kuma Tabbas shigowar ta cikin Masarautar Zahel tsararran abu ne, ba ganganci ba, ka sani bakai ka kawo ta cikin Masarautar nan ba, Ita ta kawo kanta kamar yadda zanan ƙaddarar ta ya nuna, zaka samu ɗaukaka ta sanadin ta, wacce babu sarkin daya taɓa samu a masarautar Zahel, amma dole sai ka aureta, jininta ba zai taɓa shawowa a wajan Dodo ba, sai abu na ƙarshe wanda na kasa ganewa kuma shine mafi haɗari, amma zan ci gaba da dubawa tare da ƴan uwana bokaye" Jinjina Kai Sarki Mabus ya yi kana ya saki dariya yace "Dole ne ta zama Sarauniyar Zahel....

ZAIN_ABEEDWhere stories live. Discover now