Abeed na ƙoƙarin fita daga cikin ƙofar, Sara ta zame daga riƙon da yay mata kai tsaye kuma ta nufi ƙofar data fito tana kiran sunan "Twin" Abeed ji yay kamar an caka masa mashi a ƙahon zuciyarsa, tashin hankali ya shiga sosai, a hankali ya sanya hannunsa ya dafe forehead nasa dashi, wanda yake jin Tamkar zai rame gida biyu sbd tsananin ciwon da Yake masa, gashi Numfashinsa da ƙyar yake fita, hakan kuma ya fara taimakawa wajan tashin ciwon da yake fama dashi. Shiru yay yana kiran sunan Allah a zuciyarsa, azabar da ya keji a cikin jikinsa ba zai faɗo ba, sai wata zufa yake haɗawa jikinsa na wani irin vibration. Dattijo dake kulawa da yanayin Abeed yace "Muje kawai" sai a lokacin Abeed ya buɗe Manyan idanunsa da suka fara juyewa looking so sickness, kallon Dattijon yake ba tare da yace komai ba, Dattijon ya kama hannun Abeed ya fara tafiya dashi, kamar wanda aka tsikara yay tear out na maganar sa yace "kace zai mt wani abu?" Dattijo yace "Abin bauta kabas ya sahale masa kwanciya da ita, hakan kuma yana nufin ta zama matarsa" Abeed ji yay ya nemi raguwar numfashin nasa na wani lokaci ya rasa, Dattijo na ƙoƙarin magana Abeed ya zame hannunsa, ya nufi hanyar da yaga Sara tafi, yana tafe dafe da kansa. Sarki Mabus kamar yadda tsara yana zuwa yabi ta wani way wanda ba tanan ne yake bi ba, wannan dalilin ya sanya suka samu saɓani dasu Abeed, bedroom ɗin daya ajjiye Sara nan ya shigar da Sairah yana zaunar da ita yace "Duk jama'a ta ne a waje, kina fita za'a yanka ki" wani tsoro ya shiga zuciyar Sairah banda sunan Allah babu abinda take kira a Zuciyarta, Mabus kuma ya nufi wani sashe domin shirya wa, acewarsa zuwa na musamman zai mata. Sara kuma na barin wajan su Abeed ta shiga lalluban ɗaki, kana ganinta kasan ta samu prblm a cikin ƙwaƙwalwarta, tafiyar ma da ƙyar take, hakan ya sanya Abeed ya kusa cimmata, yana shigowa sashen tana shigewa wani bedroom, shi kuma kai tsaye ya miƙe zuwa sashen da Sarki Mabus ya ajjiye Sairah, Time Sairah tana zaune ta kasa ko motsawa banda kuka babu abinda take, motsin da taji yasa tayi saurin miƙewa tsaye, amma babu wanda ta gani kamar daga sama idanunta ya sauka akan wata wuƙa cikin sauri ta ɗauki wuƙar jikinta na rawa. Abeed dake tsaye nesa da ita tun shigowar sa shanyayyun idanunsa suka sauka a kanta, walking slowly ya nufi inda take kamar wanda aka tilasta wa, har daf da ita ya ƙarasa without making any sounds, shiyasa bama taji zuwan nasa ba, hannunsa guda ɗaya ya cire daga kansa ya ɗura a shoulder ɗin Sairah, Innalillahi wani irin ihu Sairah tayi tare da juyowa da sauri ta ɗaga wuƙar hannunta ta cakawa Abeed a cikinsa. "Ya Rabb" shine kalmar da Abeed ya samu damar furta wa, idanunsa akan SAIRAH wacce yay tunanin Sara ce, nan take kuma jini ya fara zuba daga jikinsa jiri na ɗaukan sa, daidai lokacin kuma Sara ta shigo ɗakin, duk da bata hayyacinta amma bai hanata ware idanunta ba, na mamakin ganin Sairah, ko zata mance da kowa banda twins ɗinta. Da ɗan saurin daya rage mata ta shiga cikin bedroom ɗin tana zuwa ta amshi wuƙar hannun Sairah wacce jini ya ɓata ta, daidai lokacin kuma Dattijo ya shigo cikin bedroom ɗin. A matuƙar kuɗi me ya nufi wajan Abeed wanda ya durƙoshe kan ƙafafuwan sa, idanunsa kuma suka shiga rufewa, cikin tashin hankali Dattijo yace "wace ta caka masa wuƙa a cikin su" Shiru Sairah tayi domin sai a lokacin da lura ba Sarki Mabus bane, Sara kuma bakinta ne ya kulle ba komai take iya cewa ba, wata ƙinƙina ta same ta, cikin tsawa Dattijon ya kuma cewa "nace wacece ta caka masa wuƙa a ciki?" Jikin Sairah na rawa ta ɗaga hannunta tare da nuna Sara, Kallon Sara Dattijon yay ga wuƙar nan a hannunta tana ɗigar da jini, Sara da mamakin ƴar uwarta ya kamata ta kasa cewa komai, bata taɓa tunanin a rayuwa Sairah zata iya aikata mata wani abu ba, sai gashi ta haɗata da sharrin da babu mai iya wanka ta, Sairah ta ƙara cewa "ban san me yay mata ba, amma tace idan har bata kashe sa ba hankalinta ba zai kwanta ba" slowly Sara ta dinga girgiza kanta, so take tace ba ita bace, amma ta kasa bakinta sai rawa yake, Dattijon yace "Kin aikata babban kuskure kuma zaki amshi hukuncin ki" yana faɗin hakan ya nufi wajan Abeed da ƙyar ya iya ɗaga sa, domin gaba ɗaya jikinsa ya saki, jansa ya fara yi zuwa waje, suna zuwa daidai inda Sara take Abeed ya miƙa hannunsa, tare da kama hannun Sara da kyau, yadda Dattijo ke jan Abeed haka Abeed ke jan Sara, har suka fita daga cikin sashen kana suka fita daga cikin Masarautar Zahel baki ɗaya..Suna fita Sairah ta saki ajjiyar zuciya, bata da wani zaɓi wanda ya shige tace ƴar uwarta ce ta aikata hakan, domin tasan idan tace itace babu shakka kasheta za'ai, bata taɓa tunanin zata ƙara ganin Sara ba, ashe itama tana gidan, babu mamaki da gayya ta tafi ta barta, fita tayi ɗaga daƙin ta fara tafiya babu jimawa ta haɗu da Kuyangin Gimbiya Noro Wanda ta aiko su duba mata Sairah, suna ganinta kuwa sukai wajan Gimbiya Noro da ita....Cikin ikon Allah inda Abeed ya ajjiye motarsa a nan suka sameta, babu abinda akai mata ba wanda ya lura da ita ma, Abeed wanda bai san me yake faruwa ba, domin ya jima da fita hayyacinsa, Dattijo ya samu wani ganye ya rufe wajan da yake zubar da jini kana ya ɗaure masa wajan da wani yadi, bayan motar ya buɗe ya saka Abeed kana ya saka Sara a gaba, shiga kuma ya shiga mazaunin driver da wani irin gudu yaja motar tare da nausawa cikin jejin ya ɗauki hanyar fita daka garin Zahel baki ɗaya....
YOU ARE READING
ZAIN_ABEED
RomanceLabarin wasu tagwaye, maza da mata. Ɗaya mawaƙi, ɗaya lawyer, yayinda matan kuma Sarah, da Sairah suka kasance ƴan ƙauye kuma abokan hamayya wa junansu. Meke kawo su cikin Masarautar su Aberdeen? Uhm! Labarin daman yake, ba kamar sauran ba.