6

462 16 2
                                    

“Kada a bari ta sake yi sallah, a cikin Masarautar Zahel” shine abinda boka yake faɗa, wanda a tunaninsu Dodo ne da kansa yake faɗin hakan, Sara shock da abinda taji ana faɗa, tana matsayin musulma za'a ce kada ta sake yin Sallah? What does that mean? Ka furta ta za suyi or what? Sarki Mabus yace "Akwai illa gayin dunguran nasu a cikin wannan masarauta ta Zahel?" Boka yace "Na rantse da Abin bauta kabas, duk sanda ta sake yin Sallah, Tabbas dubban mutane zasu halaka, a kullum tai sallah Abin bauta girgiza yake" Jinjina Kai Mabus ya yi kafin yace "Mene mafita, Wlh ina sonta kamar na lasheta hakan nan na keji, bana son a cutar da ita" Boka yace "Da acutar da ita, da kuma mulkin daka ƙafa bisa tsari da adalci ya wargatse fa?" Da mmki Mabus yace "kamarya?" Boka yace "Ina nufin, dukiyar ka zata halaka, kujerar mulkin ka zata zama bakai bane akai, gumaka zasu ƙone, garin Zahel zai shiga uku" cikin girgiza da tashin hankali Mabus yace "kutumar uba, na rantse da abin bauta, har gobe nine Sarkin Zahel, babu mutuwa a zanan lissafin ƙaddarata" ya faɗa idanunsa na juyawa, kafin a hankali ya juya wajan da Sara take tsaye kanta ƙasa, ƙirjinta na bugawa, tashin hankali tsoro ya bayyana saman fuskarta, bata son sha rauninta wannan dalilin ya sanya gaba ɗaya tayi ƙasa da kanta, wacce kalar masifa ko ƙaddara ce ke bibiyar Rayuwar su, Ina Twin take, mene makomarta...tana tsaka da tunani taji ance "Ke kice kin rantse da abin bauta kabas" shiru tayi deep down na Zuciyarta tana kiran sunan Allah akan ya kawo mata ɗauki, jin tayi shiru yasa Boka ya ƙara cewa "kic kin rantse da abin bauta kabas, kin daina sallah kin kafurta kin koma ƙabilar Zahel?"  A karo na farko ta ɗago jajayen idanunta wanda launinsu yay masifar sauya kala, kallon baku da hankali tayi musu, kafin a hankali ta kalli Sarki Mabus ta tofa masa yawo, cikin nutsuwa da kuma kakkausar murya mai kama da gargaɗi da kuma fansa tace. "Allah ya tsinewa Abin bautar daku, In sha Allah Ubangijin al'arshi wanda ya halicci ne, ya halicci ku, sai ya kawo ƙarshen ku, zuciyata cike take da soayyar Manzon Allah, wanda ake duniya domin da lahira, kuma albarkacin Baban faɗimatul-Zahrah sai na kuɓuta daga hannunku" Sarki Mabus ji ya yi kansa yana sarawa, babu abinda yake kalla a jikin irin ƙaramin bakinta, da yadda take magana a nutse, shi dai yana ganin soyayyarta itace rauninsa, cikin gargaɗi yace "kafin ke mun samu wasu, kuma ƙarshe mun aika ka su lahira, ta hanyar yanka wuyansu, ina gargaɗinki da ki gaggauta amsar addinin Zahel, wanda shine yake daidai ba naku addinin na Musulunci ba, idan addinin Musulunci shine daidai, mene ya sanya kuke zuwa wajan bokaye da mutunan tsubbu bayan kun san su ɗin ɓatattu ne?" Tafiya Sara ta dinga yi har zuwa gaban Mabus kamar ba zatai magana ba, sai kuma tace "Wacce buƙata wancan gunkin ya taɓa biya maka? Ubangiji na halittar Mutane da ƙyakkyawar zuciya, sharrin shaidan da kuma sharrin irinku wanda har yanzu ko kasa ajjiye Littafin Injila ko ɗauki Alqur'ani, shine yake sanya wasu nagartattun ɓata, na Aminci koda yanzu shine rayuwata ta ƙarshe ka bani dama nayi alwala nayi sallah na roƙi Ubangiji ya kare ni daga sharrin ku, kai ma kaje gaban gunkin naku wanda baya tsinana maku komai ka roƙesa akan ya kareka daga masifar da zata iya samunka, idan har wani abu bai sameka ba, ni kuma ban kuɓuta ba, zan tabbatar cewa nayi maku mubaya'a" girgiza kai Boka ya yi yace "wannan tatsuniya kike, musulmai nawa ne suke zuwa waje na, akan samun mulki, ko ɗaukaka, ko kuma kashe kishiya, sun san cewa ni ba musulmi bane, amma suna bina muna shirka tare,su da kansu sun tabbatar abinda nake gsky ne, kuma bisa sahalewar abin bauta kabas nake hakan..." Sara tace "Ohh really! Let's see,who win between i and you...,zan tabbatar maku cewa addinin musulunci shine addinin gaskiya, kuma Shine aka aiko Manzon Allah Sallallahu alaihi dashi bayan zuwan Annabi Isa Alaihissalam, ɗan Nana Maryama da yazo da Littafin Injila,idan duk kun amince a bani ruwa..." Sarki Mabus yace "a bata ruwa" boka ya girgiza kai yace "kada ka biye mata, akwai hanya mai sauƙi wacce zamu iya wajan ganin tayi mana mubaya'a" Mabus yace "barta, bana son ta raina min addini na, da kuma ƙarfin mulkin da Zahel take dashi na san me zanyi akai" Ruwa aka bawa Sara, mutunan wajan duk suka bita da kallo,ta shiga yin alwala a nutse, tana juya fararan yatsunta masu kyau da tsari, bayan ta kammala alwalar ne ta buƙaci abu mai kyau da kuma tsafta,tayi nesa da wajan Dodo, tasa kanta Gabas, tun a kabbarar farko sukaji wajan yana girgiza, da sauri Mabus ya nufi wajan abin bauta kabas ya shiga yi masa kirari...Sara addu'a take a sujjada for the first time hawaye masu zafi suka shiga fita daga cikin idanunta, zafin da Zuciyarta yake ya ɓaci, tana ganin duk abinda ya samesu mahaifinsu shine sanadi, tashin hankalin ta bai shige tunanin inda Sairah take ba, addu'a ta dingayi a hankali taji Zuciyarta na sanyi... Yayinda Mabus ma yake neman tsari daga sharrin mugwaye gefe guda kuma yana neman yardar Kabas wajan sahalewa masa kwanciya da Sara a matsayin sarauniyar Zahel. Gimbiya Noro ce zaune tana kallon Sairah wacce take shan ruwa da saurin ta kamar bata taɓa ganin ruwa ba, Sairah na gama shan ruwan ta sauke ajjiyar zuciya, kafin a hankali tace "where are you Twin, Ubangiji ka bayyana min ita, Allah ka kareta ka duba halin rashin lafiyar da take ciki" Gimbiya Noro tace "me kike cewa?" Gently Sairah ta girgiza kai tace "Cewa nayi zanyi Sallah" a ɗan tsorace Gimbiya Noro ta juya sai kuma ta saki ajjiyar zuciya ganin babu kowa a ɗakin kafin tace "mene sallah? Ohh wannan dunguran?" Kai kawai Sairah ta ɗaga alamar "eh" Gimbiya Noro ta miƙe tace "biyoni" Tashi Sairah tayi tabi bayan gimbiya Noro, tafiya sukai mai nisa, har suka kawo wani sashe da babu wanda yake shigarsa, kallon Sairah tayi tace "kiyi a nan, amma duk sanda wani ya ganki babu ruwa na"  Sairah ta jinjina kai tace "Thank you Maahh..." Gimbiya Noro na kallon Sairah tayi sallah, bayan ta gama suka fita zuwa sashen gimbiya Noro, ɗawisu ta saka aka dafawa Sairah ba tare da Mabus ya sani ba, sosai kowa Sairah taci domin yunwa take ji kamar ta mutu haka ta keji, a nan bacci ya ɗauke Sairah ita kuma gimbiya Noro ta fita zuwa wajan Mabus. Mabus bayan ya kammala abinda yake ya dubi Sara yace "akwai sharaɗi idan har wani ya kasa cetonki to Tabbas zaki zama matata ko baki so.."  Sara nada yaƙini addu'ar ta ba zata tashi a banza ba, hakan yasa ta ɗaga kai alamar ta amince, Murmushi kawai Mabus yay kafin yace "a kira min dakaro domin ƙarawa masarautar Zahel tsaro" yana faɗin hakan yaja hannun Sara zuwa inda yake ajjiye ta wajan da yafi ko wanne tsaro a cikin Masarautar... Da yamma Mabus ya kalli boka yace "Ina son a hargitsa min ƙwakwalar yarinyar, dukkan abinda nace tayi babu musu, koma a tilasta ta yiwa addinin mu biyayya" Boka yace "hakan nasu ayi tun farko, ashe tunaninka yafi nawa" Mabus yace "na barta ne, sbd bana son ta fahimci zan mata wani abu" Boka yace "Na fahimta, ita da sallah yanzu har abada, amma dole sai mun rabata da dukkan wani musulmi da zai shiga rayuwarta" Mabus yace "Kana tunanin wani zai iya shigowa masarautar Zahel ne? Balle har ya haɗu da Ita? Ya ruguza min tsarin da na shirya" Boka yace "Uhm, babu kam domin duk Musulmin daya shigo Zahel to ya shigo abakin ransa" daga nan ya tashi ya fita, shi kuma Mabus ya fara cin naman Aladen da aka dafa masa, bayan ya gama ya miƙe tsaye ya nufi sashen gimbiya Noro time ɗin tana zaune ita da Sairah har lokacin babu wanda yay magana, sai kafeta da ido kawai Gimbiya Noro tayi, motsin shigowar Mabus taji cikin sauri ta kama hannun Sairah zuwa cikin wani daƙi, sakata ciki tayi ta kulle, fuskarta ɗauke da Murmushi tace "Abin bauta kabas ya taimake ka, an shigo lafiya" kallon ta kawai yay dai kuma yace "Akwai wani aiki dana shirya, gidan wani attajiri kece zaki aiwatar, akwai taron bokaye da Za'ai a wannan satin domin neman Masarautar Zahel kariya" kai ta jinjina tace "Abin bauta kabas ya bada Sa'a" hannu ya miƙa ya jawota suka faɗa gado... Washegari da safe Sara na zaune ta haɗe kai da gwiwa, yunwa ta keji tube tazo masarautar babu abinda take iya ci, face ruwan da take samu tasha, ta rame sosai time to time kuna gabanta na faɗuwa, ji tayi kanta ya sara da ƙarfi, da sauri ta dafe kan nata, ta shiga motsa bakinta da niyyar kiran sunan Allah, amma abin ya gagara jikinta sai rawa yake idanunta na zubar da hawaye, da wani irin ƙarfi ta ƙanƙame jikinta tare da faɗin "Abin bauta kabas ka taimake ni..... Jirgin su Abeed ne ya sauka a airport, wata haɗaɗɗiyar mota ce tazo ɗaukan su, wacce akaiwa tambari da Masarautar Bilhira, suna gidan baya driver na jansu, a haka suka isa cikin Masarautar Bilhira, idanun Abeed a lumshe yake, wlh dauriya kawai yake amma kamar ana jan gangar jikinsa zuwa garin Zahel haka ya keji. Ga wani matsanancin ciwo da ƙirjinsa yake masa, jijiyar kansa ta fito tayi raɗa raɗa, saboda masifar da kansa yake, driver nayin parking Zain ya juya ganin yadda Abeed ke sauke numfashi yace "What's wrong?" Girgiza kai kawai Abeed yay tare da buɗe murfin motar kusa dashi ya fita, shima Zain ya fita driver kuma ya shiga da kayansu, kamar mai counting steps ɗinsa haka Abeed ke tafiya, domin duk tafiyarsa guda ɗaya ji yake kamar kansa zai cire, ganin Abeed ya ɗauki hanyar sashen Naila yasa Zain yace "why not AMMA?" Abeed yace "i wanted to see Naila frist?" Zain yace "Ok then.." ya juya ya nufi part ɗin Amma domin ya tabbatar yanzu suna tare da Abba, Walking slowly Abeed ke tafiya, zuwa sashen Naila yana tafe jiri na neman ɗaukan sa, a bakin ƙofa ya tsaya, idanunsa ƙuri akan Naila dake zaune tana azkar, a jikinta taji ana kallon ta, ɗago idanunta tayi tare kallon Abeed, cikin sauri tace "Muhammadur Rasulullah s.a.w saukar yaushe ɗan nan kamar wani mikiya, shigowa Abeed yay ba tare da yay mgn ba, hakan yasa Naila cewa "Shalele ne ko kuma wancan maƙaryacin lauyan?" Abeed yana zama kan kujera tare da lumshe idanunsa yace "Laywers na wajan Amma" Naila ta washe baki tace "To wa nake dashi a duniyar nan ai sai kai ɗin, wallahi babu mai iya raba wannan Soyayyar tamu, sai munafiki shima Allah ya tsine" ta ƙare tana zama kusa Abeed, hucin zazzaɓi taji a jikinsa tace "Kai kuma lafiya, kake numfashi kamar wani zaki ɗan shekara sittin?" Murya a maƙale yace "Fever and headache Naila" Naila tace "Wani abu ne haka kuma?" Shiru yay mata yana ɗura kansa a cinyarta tare da lumshe idanunsa, try to force his self to sleep. Zain ya ƙarasa sashen Amma kamar yadda yay tunani suna tare da Abba, da murmushi Amma tace "wlcm back twins" Zain yay Murmushi yana zama ƙasan carpet yace "Abba, Amma good evening" Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas dake zaune yana shan dakakkiyar fura wacce tasha cikwi yace "Evening how are you?" Zain yace "Allahamdulillah" Amma tace "and where is your brother?" Kafin yay magana Abba yace "Yana wajan Naila" dry Zain yay yace "Ya akai ka sani Abba?" Abba yace "Abinda tun yana ƙarami,ya fifita Granny akan parents" Amma tace "Ai ya lalace, yanzu da zaka je yana kan cinyarta a kwance, tayaya zai saki jiki ya nemo matar aure tana sangarta shi, kayi magana kuma wlh kaji abinda yafi ƙarfinka" Abba yana shan furarsa yace "Soon zai aure, ai tace dole ayi aurensa da Riya" da mmki Zain yace "Abba Abeed doesn't like Riya, ko forcing nasa za'ai?" Abba yace "ni ɗan kallo ne, ɗaurin aure ne nawa, haka Naila tace" shiru kawai Zain yay sam baiji daɗi ba, baya son abinda zai ɓata ran Abeed musamman da yanzu yake fama da ciwo, miƙewa yay Amma tace "where are you trying to go...?" Yace "i wanted freshen up" tace "ok, let me get you something to eat..kafin wankan" fita yay zuwa haɗaɗɗan sashen su, yana zuwa ya faɗa toilet, yay wanka tare da gabatar da Zhur prayer, wasu ƙanan kaya ne a jikinsa farare, a hankali yake tafiya, har ya fito main Parlo, Amma ce ka ɗai zaune, domin idan tana nan kuyanginta baza shigowa, Kallonsa tayi tace "Lunch ɗin" yace "Bari naga Abeed" tace "ok a gaida Naila" fita yay zuwa sashen Naila, lokacin daya isa yaga Naila zaune ta zabga tagumi, ga kuma family doctor nasu, sai Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas, da mmaki yace "hey, what's going on here?" Abba yace "Yanzu Naila ta kirani tana, kuka wai zazzaɓi yake hadda aman jini" gaban Zain ya faɗi, da sauri ya zauna kusa da Abeed dake bacci, ya ɗura kansa akan cinyarsa yace "We need to go to the hospital" Dr yace "No need, he will soon recovering" Mai martaba dai shiru yay, yana amincewa da auran da Naila za taiwa Abeed ƙilan hakan zai sanya ya samu lafiya. Can yamma Abeed ya farka time ɗin Zain ya fita zuwa Court, ganin babu Naila yasa a hankali ya nufi part ɗin su, wanka yay yazo saka kaya ya rasa, wanne zai saka number Amma ya kira bayan ta ɗaga yace "Wanne kaya Zain ya saka" dry tayi tace "Suit nevy blue." Kashe wayar ya yi, ya ɗauki irin kayan Zain ya saka yana wani irin ƙamshi, ya fito sashen iyayen nasa, Zaune ya samu Amma da Abba, gaishe su yay, daga nan bai sake magana ba, ganin yadda ya rufe idanunsa sosai yasa Amma faɗin "kana stressed kanka da yawa wlh,U look stressed out."  Abeed ya girgiza kai can yace "Abba zan fita" Abba yace "where" Abeed yace "Waje zani" Abba yace "take care" yana fita waje wajan compound Riya na zuwa, cikin sauri tai hugging nasa ta baya tace "wlcm back my singer" hannu yasa ya ture ta, murya can ƙasa yace "Middle class..."  Yau Monday kwannasu biyu da dawowa 9ja, Zain ne ya dawo gida da ciwon kai, saboda wata Shari'a daya gabatar kuma gobe yake son tafiya Zahel, Abeed da kansa ya kira Dr yaywa Zain injection, lokacin da akai masa allurar Abeed ya sauke wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, nan take kuma bacci ya ɗauke Zain, wayar Zain ya ɗauka, da komai nasa, kana ya saka key ya rufe sashen baki ɗaya, cikin sauri yake tafiya waya maƙale a kunansa yana faɗin "Abba, zamu somewhere, Kada abar kowa ya shiga shashen mu, akwai kaya masu muhimmanci, nan da 3 to 4days zamu dawo" Abba yace "Allah ya kiyaye" yana faɗin hakan ya shiga mota tare dayi mata key, gudu kawai yake yana duba map yana nuna masa direction ɗin da zai bi, cikin ikon Allah misalin 10 na dare ya shigo Garin Zahel....

_Wannan labarin, ban fara ba sai dana tabbatar da ingancin cinsa, da kuma lesson ɗin da Za'ai leaning a ciki, ba zan ɓoye ba akwai Romance a labari, domin haka na tsara,  so dan Allah Dukkan wanda ya san ba Zain Abeed zai siya ba, kada wanda yay min mgn for no reason, masu cewa a basu kyauta ko kuma saboda Allah basu da Kuɗi, kullum ina sadaƙa wlh, ga free book nan suna ta gantali a media, *Zain Abeed* na kuɗi ne, babu kuma wacce zan bawa kyauta ki biya Ni Sarauta na saki a original grp soon zanyi ending free pages.........._

*ZAIN ABEED*

BOOK 1,2,3
AMOUNT #500
6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank.... EVEDANCE 08119237616

Wanda suka biya za'a zasu a Original grp Na vip.

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

ZAIN_ABEEDWhere stories live. Discover now