ZEEYAD

89 5 0
                                    

*Z E E YA D*
'''(The Abandoned Prince)'''

                 *NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*



*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*004...*



.............Kujera aka ja masa ya zauna kafin ya shiga ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya.

Idanun sa ne suka sauƙa kan ZEEYAD da kansa ke sunkuye  take yaji ransa ya 6aci,juyar da kansa yayi tare da buɗe tray ɗin breakfast ɗin dake gaban sa tare da ɗaukar fork da wuƙar da aka ajiye dan cin abincin,kafin yayi bismillah ya fara ci.

Ganin haka ya sanƴa kowacce buɗe nata abincin ta shiga ci,sa6anin ZEEYAD da bai buɗe nasa ba kuma har yanzu bai ɗago ba.

"ZEEYAD my dear,eat your food" faɗin Sarauniya Naseeba tana kallon sa.

Kallon ta Sarauniya Hafeezah tayi ta ƙasan ido kafin kuma ta kalli ZEEYAD ɗin shima a zuciyar ta tace _"What on earth is going on between them, she seems very nice to him, koma dai menene i must find it out very very soon"_ ta ƙarashe tana kallon ZEEYAD.

Kai ya jinjina tare da ɗaga murfin da aka rufe tray ɗin dashi,ƙurawa abincin dake kan tray ɗinsa idanu yayi yana jin wani abu na taso masa daga chan ƙasan zuciya.

Slice ɗin bread ne kwaya biyu sai kuma wata fale-falen soyayyiyar kwai da bata wuce yayi mata loma ɗaya koh rabi ba, kasa ɗagowa yayi ya kalle su dan kuwa yasan kowa shi yake kallo,dukda baya cin kwai haka nan ya daure ya sanƴa hannun sa tare da ɗaukar bread guda ɗaya ya haɗa da kwai ɗin tare da yin basmala ya kai bakin sa.

Kallon sa kawai Sarauniya Hafeezah keyi dan ganin reaction ɗinsa,dan kuwa itace wacce tasa akayi masa serving ɗin wulaƙancin nan.

Idanun mai Martaba ne ya faɗa kan tray ɗinsa,magana zaiyi sai dai yaji bakin sa tayi nauyi ya kasa buɗe ta,hakan ya sanƴa sa maida hankalin sa kan abincin da yake ci.

_"Mai kuma wannan yaron ke son nunawa,kamata yayi ya tada husuma anan wurin ta yadda zai fusata mai Martaba a yi masa hukunci mai tsanani,sai dai ya fuske yana cin abincin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata damuwa ba,what is he actually up to?"_  cewar Sarauniya Hafeezah tana kallon sa har yanzun.

Bai iya cinƴe koh rabin wanda ya ɗauka ɗin ba sakamakon kwai ɗin da ya haɗa ta da ita yaji zuciyar sa na tashi,ga kuma jiri da ya fara ji duka a lokaci ɗaya.

Murmushi Sarauniya Hafeezah ta saki a cikin zuciyar ta tace _"Wow"_

Tashi yayi tsaye da kyar sakamakon kansa da yakejin tana juya masa,runtse idanun sa yayi yana sake ware ta tare da jijjiga kansa koh zai dawo saiti.

Ya san ba zai ta6a dawowa saiti yanzun ba indai har ba wai ya samu hutu da bacci bane,komawa yayi zaune kan kujerar tare da ɗaukar fork ɗin dake kan tray ɗin abincin sa yana damƙe ta a hannun sa inda yake trying so very hard ganin ya dawo nutsuwar sa,dan kuwa har dishi-dishi yake gani.

Miƙewa mai Martaba yayi bayan ya gama cin abincin sa tare da barin dining area ɗin ya haura sama.

Tashi Sarauniya Nazeerah tayi ba tare da ta tanka ba itama ta fice zuwa part ɗinta inda ya saura Sarauniya Hafeezah da kuma Naseeba.

Murmushi Sarauniya Hafeezah tayi tare da miƙewa itama ta fice ta zuwa nata part ɗin.

Kallon sa Sarauniya Naseeba tayi kafin kuma ta hau duba arear wurin dan ganin babu hankalin wanda ke kansu, tasowa tayi ta ƙaraso wurin sa tana shirin kai hannu jikin sa ne yace "Don't you dare...don't you dare touch me" ya faɗa cikin muryar dake nuna alamun yana jin jiki.

ZEEYADWhere stories live. Discover now