Z E E Y A D

54 4 0
                                    

*Z E E Y A D*
'''[The Abandoned Prince]'''


                  *NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*



*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*



_Kada wacce tayimin Kuka a page ɗinnan😩_



*011...*



_*Banida lafiya ku sani a addu'oin ku, banyi editing ba*_


...............Da kallo suke bin juna wondering wane irin amsa yakamata su bawa Mahaifiyar tasu, Jafar ne yace "Umma ai basuda gida, shi kaɗai ne yake rayuwa."

"Um!, bangane ba, kamarya shi kaɗai yake rayuwa?."

"Umma Balarabe ne fah, ba ɗan nan ƙasar bane, kuma bashida wurin kwana da zama sai gindin ƙatuwar bishiyar dake hanƴar islamiyyar mu."

"Balarabe, then toh a'ina ya san ku har kuka zama abokai dashi?."

"Shine wanda DEENAH take kaiwa abinci kullum."

"Shine yayi wannan zanen?."

"Eh Umma kuma fah bayajin hausa ma, sai turanci kaɗai" cewar DEENAH tana kallon ta.

Tunani Ummar tasu ta shiga yi kafin ta rufe takardun tace "Ku maida cikin jakan ku, bari na dubo mana girkin" ta faɗa tana tashi ta fice zuwa waje.

Da kallo suka bita kafin Jafar ya kalli DEENAH yace "Ya naga fuskar Umma ya canza?."

"Koh ka sani zata ce kada mu sake kula shi tunda bamu sanshi ba" ta faɗa kamar zatayi kuka.

"Umma tana da kirki ba zata raba mu dashi ba."

Takardar ta sake ɗauka tana sake kallon hoton dake jiki fuskar ta na fitar da murmushi...........

******************

...........Washe gari bayan gari yayi haske tuni sunyi shirin makarantar su kowa ya sanƴa uniform ɗinsa inda Ummar su ma tayi shirin fita aiki.

Kallon Umma dake ta sauri tayi tace "Umma baki fah zuba min abincin ba."

"Wane abinci kuma DEENAH?" ta faɗa tana kallon ta.

"Abincin da zan kaiwa abokin Yaya."

"Ina shi yayan naki?."

"Yana waje."

"Kira shi yazo ya kai masa dawuri, kinga dai zanyi latti koh?."

Da sauri ta fice taje ta kira Jafar da har ya fice waje ta dawo.

Abincin Umma ta miƙa masa tace ya kaiwa abokin sa ya dawo da wuri su wuce.

Amsa yayi cike da farin ciki yace "DEENAH zo muje."

"A'a ba zata ba, kai kaje" cewar Ummar tasu hakan yasa farin cikin dake ɗauke kan fuskar DEENAH gushewa.

Ficewa yayi nan Ummar tasu ta kalli DEENAH da kanta ke ƙasa alamun tayi fushi kafin kuma tace "Kinason ganin sa kullum?."

Da sauri ta ɗago tana kallon Mahaifiyar tata jin abinda ta faɗa.

"Kinason ganin sa kullum?" ta sake tambayar ta.

Da sauri ta jinjina mata kai alamun eh, nan ta sake cewa "Daɗi kikeji a ranki idan kin ganshi?."

Shiru tayi tana kallon fuskar mahaifiyar tata kafin kuma tace "Umma idan yaƙi cin abincin da na kai masa ne nakejin babu daɗi."

"Maiyasa baya cin abincin da kike kai masa?."

"Nima ban sani ba, amma idan naje har korata yakeyi yace na daina zuwa kusada shi, kullum baya cin abincin da nake kai masa sai dai na baiwa almajirai a hanƴa."

ZEEYADWhere stories live. Discover now