Jihar Adamawa (Fula: Leydi Adamaawa) jiha ce dake a shiyyar arewa maso gabas na siyasar Najeriya, Gombe (jiha) da Borno daga arewa maso yamma, Gombe zuwa yamma. a yayin da ta hada iyaka da kasar Kamaru daga gabas. Jihar ta samo asalin sunanta ne daga tarihinta na Masarautar Adamawa, tare da tsohuwar babban birnin masarautar watau Yola wanda take matsayin babban birnin Jihar Adamawa a yau. Jihar ta kasance daga cikin mafi rabe-rabe tare da harsuna na asalin garin daban daban fiye da guda 100 - an kafa Jihar a 1991 a sa'annin da aka raba tsohuwar Jihar Gongola don samar da Jihar Adamawa da Taraba.
Labarin *IDAN BA KE* labari ne da ya faru a zahiri bawai ƙirƙira ba, ina nufin ba (fiction story) ba ne. Jaruman Littafin mu guda uku ne, *HALISA* *ZARAH* da kuma *CAPTAIN ALIYU HAIDAR* wanda ya fito da ga cikin ƙabilar *Kanuri* yayinda Halisa y fito da ga cikin ƙabilar Fulani. Sai dai rashin sanin kalar zanan ƙaddarar da ya haɗata da Captain Aliyu Haydar shi ne babban abin duba a wannan labarin.
Kafin shiga asalin labarin, bari muji su waye Fulani da kuma kalar rayuwar da suke fuskanta, wanda zai taimaka wajan fahimtar labarin kai tsaye da zarar an fara.
Fulani dai ƙabila ce da tarihi ke turke Asalinta tun ƙarni na 15 da ga wasu manyan yankuna biyu da ke ƙasashen Senegal da kuma Guinea Conakry, wato Futa Toro da kuma Futa Jolloh.Daga nan ne suka ci-gaba da ba zuwa cikin ƙasashen duniya musamman yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka domin nema wa dabbobinsu abinci da kuma ingantacciyar rayuwa. Fulani sunfi yawa a Nijeriya sannan suna da yawa a kasashen: Guinea Conakry, Guinea Bissau, Mali, Senegal, Gambia, Mauritania, Kamaru, Niger, Sudan, Saliyo, Burkina faso da kuma Chadi. Fulani nada manyan masarautu a Nijeriya sun haɗa da: Masarautar Fombinah ta Modibbo Adama, Masarautar Sokoto, Masarautar Kano, Masarautar Zazzau, Gwandu, Katsina, Gombe da sarauransu.
Fulani suna da rabe-rabe, kamar ma zauna gari, Makiyaya wanda akewa laƙabi da Bororo, sai mazauna ƙauye. Kai tsaye bari mu leƙa RUGAR ROME. Da ke yankin Yola domin a nan ne labarinmu zai fara....
Halisa Dajeno
Aliyu Haydar
(Yaa Sheikh)A watar fuskar kuma Yaa Lee
YOU ARE READING
IDAN BA KE
Non-FictionTrue life story. labarin zanan ƙaddara wanda babu wanda ya isa ya hana shi faruwa sai Ubangiji al'arshi. soyayya mai cike da tausayawa wacce ƙaddara ta haɗa a lokacin da ba'ai zato ba.