_*Zaku samu cikakken labarin a Arewabooks, kuyi searching sunan littafin ko username Arewabooks@Nimcyluv*_
8....
Ihu da kururuwa Prince ya din ga yi, sbd tsananin azabar da Abba ya ganawa masa. Cikin wata kakkausar murya wacce take nuna cewa ko a cikin Aljanu shi ɗin nada banne, kuma taƙadiri ne. "Akan aurena dake kan Halisa banƙi na kashe kowa na illata shi ba, daga ci hadda kai Abba, ba ruwana da kasancewar ka mahaifina, kada ka rabani da Danejona zakai babban kuskure zanyi ɓarna a duniya" Bakin Abba na fitar da hayaƙi kamar zai kunna wuta a ciki ya ɗaga hannunsa sama gaba ɗaya ya naɗe Prince cikin wata sarƙa da yana bakinsa ɗauke da addu'ar neman samun nasara akan Prince ɗin.
Duk ihun da yake bai hana Abba ya sarƙafesa cikin yanar ba idanunshi ya yi wata kala. Cikin ɗaga murya mai amo! Ya ce "Na raba aurenka da Halisa, babu kai ba ita, kuma a yanzu zan cire cikin dake jikinta mara imani mai muguwar zuciya" yana faɗin haka ya yi girgiza tare da ɓatar da Prince ɗin baki ɗaya daga wajan. A hankali Abba wanda Asalin sunansa ya kasance MURWAS ya sauke numfashi, tare da juyawa ya kalli Halisa dake kwance a ƙasa tana barci, juyawa ya sakeyi ya kalli Safwan dake kwance shi ma. Cikin nutsuwa wacce ba zata addabi dabbobin dajin ba ya yi Girgiza tare da rikiɗewa ya koma suffar mutane sak. Hannuna ya ya ɗauki Halisa Dajeno Rome da sauri ya nufi cikin Rugar Rome zuciyarsa fal farin ciki ganin yau ya raba ɗansa Bilal da Bil-adam.
Babu kowa cikin rugar kamar an share hakan yasa ya fara bin bukkokin Rugar da kallo kamar daga sama Hamma Yabi ya fito daga cikin ruga zufa na yanko masa hannunsa riƙe da ƙwarya maganin gaba ɗaya tunaninsa ya yafi wani wajan bai lura da mutumin dake tsaye yana binsa da kallo ba. "Jamɓanduna" Abba ya faɗa yana kallon Hamma Yabi dake ƙoƙarin yin gaba, tsayawa ya yi yana duba mutumin da ya ce masa Ina kwana, cike da mamaki ya ce "Jamni tawon" ma'ana lafiya. Abba ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba, jikin Hamma Yabi na rawa ya amshi Danejo daga hannun Abba kafin ya ce "Ikon Allah, ina kasa meta? Tsayin mako guda ta ɓace mana ba ita ba labarinta, shai Allahamdulillah" Murmushi mai sanyi Abba ya yi cikin nutsuwa ya ce "Ayyah ni ma yanzu ina iyu a cikin ruwan na ganta kwance gefen ruwan" cikin nuna jin daɗi da manta halin da Dada ke ciki wanda duk rashin Danejo ya haifar da haka ya ce "Shannu, wallahi shannunka kaji" kai kawai Abba ya ɗaga yana ƙarewa yanayin rugar kallo kafin ya juya bayan sun yi Sallama da Hamma Yabi yabar wajan. Yana fita ya ɓace a wajan baki ɗaya.Dada na kwance bakinta na fitar da wani ruwa kamar dafara Shatu na gefe tana kuka tamkar ranta zai fita. A cikin wannan halin Hamma Yabi ya shigo cikin bukkar hannunsa ɗauke da Danejo wacce har yanzu take bacci. Jikin Shatu na rawa ta miƙe fuskarta cike da hawayen halin da mahaifiyarsu ke ciki, amma hakan bai hana Fuskarta baiyyanar da farin cikin da zuciyarta ke ciki ba na ganin Yayarta Danejo. Bakinta na rawa ta ce "Hamma ina ka samu Danejo, da gaske ita ce yanzu Dada zata tashi naji daɗi sosai" bai ce komai ba ya kwantar da Danejo gefen Dada idanunsa akanta ya ce "Maza kawo mini ruwa" Shatu ta miƙe da sauri tare da nufar tulo ta tsiyayi ruwan mai ɗan sanyi, tana bashi ya shiga shafawa Danejo yana kiran sunanta. A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana buɗe ido a nutse. "Danejo"... "Halisa" Shatu da Hamma suka kira sunanta lokaci guda,a sanyaye cikin sanyin jikinta kamar kullum ta shiga binsu da idanu. "Kin farka?" Kalmar Hamma ta sanya ta lumshe idanunta kana ta buɗe a hankali tana sake binsa da kallo kafin ta yunƙura zuwa zaune "Naga kuna ta kallona kamar za a cini ɗaya?" Murmushi Hamma ya yi ya ce "Munji daɗin ganinki Danejo, mako guda kenan mun rasaki kin ɓace daga idanunmu" da Mmki take kallonsa ɓata? Mako guda? Taje ina? Ita gani tayi kamar barci take mai ɗauke da mafarkai kala-kala. Shiru tayi tana ƙara sauke numfashi tare da fara tunanin maganar Hamma Yabi. "Hankalinmu ya tashi, Kullum Dada cikin kiran sunanki take, gashi yanzu ko buɗe ido ba tayi jikinta ya tashi ina tsoro kada mu rasa Dada kamar yadda muka rasa Baffa" ambaton sunan Dada ya saka Danejo saurin juyawa zuwa gefenta manyan idanunta ta buɗe "Dadata" ta furta a ruɗe ganin yadda Dada ta ƙanƙame jiki, idanunta na kafewa kamar mai shirin mutuwa cikin muryar kuka ta ce "Na lalashe ni Danejo Dadata kada ki barni kada ki mutu do Allah,Kada kibi Baffana" sai girgizata take amma ina Dada ko motsi ba tayi.
Da sauri Hamma ya fita zuwa bakin hanya tare da samu abin hawa yana zuwa suka ɗauki Dada a mota zuwa asibiti, asibitin babu jama'a sosai. Dr Hamza na zaune a Office gabansa cike da kuɗi ya kalli Dr Iliya ya ce "Kawo maganin nan ya yi mana rawa sosai, na ƙara tura saƙo zuwa ɓangaren lafiya akan magungunan da suka bayar ya ƙare, sbd cututtukan da suke damun jama'ar rugar, ina saka ran cikin satin nan za a kawo maganin" Dr Iliya ya numfasa yana jinjina kai kafin ya ce "That's good. Amma da gaske maganin ya ƙare ne?".. "No ba wani ƙare wa da ya yi, har yanzu ban bawa ko mutum ɗaya ba" cikin fahimta Dr Iliya ya kalli Dr Hamza yana faɗin "huh! za a kawo maganin sauro kyauta ma a raba, sbd yawaitar Maleriya"
YOU ARE READING
IDAN BA KE
Non-FictionTrue life story. labarin zanan ƙaddara wanda babu wanda ya isa ya hana shi faruwa sai Ubangiji al'arshi. soyayya mai cike da tausayawa wacce ƙaddara ta haɗa a lokacin da ba'ai zato ba.