A zabure ta miƙe tsaye tana ƙarewa cikin dokar dajin kallo, babu abin da ya bata mamaki irin yadda taga an sauya mata kayan jikinta, daga na Fulani zuwa na wasu saƙi farare masu kyan gaske. Jikinta na rawa sbd tsoro da tarin fargabar dake ratsa dukkan wasu lunguna na ƙofofin zuciyarta ta shiga ƙarewa jikinta kallo. Idan hankalinta yai dubu to ya tashi ta ƙara razana da halin da take ciki a yanzu, domin ba iya kayan jikinta da aka sauya mata ne kaɗai ya bata mamaki ba, zanan jan lallen data gani kwance a hannunta shi ne ya ƙara ta hanyar mata da hankali, ga sumar kanta da akai mata wasu irin kalba manyan gwanin sha'awa ita bata taɓa ganin kanta yai irin wannan kyan ba sai yau. Waye ya kawota nan Meke shirin faruwa da rayuwarta ne, ina Dadarta?.
Ƙare wa cikin dajin tai babu ko hanyar da zata bi ta nufi Rugarsu, daɗin daɗawa ita kanta bata san a inda take ba, wacce kalar rayuwa ce haka? Daga yin barci kuma sai mutum ya farka ya gansa a tsakiyar daji? Bayan tasan a bukkar Dada tai barci. Tafiya ta shagayi idan ta kalli gabas da Arewa, guda da yamma sai ta saki kuka tare da faɗin "Na lalashe jama'a ina nake ina rugar rume tayi, ina Dadata, ina Shatu, ina Hamma Yabi duk kuna ina wayyooo Hande en boni, Yettore jaumirawo" ta faɗa ɗora hannunta aka tare da sakin kuka, ta fiya kawai cikin dokar dajin tun tana kuka har tai shiru sai idanunta da take rarraba wa a ciki dajin.
Kukan da tayi da kuma gudun data jima tana yi sune suka taru suka haifar mata da wata gajiya wacce ta sanya ko idanunta bata iya buɗewa sosai sbd yadda kanta ke juyawa da kuma yunwar data keji, lokaci zuwa lokaci tana buɗe idanunta tare da zubawa zanan lallen hannunta idanu, tana cikin wannan hali ta ƙaraso wani waje wanda yake da rana sosai hakan yasa Danejo ta wahala fiye da zaton mutum, ga ƙishin da take ji. Daurewa tai taci gaba da tafiya sai dai duk yadda takai da daurewa ta kasa bata san lokacin da jiri ya kwashe ta ba, tai baya luuu zata kifa da sauri aka tareta ana faɗin "Subuhanallahi" mutumin ya faɗa a taushashe yana mai riƙe Danejo wacce ta faɗo jikinsa babu numfashi alamar ta soma kenan.Kyakkyawan idanunta mai ɗauke da kuriyar ƙwayar ido su ya ware akan Danejo yana mai ƙara jin nutsuwa na saukar masa a jikinsa, a hankali a kuma dukkan wata ƙaunarta ta shiga nunkuwa a zuciyar Prince Bilal. Yanzu ne zai samu cikakken lokacin kasancewa da ita, irin kasancewar nan ta har abada domin baya jin akwai mutumin daya isa ya raba shi da Matar Danejo a cikin wannan Dajin, zai zauna da ita zai rayuwa da ita, tai ta haifa masa yara, ya kuma yi alƙawarin ba zata taɓa sanin shi aljani bane, zaici gaba da zuwar mata a suffar Balarabe kamar dai suffar wani Sheikh ɗin Malami. Ɗaukarta ya yi a hannunsa zuwa gaɓar wani ruwa, jallabiyar jikinsa ta sauka har ƙasa tare da rufe masa ƙofatonsa, a haka ya Ƙarasa tare da kwantar da ita a gefen ruwan wajan da yake da ɗan danshi danshi musamman daya lura da jigatar da tai duk da cewa duk wani abu da take akan idanunsa ne. Yana kwantar da ita ya zauna gefenta idanunsa na juyawa tare da sauya launi zuwa wata kalar, hankalinsa ya karkata gaba ɗaya zuwa cikinta idan yake hango ɗansa dake maƙale a mararta hakan sai cike da farin ciki Prince ya saki Murmushi bakin na rawa ya ce. "Ubangiji ya saka mini sonkiwa zuciyata, tun kina cikin mahaifiyarki, zanci gaba da sonki ba zanyi saken da za a rabani dake ba, kamar yadda aka rabani da mahaifiyarki tun tana asalin inda take rayuwa" shafa cikin nata yai idanunsa na tsiyyayar da wani ruwa ya ce "Babu alaƙa tsakanin mutane da Aljanu, amma naji a wannan karan dama Ubangiji a suffar mutane ya halittoni, mene yasa bakwa iya ganinmu a suffarmu ta zahiri sai dai mu muganku? Ina son ki matata Danejo,ina gab da ɗaukeki zuwa duniyarmu" dariya ya saka gaba ɗaya wajan ya ɗauki rawa da Girgiza can kuma ya ɓace da wajan.
Acan Rugar Rome kowa gari na wayewa suka saba Danejo na tashi zuwa garken Nagge ƙara tatsar nono, hakan yasa Dada bata damu ba sbd ganin Danejon bata cikin bukkar sai Shatu dake kwance a gefe tana barci, Hamma Yabi ya fita tun sassafe zuwa asibitin dake gefen Rugar Rome domin samawa Dada layi. Yana tsaye a a ɗan wajan da mutane suke tsayawa gaba ɗaya mutanan ba sufi mutum goma ba, suna zuwa kamar mutum biyar zai koma ya ɗakko Dada. Wani Likita ne hannunsu riƙe da waya yana dubawa ya raɓa ta gefen Hamma Yabi ya shiga office, Fuskarsa ɗauke da fara'a ya kalli mutumin dake cikin office ɗin ya ce "Dr Hamza na ganka a zaune ina patients ɗin?" Dr Hamza ya dubi Dr Iliya yana ƙara ware idanunsa ya ce "Patients suna can waje, bani da time na duba su serious,idan zaka shekara kana duban jama'ar Rugar nan ba zaka taɓa samunsu da cikakkiyar lafiya ba, ƙazanta ita take ƙara lalata musu lafiyar jikinsu na gaji wallahi, sai Shegen son shanunsu amma basu san yadda zasu kula da lafiyar jikinsu ba" Dr Iliya yaja kujera tare da zama sosai yana faɗin "Ai Dr Hamza sai haƙuri, kasan cikin karkara musamman ruga haka ba komai suka sani ba, kai dai barsu da arziƙinsu wato Nagge su kawai suka sani" Dr Hamza ya ce "Let's leave this matter, it is not in front of me" ya faɗa yana duba wani file, "I got the message you want to see me up, lafiya dai kake mini kiran gaggawa haka?" Dr Iliya ya tambayi Dr Hamza cike da jin don abin dake faruwa. Gyara zama Dr Hamza ya yi kafin ya ce "The government has given free medicine to the people of Ruga, maganin da gwamnati ta bayar suna da yawa, akwai maganin Suger, Hawan jini, Maleriya, da sauran maganin cuccutikan, yawwa sai maganin sikila irin folic acid, Paludrine, Peniciillin V,Hydroxyurea. Anfi kawo maganin Sickler sbd yawaitar samunta da ake cikin karkara, shiyasa nace a kiraka" cikin jin Daɗi Dr Iliya ya ce "Masha Allah yanzu yaya za'ai kenan?" Wani kallo Dr ya Hamza yaiwa Dr Iliya kafin ya ce "Ya kowa za'ai? Kasan Rugar nan ko an basu magani a banza, basu san important ɗinsa ba, so that zamu kwashi 88% a cikin 100 mu siyar mu raba kuɗin, kai ba kana da chamist ba? Sai ka zuba kawai acikin chamist ɗin naka" cike da gamsuwa Dr Iliya ya ce "that's good, amma gwamnati ƙoƙari sosai fa, banda haka wannan maganin sunfi ƙarfin miliyan 3 da wani abu fa,ana kula yanzu da ɓangaren lafiya sosai da masu juna biyu, anywhere zuwa dare zan zo da mota na ɗauki rabona" Sallama sukai tare da fitowa a tare ganin hakan yasa Hamma Yabi saurin kallon Dr Hamza ya ce "Aradun Allah na shafe awanni a nan gashi muna ta jira" a faɗace Dr Hamza ya ce "Wai kai fillon nan wani irin banza ne bagidaje ne kai? You doesn't know anything akan asibiti ka addabi mutane da wautarku ta Fulani, mu bamu da wasu kayan aiki cikin Asibitin nan kana kallo da idanunka ai, dan haka kada ka sake zuwa idan an kawo kayan aiki zamu sanar get out" jiki babu ƙwari Hamma Yabi ya koma cikin Rugar Rome, yana zuwa ya sake tarar da wani tashin hankalin babu Danejo gaba ɗaya acikin Rugar, sanadin hakan yasa jikin Dada ƙara rikicewa abu kamar wasa duk inda suke tunanin ganin Danejo babu ita sam har kusan kwana biyu.
Tunda ya kwantar da ita a gaɓar ruwan har gari ya waye ta kwana a wajan, wani daren ya yi ta sake kwana, kwana biyu kenan amma bata motsa ba. Bata kuma da ranar tashi sai lokacin da Ubangiji ya nufa ko kuma ya tsara. A can cikin barci ta fara mafarki gata da namiji suna kasancewa waje guda, wani abu mai kama dana auratayya na gilmawa a tsakaninsu. Numfashi ta sauke tana motsa ƙafafuwanta zuwa cinyoyinta da suke mata zafi, tana jin kamar an daddaneta a firgice ta farka tana kurma ihu tare da kiran sunan Dada, ba addu'a babu komai. Cikin tsoro ta fara bin jikinta da kallo babu komai lafiyarta ƙalau domin ba wani sauyi da taji. Ajjiyar zuciya ta sauke a bayyane tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka, kenan haka rayuwarta zata ƙare cikin dokar dajin ko yaya ne? ya akai ta tsinci kanta a dajin gaba ɗaya ta rasa amsar tambayoyin zuciyarta. A hankali ta fara jin dariya na karaɗe wajan, tare da surutu ƙasa ƙasa. Miƙewa ta yi da sauri ta shiga duba inda take jiyo sautin dryar a haka ta ƙaraso jikin wata ƙatuwar bishiya, cike da tsoro da kuma tarin zullumi ta ɗaga kansa zuwa saman bishiyar idanunta ya sauka akan wani ganyen bishiya dake lilo shi ɗaya, sai ka ɗauka iska ke kaɗa shi amma abin mamaki shi kaɗai ne yake lilo daga cikin sauran ganyen bishiyar. Prince Bill wanda a yanzu ya rikiɗe zuwa suffarsa ta asalin aljani yana kwance saman ganyen yana karkaɗa ƙafarsa wacce ita ce take sanya ganyen bishiyar motsawa, Danejo dai kallon ganyen take cike da mamaki tana tsaye taci mangoro ya faɗo kanta abinka da mai jin yunwa da sauri ta ɗauki mangoron babu Bisimillah ta shiga sha idanunta na lumshewa sbd daɗi. Daga bayanta taci ance. "Kisha a hankali da wasu da yawa idan kina buƙata" juyawa tai da sauri baki buɗe take kallon mai maganar, iya tsoro da razani ta shiga domin bata taɓa ganin halitta irin wannan ba, mangoron ta saka tare fasa wani Ihu ta ɗaga ƙafa zata gudu yai saurin riƙe hannunta.
Share🥰🥰🥰
YOU ARE READING
IDAN BA KE
NonfiksiTrue life story. labarin zanan ƙaddara wanda babu wanda ya isa ya hana shi faruwa sai Ubangiji al'arshi. soyayya mai cike da tausayawa wacce ƙaddara ta haɗa a lokacin da ba'ai zato ba.