Cikin ƙaramin lokaci ƴan Rugar Rome suka shiga cikin tashin hankali musamman wajan su Danejo. Ko kuka ta kasa ta kafe gawar Hamma Yabi da kallo sai Ajjiyar zuciya take, shatu na gefe ta ƙanƙame jikin Dada wacce ke sanƙame bata san meke faruwa ba sbd halin da take ciki. Bata taɓa ganin anyi kisan kai a gabanta ba, yaushe gashi an kashe mata yaya wanda ke kula dasu shi kaɗai ya rage musu. Halisa Danejo Rome ta shiga halin firgici ita kaɗai tai ta razana har lokacin idanunta bai motsa daka kan gawar Hamma Yabi ba a haka Asuba ta risketa. Sarkin ruga da Giɗaɗo ne suka shigo bukkarsu Danejo ba neman iso domin basu damu da cewa Dada matar da za a nemi aminci a wajen ta bace. "Allahu Akbar Allahu ya jiƙan Yabi shai abu bai kyau ba sam" Sarkin ruga ya girgiza kai ya ce "Allah sharki aradu harbi har biyu dole ya mutu" da sauri Danejo ta miƙe jikinta na rawa ta kama hannun Giɗaɗo ta ce "Da gaske Hamma Yabi mutuwa ya yi? Da gaske ba zan sake ganin Hamma ba?" Ta faɗa cikin rauwanin muryar kana ganinta kasan damuwa ta jima da kama zuciyarta ta samu waje ta zauna. "Ya mutu mana kamar yadda Baffanku ya mutu ba zai dawo ba" ƙurr ta kafe Giɗaɗo da idanu kafin taja numfashi mai tsayi sai kuma ta sulale a wajan ta faɗi babu numfashi.
A hankali take buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi, hannunta ta kai tare da dafa kanta wanda yake mata ciwo sbd barcin data daɗe ta nayi. "Sannu kin farka Danejo?" Shatu ta furta cikin murnar ganin Danejon na motsi bayan suman da tayi. Danejo ta juya tana kallon Shatu kafin a hankali ta buɗe baki ta ce "Ina Hamma Yabi? Ya tafi da Dada asibitin burni?" Shatu tayi saurin faɗin "Hamma Yabi ya mutu ai kuma har an rufe shi a ƙasa" zuciyar Danejo ta buga da ƙarfi tana runtse idanunta sosai tsoro da fargabar makamar rayuwarsu ta dirar mata a zuciya, yaya za tayi da Dada? Ina zata samu kuɗin asibiti ko shanu zata siyar? Mai Hamma Yabi ya yiwa wannan mutunan da shi kaɗai kawai suka kashe cikin Rugar Rome?.
Juyawa tayi ta sake kallon Dada wacce kawo yanzu ko motsi ba tayi ruwa ma idan aka bata ta gefen baki yake zubewa, hawayen da take maƙalewa suka sakko daga cikin idanunta Shatu wacce ke shirin yin kuka ta ce "Kuka ki ke Danejo? Me akai miki ba ga Dada ba muna tare da ita?" Danejo ta goge idanunta da kyau ta ce "Ba kuka nake ba, ki zauna wajan Dada bari naje wajan sarkin ruga na dawo" miƙewa tayi jikinta sanye da fararen kaya na Fulani sumar kanta ta naɗeta da wani zare mai ɗauke da kuran duwatsu masu kyau. Kanta a ƙasa take tafiya cikin sanyin jiki kamar ko yaushe a haka ta ƙarasa bukkar su Sarkin ruga ta tsaya daga waje tana neman iso. Matar Sarkin ruga ta ce "A'a Danejo ne bismillah shigo" kamar ba zata shiga ba sai kuma ta shiga ta samu Sarkin ruga zaune yana shan kindirmo a diririce ta ce. "Jamɓanduna. _Ina kwana_" Ya ce "Jamni.. _lafiya_" zata sake yi masa wata gaisuwar ya dakatar da ita da faɗin "mene ya kawo ki?" Kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta ce. "daman cewa nayi ko zaka sayi nagge guda biyar daga cikin garkenmu?" Kallon tsaf ya yi mata yana sakin murmushi kafin ya ce.
"Yabi bai faɗa miki ɗan cewa gaba ɗaya ba naggenku bane? Kiwo kawai aka baku?" Cikin rashin fahimtar maganar Sarkin ruga Danejo ta ɗaga kanta da sauri ta kalle shi tana faɗin "Dada ta sanar mini gaba ɗaya garken na Baffanmu ne, shanuwan sa ne, kuma kowa ya sani Hamma Yabi ma yasan da haka" Ya ce "E, to buɗe kunne kiji kaf cikin garken naggen nan guda biyu ne naku, sauran duk mallakina ne kuma yanzu zan ɗauka aje kasuwar burni a siyar dasu, idan kina buƙata sai a haɗa da guda biyun naku a siyar daga nan sai ku biyawa Baffan naku bashin da ake binsa ma" kasa cewa komai tayi ganin ƙarfen ƙafa da ake shirin yi musu, wanne irin son zuciya ne Wannan? A nagge sama da hamsin ace guda biyu ne nasu? Me ya sa Hamma Yabi bai taɓa cewa naggen Sarkin ruga bane? Da gaske nasa ɗin ne ko ba haka bane?. Jiki a saɓule ta dawo gida zazzaɓi na rufeta sbd fargaba. Kenan tana ji tana gani Dada zata sake mutuwa ta barsu basu da kowa a duniya?.Sheikh Aliyu haydar Aliyu na zaune yana duba yadda ginin bankunan guda biyu suka ɗauki harami cikin ƙaramin lokaci tare da kamfanin sarrafa shinkafa. A nutse cikin kulawa da haibarsa kamar kullum ya miƙawa Umar-khan Album ɗin. "Ina fatan komai ya yi yadda kake so?" Kallo ɗaya Sheikh ya yi wa Umar-khan a hankali ya juya kansa yana mai jinjina shi a nutse alamar "Ya yi" Umar-khan yai murmushi kaɗan yana jinjina halin Sheikh da yawan lokaci ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita. Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai miƙe ƙafafuwan shi saman table a hankali ya fara tunanin yadda zai gina rayuwar shi wanda zai sanya father farin ciki duk ƙoƙarin shi na gano abin da ke sanya father yaji zafin shi har haka ya rasa, da yawan lokaci abubuwan na damun shi nunawa ne kawai ba ya yi. Zuciyar shi na shiga tunani na tsayin lokaci. Miƙewa ya yi cikin kulawa ya shiga takawa a parlourn na shi, ƙarar wayar shi ta dakatar da shi daga tunanin da yake jin ringtone ɗin is different ya sanya ya fahimci mai kiran na shi. Farar Alkyabbar shi mai fidda ƙamshin Roja ya ɗauka tare da ɗorawa saman jallabiyar jikinsa banda dole ko hannun shi bai son a gani sbd tsarin halittar jikin na shi. Kansa a ƙasa ya nufi Main parlour babu kowa sai Hajjir bai ko kalle ta ba ya nufi sashin Abba Hakimi. A zaune ya same shi saman ladduma gabansa ɗauke da kayan marmari sai ƙwaryar zuba da kuma ta fura da nono. Zama ya yi yana fuskantar Abban na shi cikin mutunci bakin na motsa wa alamar gaisuwa Abba Hakimi ya yi murmushi ya ce. "Ba sai kace ba, Allhamdulillah" Sheikh Aliyu a lumshe idanunsa yana mamakin yadda Abba Hakimi ke fahimtar zuciyarshi da yawan lokuta.
"Naga baka shirin auren naka, kamar dai you're not ready if i not mistaken?" Sheikh ya buɗe idanu da kyau akan Abba Hakimi cikin mantuwa domin gaba ɗaya ya manta da batun komai cikin In-ina yana riƙe Alkyabbar dake jikinsa da kyau tare da karkatar da kansa yana rufe idanu ya ce. "A...a...au au aure kuma A a Abba?" "E, Aure mana Sheikh haka za ka yi ta zama babu aure ni ma da kaina ban goyi bayan hakan ba, kayi aure kamar yadda Engineer ya buƙata ko dan samun kusanci da shi" Sheikh zai magana Abba Hakimi ya ƙara ɗaga masa hannu ya ce.
"Kada kai musu, ka amince Allah ya sanya albarka, Engineer ya buƙata ka tura kuɗin lefin ita yarinyar tun da ba auren kake so ba, yi maka za ayi na fanshe ka na bada kuɗin lefen kamar yadda suka ce 2.5m zai isa komai na lefen" Sheikh ya ware idanu jin wai 2.5m kuɗin lefen yarinyar da ko sanin kamarta bai ba,baya buƙatar kuma ya sani ɗin.
Cikin kyakkyawan lafazi Sheikh ya sake furta "2.. 2.. 2.5m A aaaa Abba yai yai yawa fa?" Abba Hakimi ya girgiza kansa yana mmkin yadda Sheikh babu abin da ya sani dan gane da rayuwar mace.
YOU ARE READING
IDAN BA KE
Kurgu OlmayanTrue life story. labarin zanan ƙaddara wanda babu wanda ya isa ya hana shi faruwa sai Ubangiji al'arshi. soyayya mai cike da tausayawa wacce ƙaddara ta haɗa a lokacin da ba'ai zato ba.