Page 11

569 12 2
                                    


Abba Hakima ya kalli Sheikh a nutse yana mai sakin murmushi shi ma, tare da juyawa ya kalli budurwar wacce taƙi yarda ta kalli inda Sheikh ɗin yake, tun daga sama zuwa ƙasa Abba Hakimi ya ƙare mata kallo kafin ya ce "A'uzu bi wajhillahil karim, Wabi kalimaatil lahillati la yujawizuhunna barran wala fajiran, wabi asma'illahil husna kulliha, ma alimtu minha wa malam a'alam min sharri ma yanzilu minas sama'i, wa zara'a fil'ardhi, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatillaili wan nahari, wa min ɗawariƙil laili wan nahari, illa ɗariƙan yadruƙu bikhairin ya Rahamanu. Wa min sharri kulli dàabbatin Rabbi akhizun bi nasiyatuha inna Rabbi ala siraɗin mustaƙim" jikin budurwar ne ya fara rawa sosai, tsoran Abba Hakimi da Sheikh Aliyu Haydar Aliyu suka cika mata zuciya, bata son su cutar da ita tunda ita bata zo da nufin hakan ba, kuma daman Ubangiji ya ɗora mata tsoran Sheikh ɗin tun ba yanzu ba, tana jin girma da nauyinsa tare da shakkar sa kwarjininsa yafi komai dagula mata lissafi. Idan ka ɗauke Abba Hakimi, No one understands the words of Sheikh Aliyu.

"No!!!"
Sheikh Aliyu Haydar ya furta a nutse yana riƙe hannun Abba Hakimi wanda bakinsa ya kasa yin shiru da addu'ar da yake, dalilin hakan yasa budurwar ta nemi birkicewa wanda kuma daga Abba Hakimi sai Sheikh ɗin ne kawai suke ganin hakan. Shiru ya yi da addu'ar yana kallonta kafin ya juya ya kalli Sheikh fuskarsa ɗauke da annuri irin na cikakkun dadtawan nan ya ce. "Yaushe Aliyu ya samu abokai haka bani da labari" a wannan karan Sheikh bai murmushi ba sai rirriƙe hannun Abba Hakimi da ya yi yana lumshe idanunsa tare da buɗewa alamar "Bai san yadda akai hakan ya faru ba" riƙe hannu Sheikh ɗin kai tsaye Abba Hakimi ya yi domin kai tsaye ya fahimci karatun idanun na Sheikh.
I.G dake tsaye shi da Barrister Maryam yana bata haƙuri ya ce.
"I'm sorry, action was taken without investigation, we were wrong" kasa riƙe kanta mother ta yi cikin losing control ta ce. "You have defamed Sheikh's name, all those who respect him have now stopped, Sbd Kuskuren ku my son is innocent na riga dana faɗa muku, but you refused to understand me" Bar Zainab ta numfasa cikin rashin jin daɗi ta ce "Everything that has happened has already happened, kawai a kira ƴan Jaridu a shaida masa Sheikh bashi da laifi, sharri ake masa bai san komai ba a  wanke sunan shi daga ɓacin da ya yi" cikin martabawa da nuna rashin daɗin abin da duk ya faru I.G ya ce.
"Aikinmu ne hakan, za muyi abin da ya dace muma ba zamu so sunan Sheikh ya lalace ba yana da girma da daraja a idanun ba" Mother gaba ɗaya haushin duk wasu jami'an tsaron take ji hakan yasa cikin sauri ta juya zuwa inda Abba Hakimi da Sheikh suke tsaye, idan ka gansu zaka ɗauka da gaske Hakimi shi ne ya haifi Sheikh sbd tsananin haibar dake maƙale a jikin ko wanne kusan duk halin Hakimi Sheikh ya kwashe shi tas.
Kallonsu ta yi cike da son ko wanne wanda ke rinjayar zuciyarta ta ce "Thank you Abba Hakimi" murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba, tana ƙoƙarin sake magana ya yi saurin barin wajan zuwa cikin motar da Umar-khan ya buɗe masa baya.
Tsaye Sheikh yana bin mahaifiyar tasa da kallo ganin tai shiru ya waro mata manyan Idanun shi yana son cewa wani abu amma ya ja bakinsa ya yi shiru a hankali ta ce "zaka bini ko Abban naka za kabi?" Bakinsa ya motsa yana rufe idanu tare da fara buga ƙafa yana riƙe jikinsa da kyau cikin In-ina ya ce "Zazzzza... zan zan zanje gida wajan fa... fa.. father ina soooo son ganinsa"
haushi ne ya kama Mother ganin duk abin da ake Sheikh yana maƙale da son mahaifinsa. "Father baya gari, kaje wajan Hakimi ka huta da kyau gobe sai kazo mu tattauna, ina tunanin za a haƙura da zuwa Madina haka" girgiza mata kai ya yi bai ce komai ba ya juya ganin har lokacin Abba Hakimi na zaune bayan motar, yanzu zuwa shima ya shiga baya Ishaq-hakim ya jasu. daga nan Bar Zainab gidanta ta shige hakan yasa Umar-khan ɗaukan Mother a ɗaya daga cikin motocin Sheikh suka nufi gida, Saif-Wazir kuma ya tsaya domin magana da ƴan jarida.

Suna tafe a hanya Sheikh na yiwa Abba Hakimi hira cikin nutsuwa duk da In-ina yake amma Hakimi na fahimtar komai da Sheikh ke faɗa, a duk maganganun Sheikh ba za kaji kalmar MACE ta fito daga bakinsa ba, balle har ya ware wata musamman yana magana a ganta, Murmushi kawai Hakimi yake Ubangiji ne shaidar son da ya kewa Sheikh a jinin jikinsa yake.
A haka suka ƙarasa haɗaɗɗan gidan Abba Hakimi dake Dawaki roud, gida ne irin na sarauta mai kyan tsari da fasali ko'ina ma'aikata ne , motar na tsayawa Sheikh ya fito ƙwayar idanunsa na nuna gajiyar da yake ciki.
Bai tsaya jiran Abba ba, kai tsaye ya nufi part ɗinsa wanda yake cikin gidan Abba Hakimin wanka ya yi da ruwa mai zafi yana gamawa ya fito ɗaure da babban towel idanunshi na janye wa barci na cin ƙarfinsa ya ɗauki wani tsadaddan lotion, Shea body butter ya shiga shafawa saman fatarsa a kasalance, Engage Cologne Spray ya fesa a fatarsa sbd ɗauke zafin da ya keji yana gamawa ya miƙe zuwa clothes ɗinsa ya ɗauki wani trousers mara nauyi ya saka ko riga bai saka ba, ya cilla mint bakinsa ya kwanta saman bed yana lulluɓe jikinsa da bargo, ganin rana ce ya sa ya kunna A.c tare da rufe idanunshi cike da fatan barci ya ɗauke shi.

IDAN BA KEWhere stories live. Discover now