Page 2

965 21 0
                                    

Ihu Danejo ta fasa lokacin da taji an saka hannu tare da yin sama da ita cikin muryarta ta Fulani ta ce "Mi boni Dada'am mi nasti tati hande mi mayi" gaba ɗaya ta tsorata ta ɗauka motar za tabi ta kanta. Jin an direta gefe guda ya sanya ta buɗe idanunta a hankali a tsaye ta gansa nesa da ita kaɗan hannunsa harɗe a ƙirji yana ƙare mata kallo tare da nazartar yanayinta. Kasa daina kallonsa Danejo tai sbd yanayin shigar jikinsa wani farin yadi ne a jikin nasa amma yai baƙiƙƙirin sbd dauɗar daya haɗa gaba ɗaya yadin ya yayyage har ana iya ganin farar fatar jikinsa, sumar kansa rabi furfura rabi baƙa. Ajjiyar zuciya ta sauke da sauri kuma ta juya sbd ƙarar motar da taji sai a lokacin lura da shegewar motar cikin Abti America.
Ƙugu ta riƙe tana fari da manyan idanunta cike da tsiwa ta ce "Shai mutum ya tsaya yaga yadda ake tijara aradu ina iya fasa gilahin moto ɗin" daga bayanta taji murya mai sanyi ta daki kunnenta ance "Zaki biya?" Juyawa tai ta kallesa mutumin ɗazo ne dai wanda ya taimaketa kafin motar ta bigeta, harara ta banka masa ta ce "Kai Almajiri Sukajo meye ruwanka dani? Ina ruwanka idan moto ya takani, da kayanka duk a yage" ta faɗa tana murguɗa masa baki. A hankali ya nanata kalmar “Sukajo” a ransa idan ya fahimta Sukajo na nufin “Saurayi”  Girgiza kai kawai yai ba tare da yace mata komai ba ya juya zai bar wajan. Da sauri ta sha gabansa tana faɗin "hani inbano ina ka kai mini kindirmon shaniyata? Waye ya tittila a tumbinsa?" Juyawa yai tare da kallon ƙwayar nonon babu komai a ciki sbd tuni ta zubar da nonon dalilin tsoran da taji, amma ta kasa fahimtar ita ta zubar ɗin. Yana dai tsaye bai ce komai ba can kuma ya kalli cikin idanunta da sauri ta ɗauke nata idanun tana murguɗa masa baki cikin ƙasa da murya ya ce "Siya akai ai" baki ta buɗe ita ai ba taga wanda yazo ya siya ɗin ba kuma gaba ɗaya nonon aka siya kenan? "Ina kuɗin to ɗan Almajiri mai yagaggun kaya?" Da hannu ya nuna mata ƙasan ƙwayar yana rufe idanu da buɗewa ya ce "Gasu can" ta durƙusa ta ɗaga ƙwayar sai ga kuɗi da gudar dubu ɗaya da ɗari biyar guda biyu sai ƴan ɗari guda goma. Zaro idanu tai waje jikinta na rawa ta ce "Kai ɗan Almajiri mai ƙarya wannan kuɗin duk na kindirmona ne? Ai aradu kuɗin yai yawa" hannunsa dake harɗe a ƙirji ya wara tare da ɗaga kafaɗa ya ce "haka suka bayar ai" "su waye?" Shiru yai mata yana ƙoƙarin juyawa ta ce "Mene wannan a ƙafarka?" Zaro idanu waje yai tare da yin baya ganin tana ƙoƙarin zuwa inda yake yasa yai saurin faɗin "ke fillo bayanki" juyawa tai da sauri amma babu kowa a wajan tsaki taja tana kakkaɓe zanin jikinta ta ce "Mai ƙarya dai ɗan wuta" ta ƙare zancan tana ɗago kanta babu Almajirin kamar yadda ta raɗa masa suna babu ko inuwarsa sai wani farin Zomo data gani kyakkyawa dashi ya ƙura mata idanu, itama kafesa tai da idanu kamar zata kamasa sai kuma ta ɗauki ƙwayarta ta nufi  bakin hanya inda zata samu motar da zata kaita Njoɓoli. Da idanu Zomon ya bita har tayi nisa sosai yana kallon sanda ta samu abin hawa, girgiza yai yana kaɗa kunnuwansa sai gashi ya koma mutumin ɗazo wanda take ce masa Almajiri mai yagaggun kaya. Murmushi yai mai kyau a kuma fili ya furta "Danejona"

Da gudu motar mai ƙirar  Toyota Rav 4 ta Ƙarasa shiga cikin compound na Abti American University Yola (AUN). A hankali akai parking motar a tsakanin jerin motocin da suke cikin harabar. Buɗe murfin motar tai cikin faɗa faɗa ta ce "No! I mean I lost my eye sight for a while, my Mom slapped me and i was very shouked da marin, Sbd kawai wancan banzan ya kai ƙarata gida i hate him wallah ai babu dole cikin aure ko? I'm 29 years mene ya sa za ana damuna akan wani aure?" Yanayin yadda take maganar kaɗai zai sanya kasan ranta ya ɓaci har buga kan motar take sbd zafin zuciya tsaki tai ta ce "No am okay nazo ganin Zahrah ne, i will catch you later" kashe wayar tai baki ɗaya tana fitowa daga cikin motar tunawa da yadda Yarinyar ɗazo da yadda ta  firgita ya sanya tai Murmushi tana nufar hanyar wani office. Office ɗin ba kowa sai some of things da suke saman table zama tai tana danna number Zahrah.

Zahrah na tsaye cikin hall ɗin da take lecturing wayarta tai ringing ta san babu wanda zai kirata at this time sai Surayyerh da sauri ta kalli students ɗin dake hall tana faɗin "Ok guys Conservation biology has two central goals 1. to evaluate human impacts on biological diversity and 2. to develop practical approaches to prevent the extinction of species (Soulé 1986, Wilson 1992)" tana faɗin hakan tace "You get it?" Gaba ɗaya suka ce "Yes Maaa"  jinjina kai tai tana taɓe baki idanunta akan wani matashi da sauri kuma ta juya hannunta riƙe da Ink pen ta nufi wajan bord da sauri ta shiga rubuta.

IDAN BA KEWhere stories live. Discover now