SAI NAGA BAYAN KI

407 32 4
                                    

*SAI NAGA BAYANKI*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

*PAGE 1*

Rasheeqa

Kallon tv nake ba wai dan Ina fahimtar ma Mai nake Kallo ba dan hankalina ba a wajen yake ba, Kara daga kaina nayi na kalli agogon dake jikin bango zuwa lokacin raina ya Kai karshe wajen b'aci,wayata da na jefar a gefena na Kara daukowa na Kara Kiran lambarta Wanda Ina ga nafi awa daya Ina kiran ta bata d'auka ba miss call da na mata yafi ashirin,kamar yadda nayi zato har ya karaci ringing bata d'auka ba,girgiza kaina nayi na mik'e ganin goma da rabi tayi yasa na karasa wajen tv na kashe na dauki Yara na biyu Abul da Abla da tun wajen Tara bacci ya d'auke su na dauki Abul na dan bugi kafar yayansu Imrana da shi ma baccin ya Dade da kwashe shi Ina "tashi ka tafi daki ka kwanta"

Mikewa yayi Yana mitsitsika ido ya hau sama ni kuma na shiga dakina na Kai Abul na kwantar na dawo na dauki Abla itama na kai ta dakin.

Na koma Palo na kulle kofar palon,na koma cikin dakina sai da na watsa ruwa na kwanta duk raina a b'ace har ga Allah kishatu ta fara Kai ni bango bazan zauna na zuba mata ido tana abinda ranta ke so ba,kiran mijina daya shigo wayata ya katse min tunanin da nake kamar bazan dauka ba dan duk ranar da ba nice da girki ba da haushinsa nake kwana dan gani nake yadda yake rawar kafa a kaina haka yake yi akan bakar matarsa,ban kuwa daga ba sai da ya sake kirana,na d'auka nayi shiru ya fara magana yana "Gimbiya ko har kin fara bacci ne"?

Kamar Yana gabana sai da na gama hararar wayar nace "Ban yi ba sai yanzu kaga damar kirana sai yanzu aka bar ka ka kirani kenan"?

"Gimbiyata kenan kema Kinsan duk abinda nake wallahi kina raina yau lissafi muka tayi sai yanzu na baro shago ko gidan ma ban kai ga karasa wa ba"

"Hmm na d'auka ai hana ka tayi ka kirani"

"Wane mutum yanzu ma idan kikace ba acan zan kwana ba kinsan tahowa ta zanyi nan dan ni akan dole nake nisa dake"

Sai a lokacin na dan ji sanyi a zuciyata bacin ran kishatu ya dan sakeni

Na saki murmurshi Ina "ai shikenan yanzu dai ka karasa gida sai da safe"

"Ina Su Abul ne banji motsinsu ba ko su ma sunyi bacci "?

"Sun Dade da bacci ni kadai ce banyi bacci ba"

"Kishatu ma tayi bacci kenan"?

Shiru nayi Ina Jin bacin rai na taso min da na daga kaina na ga Sha daya ta wuce har da minti goma

Sai na daure Ina "Tayi bacci itama tundazu"

"Allah sarki gimbiyata na d'auka fa zata na debe Miki kewa idan bana nan akan me za tayi bacci da wuri ko dai nazo na tayaki kwana"?

Har ga Allah da zai zo din Dadi zanji kuma Ina ce yazo din zuwa zai yi amma bana so ya gano kishatu bata gida hakane yasa nace "Aaa ba sai kazo ba ka wuce gida kawai nima na fara jin baccin kwanciya zanyi"

"Ba wani matsala dai ko ba wani Abun da kuke bukata"

"Babu komai Alhaji"

"Tom shikenan bari na karasa idan na isa zan kiraki idan kuma baki dauka ba nasan kinyi bacci gobe da asuba zan zo"

"Tom shikenan Ina Jira sai da safe"

Daga haka na katse wayar dan Allah Allah nake na kashe wayar na Kara Kiran kishatu a waya.

Sai dai Koda na sake kiranta haka yayi ta ringing bata d'auka ba.

Jefar da wayar nayi na kwanta zuciyata fal bacin rai har ga Allah bazan tab'a daukar wanan iskancin ba ya zama dole nayi kararta,toh wajen wa zan Kai kararta ma,Aunty Ama ce zata iya daukar mataki ita kuma munyi fada da ita,naja dogon tsaki da na tuna abinda ya hadani da ita nayi na Allah nayi na Annabi idan har Kishatu bazata shiga hankalin ta ba wallahi korarta zanyi bazan iya da wanan iskancin ba.

SAI NAGA BAYAN KIWhere stories live. Discover now