BARAGURBIN KYAU 6

4 0 0
                                    


*BARAGURBIN KYAU*

*_Aysha D Fulani_*

*SHAFI NA SHIDA*

*Page 6*

*_Afuwan don Allah rashin wuta ke hanani typing kulum_*


                    بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

________Hmmmm. Dan da shi zan fara kin san wasa farin girki? To shine wannan farkon labarinmu ne daga makaranta na dauko miki domin ki fahimci abun, a lokacin da Hamdan yafara zuwa gidanmu ashe tun a wannan lokaci Zainab ta fara son shi.

Hamdan idan muna tare da shi ji take kamar zuciyarta zata fashe idan muna tare da shi daurewa kawai take, idan abun ya ciyota sai ta shiga bayi tai kuka ta yarda babu mai ganewa.

Shekaramu uku ana wannan halin ni ban sani ba ƙwasam muna gama secondary sai Hamdan ya sake turo iyaye shi da kudin aurena, cike da murna Abba ya kira ɗan uwanshi dake nan wato wanda ki ka ga yanzu ina zaune a gidansa. Ashe shikuma baya kasar a lokacin, ai ko take mahaifina ya wakilta mahaifin Zainab suka kawo kudin gaisuwa da sadakin wato kudin aure.

Koda aka mana baiko mahaifin Zainab ya amshi kudin ya kawo ma mahaifina bayan tafiyar masu kawo kudi, sai mahaifina ya ce ya rike kudin a wurin shi zuwa lokacin da ɗan uwasa zai dawo.

Ni ban sani ba ashe kawo kudin aurena da Hamdan ba karamin daga hankalin Zainab ya yi ba a lokacin ta fara wata irin cuta, yau lafiya gobe babu lafiya haka a ka dinga tirzawa har ta samu lafiyaa, Ni kaina na samu wani  irin chaji daga gareta sai dai abun bai dameni ba duba da yarda na gani  ko ciwon da taine ya sa hakan ta kasance.

A lokacin ta rage zuwa gidanmu sosai kuma idan Hamdan yazo bata cika fitowa wurin shi suka gaisa, abun ya fara bani haushi na tirketa ina tambayarta sai cemun tai ai yanzu mun girma ya kamata ace ta ringa barin mu mubiyu muna zantawa saboda ko munyi aure ba da'ita zamuyi zaman auren ba.

Wannan dalilin tai anfani da shi tasa na kyaleta, shi kuma Hamdan da haka yai anfani a farko idan yazo yakan rike mun hannu, sai na fara nuna banso shi kuma ya nuna mun ya ke ai bakomai ba ne da na takura banso, sai yake cemun idan har cutar da Ni zai yi da bamu kawo yanzu ba, kadda na manta cewa shekarar mu uku yanzu idan wani abu yake nema zai nema tun kafin kawo yanzu.

Nazari mai akan kalamansa tabbas hakane zuciyata ta ban amsa da zai cutar ni da fah tuni an dade da wuce wurin, kawai ni kuma sai na kyaleshi abu kamar wasa yafara sai da muka kai gabar da babu inda Hamdan bai kai hannun shi jikina.

Zainab daukewar da Zainab take mun ta bamu dama sosai wurin dilmiya wa komar shaidan, dan duk sanda Hamdan zai zo sai ya lalubeni yake jin dadi ko ince muke jin dadin jikinmu.

Shigata gidansu Zainab na isketa a dakinsu tai rufda ciki, kallanta nai ina tambayata lafiya sai take shaida mun cewa babu komai nace don Allah ta gayamun gaskiya ta tabbatar mu da babu komai, waya na ciro masu kyau sabbi kal a kwalin su na mika mata nace ta zabi ɗaya a ciki Hamdan ne ya ba mu.

Murna sosai ta nuna ta dauki ɗaya tunda kalarsu ɗaya, layin na miƙa mata ta bude, wurin Ummata muka zo muka nuna mata ta sanya albarka, shima Baba da yadawo har gida yazo yai mahaifina godiya.

Tofah ki saurara daganan wasan yafara, ya bamu waya ashe makamin rabuwar muce ya bani, dan a lokacin ne muka samu admission muka koma makaranta.

Hamdan shi yake zuwa ya ke dauko mu daga makaranta, farkon zuwan mu makaranta samari sukai mana cha akai, akwai wani Abakar shine ya nace mun yin duniya na fahimtar dashi ya kasa ganewa.
Abin da ban sani ba ashe ta bayan fage Zainab ke zuga shi, tana bashi duk wasu bayanai nawa ita kuma ta sauya layin wayarta tana yawan tura wa Hamdan sakon soyayya, yau da gobe mai abin ban mamaki tun baya bi takai har ya soma kiran layin yaji ko wacece, duk yadda yaso da'ita taki bayyana mai kanta kulum gaya mai take ya jira lokaci zata bayyana mai ko wacece ita.

Abakar ya yi juyin duniya ya samu kaina ni kuma na ki amcewa, hakan yasa yaje gurin mahaifina anan ne yasamu tabbacin baikona da Hamdan, haka ya hakura ba dan yaso ba.

Soyayya kamar wasa ta fara zama gaske kinsan abun da baka taba gani ba jin kan ka kake kamar kai tsuntuwa ka nemo shi, na shigo dakin baki na iske Hamdan zaune yana kallan vedio, sai dai ban ji mai ake cewa a vedio ba dan  kunne sa da Bluetooth, matsawa nai na leka wayar aiko nai arba da vedio mata da miji tsirara suna jima'i kauda kaina nai gafe Hamdan ya jawoni jikinshi yafara wasa dani yau salon ya bambanta da na kulum, domin a zafafe yake aikamun da sakonninsa.

Kin san jiki da jini haka na kasa jurewa na biye mai a inada aka tirje shine ala dole sai ya kusance ni, anan na tada hankalina da lalami ya nuna mun cewa ai bazan ji zafin ba saboda ai na riga da nasaba da wasan da yake mun da hannunsa. Da haka ya ribace ni ya kwanta dani a cikin gidanmu, ina jin ciwo mai zafi idan na tuna wannan abu.

"Ramatu mu bari sai gobe kinga yamma tayi yanzu kuma na gaji ga gajiyar hanya kaina yafara ciwo, wallahi idan mun cigaba yau zan iya kwana da ciwon kai".

A jiyar zuciya Ramatu ta sauke "Lallai ko iyanan ki ka tsaya nasan akwia tarin labari a baya, amma kiyi hakuri ki dauka hakan ƙaddarar ki ce domin shi bawa baya tsallake abin da Ubangiji ya ajiye mai. Na sani da ciwo matuƙa amma sai an daure Allah ya yafe mana baki ɗaya Ni ma bari inje gida sai zuwa gobe idan Allah ya kaimu".

Miƙewa Ramatu tai wa Umma sallama ta nufi gidansu, itama mardiay miƙewa tai ta kwashe kayan wurin ta gayara falon, ta wuce daki ta sillo wanka a bayanin da ke manne da dakin.

Wayarta ta ciro wacce ta iske miscll wurin goma, kuma dukka kusan lambobine daya ce kawai a jiki ba bakuwar number ba, Kuma itace kiran da ya sake shigowa.

Da sallama ta daga tana fadin " Alhamdullilahi Adda mun sauka lafiya wallahi, eh na gaya mai dukka yarda akai halan ya kira ne?".

"Ya kirani amma nima bayani nai mai sosia kuma ya ce duk sanda Hamdan ya sake takowa cikin gidan in sanar mai".

"Okay Adda sai kiyi yarda yace don naga ya fusata sosai a kufule yake da lamarin, Allah dai ya kyauta".

Haka muka cigaba da tattuawa har na gama shirina, washegari na shirya zuwa school duba da bawani hutu garemu ba kwai dama na shirya zuwa gida ne, don tunanin jikin mahaifiyata da bata cika lafiya ba.

A motar gida nafita Ni da Ramatu ni ke tuka motar har muka isa cikin makaranta, daidai inda ake ajiye motoci, na ajiye tawa motar hanyar aji muka nufah, na hango wani malamin mu wanda yai matukar takura rayuwata, akan lallai sai na amince yazo gida ai babu shiri na antaya aji da sauri don banso ya karaso ya ganni.

Ina shiga Ramatu ta shigo tana dariya duba da tasan takun sakar da mukeyi da shi,dariya ta dinga mun har muka fara karatu.

Munfito misalin karfe ɗaya  ban karya ba dama nafito, hakan yasa muna fitowa na kama hanyar kafe, muna shiga wurin nai tozali da tashin hankali.

Hamdan na hango zaune ya kuramun ido yana aiko mun da wani irin shu'umin kallo, ban kula shi ba duk da gabanan sai dukan tara-tara yakeyi ganin inda na kallah da alamun firgicin a tare dani yasa Ramatu bin wurin da kallo itama a dan rikice ta jiyo tana dubana. Tambayar data wurgo mun ne yasani kallon ta dakyau.
    Ya dai Sis Hamdan ko?".Gyada mata kai nai alamar "Eh".
"Tashi mutafi gida". Ramatu ta furta miƙewa nai muka fara tafiya don bamu so ya cimmana.
Cikin motata na shiga naji an riko mun hannu, ihu na kwara wanda yai sanadiyar janyo hankalin  mutanen wurin, sake sakin wani ihun ganin Hamdan yana rike da hannuna.

A kideme nafara fadin "Wayyo Allah a taimakeni zai sace ni, wayyo Allah na jama'a a taimake ni wallahi ban san shi ba".

A hanzarce Rahma tayo kaina tana ihu itama a taimake mu zaratan samarin makarantar mune sukayo kanshi, suna fadin saketa banza yai musu ya cigaba da rukona. Basu tsaya bibiyar meyafaru ba suka rufe shi da duka, nikuma nai gefe ina murmushi a zuciyata. Dakyar da sidin goshi wasu daga cikin mutanen suka kwace shi  Ni kuma akan dinga ban hakuri, haka ina kallo a gabamu akai gidan ƴan sanda da Hamdan

✍️Aysha D fulani.
Facebook Aisha D Fulani.
What's app 09064234445.
Wattapd Fualni010.
Tiktok Fulani010.
Arewa book Aysha d fulani.


BARAGURBIN KYAUWhere stories live. Discover now